Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 32 of 49
Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set É—in kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set É—in hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
HaÉ—ine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.
Idan kin sayi kaya in dai set É—in kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuÉ—in Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.
0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
By
*GARKUWAR MARUBUUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 72
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Kan cikinta, murya a sanyaye yace.
“Farriyyha kina jin nakejiâ€. Ƙarfin Alluran da akayi mata da gajir da ya tara mata ga kukan da ya galabaitar ne suka haÉ—e suka diro mata mutuwar jiki da kasala haka nan taji idonta na lumshewa.
“Farriyyha Mamy da Malam suna fushi da ni ko?â€. Ya faÉ—a yana É“alle marfin goron Admiral É—in ya kai matashi bakinta.
Kai ta jujjuya mishi ido na zubda wahaye sake kai matashi bakinta yayi haÉ—i da cewa.
"Please dan Allah kiyi haÆ™uri kisha kar yunwa ta cutar min dakeâ€.
Ture hannunsa tayi tana yunƙurin tashi haɗe da mishi kallon dake nuna tsanar zama kusa dashi.
Ajiye goran yayi haÉ—i da jawota ya manna bayanta da Æ™irjinsa ya riÆ™eta gam a sanyaye yace. "Mamy na fushi da nikoâ€. Tana janye hannunsa ta gyaÉ—a masa kai alamun eh. Cikin yace
“Dan Allah in kin je ki basu haÆ™uri kice su yafe min kada suyi fushi daniâ€. Ya Æ™are maganar yana manna lips É—insa kan wuyanta
Ummi tacewa Amina.
“Me ya tsaidaku ne haka bayan naga tunda Dr Fadil É—in sun tafi, kuma tun safe su Hafiz sun gama sauÆ™ar da kayanta har Hafiz ya kaisu ya dawo,Ina Fariyda Abbanku na jiranta fito da nace masa sunyi baÆ™ine yace to a barsu gashi yanzu kuma har azabar tayiâ€. Cikin rashin sanin abin faÉ—i tunda Mahmoud É—in ya gargaÉ—eta karta faÉ—a musu komai yasa a hankali tace.
“Tana zuwaâ€. Goggo Dada tace.
“Ko karyawa batayi bafaâ€. Kije kice mata tayi sauri ta fitoâ€. Tana jawo jakarta jin wayarta na ringing tace. "Tohâ€.
Tattaro dukkan ragowar Æ™arfinta tayi ta fizge jikinka daga gareshi, jiki na rawa ta sauÆ™a daga kan gadon fuska a tsuke har lau ido na zubda Æ™wallan murya a dishe tace. “Ka bani wayata ni zan tafi gidanmuâ€. Shi kuwa Mahmoud wayar da kiran Muhajid ya shigo yake yiwa wani irin kallon zuciya a tafashe ya cilla mata wayar yana miÆ™ewa tsaye yace. "Kifi ruwa tafiya duk dai inda zakije da igiyar aurena a kanki, in kinje gidan nakuma kada Allah yasa ki tsaya ki wuce gidansu jakin da yake kiran naki nan zan san baki da hankali shi kuma duk abinda nayi masa shi ya jawa kansa wlh duk motsinki idona na kanki in ya kuskura ya zo inda kike sai na hanashi ganin hasken rana ma bare ya Æ™ara kallon matar wani ma bare tawaâ€. Ya Æ™are maganar yana nuna mata hanyar fita, tsaki taja tare da murguÉ—a baki ta juya ta fita tana taune lips É—inta, idonta na kan wayar kallon text É—in da yayi mata ta wayar Yah Amin bata buÉ—e ba taci gaba da tafiyar tana jin sukan zazzaÉ“i na É—an sauÆ™a dan allurar da akayi mata dana kashe zogin sun taimaka mata sosai.
Tare da Amina suka shiga parlour Abba bayan Ummi tasa sun ci abinci gaidashi sukayi kana suka bi bayansa.
Ganin ya miƙe ya fita, rungumeta Ummi tayi ido cike da ƙwalla tace.
“ina sonki Fariyda bakuma zan daina sonki ba har gaban abadan, amman Æ™addara ta rabamuâ€. Itama hawayen na zuba ta rungume Ummi haka dai suka rabu kamar yadda suka rabu lokacin rasuwar Aminullah.
A gidan Baba Malam Mamy da Aunty Amarya da Abba da Uncle Sani bappansu Fariyda ne zaune a parlour Malam É—in Abba yana tausarsu da shaida musu Babu laifin Fariyda a mutuwar aurenta.
A can cikin gida kuwa.
Fariyda ne dasu Zainab Raihana da Humaira sai matar Yah Nasir duk jugun sukayi ba wata wal-walar tare dasu tun da Hafiz ya dawo da kayanta, tana zama ta zame ta kwanta tayi pillow da sawun Aunty Saddiqa sai kuma ta kamo hannun Aunty Saddiqa tace.
“Ya jikin Yah Mujahid yana asbiti ko? Muje mu dubashi da jiki Aunty Saddiqaâ€. Mamy dake shigowa ne ta danna mata harara cikin takaicin mutuwar auren da har ranta take son Mahmoud É—in a matsayin surkinta rai a É“ace tace.
“Ki nitsu ki gama iddar kafin ki fara batun yawon dubiya ki sani yanzu ba inda zakije har sai kin sami sahalewa da yardar Mahmoudâ€. Kai ta longwaÉ“ar cikin sanyi murya a dishe tace. "Mamy ya sakeni ma sai na nemi izininsaâ€. Kwaffa Mamy tayi tace.
"Tabbas kuwa dole har sai kin gama iddarsaâ€. Ta Æ™are maganar tana shigewa bedroom É—inta rungume dasu Zaid da Abba ya batasu da kanshi.
Ita kuwa Fariyda da sauri ta kalli Saddiqa dake cewa.
"Mu fa yau gidan nan ba wani farin ciki tare damu Fariyda mutuwar aurefa ba wasa bane, naga kamar farin ciki kikeyi har kina mgnar zuwa duba wanda yayi miki sanadin mutuwar aurenkiâ€. Fuska ta kwaÉ“e cikin son fahimtar dasu tace.
"Aunty Saddiqa nifa ba wani bani da sauran matsala tunda ya sakeni ai shike nan ya kema kina mgna kamar baki san komai ba, Yah Mujahid kuwa wlh ba shi yayi sanadin mutuwar aurena ba, dama can yana da niyar saki nima kuma ba son zama dashi nakeyi baâ€.
Shiru tayi jin Mamy na cewa.
“Ci gaba da rashin kunyar ai dama ni na sani ruwa baya tsami banzaâ€. Shiru tayi tana yin Æ™asa da kanta saboda ganin kallon da Mamy keyi mata, Aunty Sadiya matar Dr Nasir ta É—an numfasa tace.
"Wallahi ni duk jikina yayi la'asar nama rasa abin faÉ—iâ€. Humaira na kallon Fariyda tace. “Ni wlh su Zaid ne suke bani tausayi a rabuwar auren nanâ€. Raihana da tuni ido ta ya tara ruwa tace. "Wallahi nima abinda nake tunawa kenan, nasan tabbas watan wata rana Yah Mahmoud zaisa a karÉ“esu.†tana yin Æ™asa da murya yadda Mamy bazata jitaba tace.
“Ai kuwa dole ya bar min su tunda bashi ya haifa min suba, kuma su Abba da Ummi ma sun yarda a barmin su ni dashi kuma haihata-haihataâ€. Kwaffa Saddiqa tayi ta miÆ™e ta shiga bathroom É—in su Raihana inda suka jera kayan Fariyda da yaranta.
Washe gari da yamma Dr Nasir ne zaune bakin gadon Mamy gefen Mamy Fariyda na zaune a Æ™asa. “Mamy muyita addu'a kawai Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, Amman batun daÉ—i kam ai abin bai mana daÉ—i ba, ni nasan waye Mahmoud wlh yana da nagartar da ita kanta Fariyda bata saniba sai yanzu da suka rabu zata gane, shine Garkuwarsu ita da yaranta, a cikin Æ´an uwa dubu kaÉ—an ake samu irin Mahmoud masu nagartar kula da tarbiya da rayuwar Æ´aÆ´an yan uwansu bayan ransuâ€. Cikin É“acin ran da har yanzu bai bar zuciyar Mamy ba tace.
"Ai ita da yake bata san abinda ake duba mata ba, har farin ciki takeyi da sakin mutumin da yake son Æ´aÆ´anta fiye da kowa a duniya, tana farin cikin zata auri Muhajid, hmmmm ba komai Allah ya tabbatar da alkhairiâ€. Amin yace yana kallon Fariyda a tausashe yace.
"Wai Sadiya tace min baki da idarsa?". Da sauri ta gyaÉ—a kanta tace.
“Eh kuma su Abba ma sun sani Malam yasaniâ€. Cikin sanyin jiki yace.
"Shike nan ai, Allah ya bawa Mujahid É—in lfy, in hannun ya Æ™ara sauÆ™i sosai dai sai a É—aura muku auren tunda dama shi yana sonki kema kuma yanzu kin amince dashi nima kuma na gamsu zai riÆ™e miki yaranki bisa amana dan nasan son gsky Mujahid keyi miki, yanzu ma muka gama magnar da Malam yace ba don karayar da Mujahid É—in ya samu da jinyar haÆ™ora biyu da Mahmoud ya zubar masa ba, da rana É—aya za'a É—aura aurenku da na Raihanaâ€. Numfashi mai nauyi Mamy ta sauÆ™e tana kallon Fariyda da tayi Æ™asa da kanta cikin yanayi farin ciki a can Æ™asan zuciyarta kuwa abinda ya faru ke mata yawo a zuciya tsoron duba text É—in da ya mata takeji ta kuma kasa tuna menene abinyi akan abinda yayi mata bata jin kuma zata iya gayawa kowa wannan abun lallai wannan shine SAƘAR MAKAFI yees SAƘAR MAKAFI mana to ita kanta bata san menene mafitaba a kanta dan ya rigada ya gama mata dabaibayi abu É—aya dai da tasani duk rintsi bazata koma gareshiba dole sai ya tabbatar da sakin nan a karan kanshi.
Salim ya zubawa Salma ido ban ya faÉ—a mata abinda ya faru na mutuwar auren Fariyda sai kuma ya gyara zamansa jin tana cewa.
"Innalillahi ta ya su Abba zasuyi haka yah Salim meyasa baku hanasu raba auren nan ba ko dan su Zaitoonâ€. Kiran Sulaiman da ya shigo wayarsa ne yasa bai amsa mataba.
“Ato Alhamdulillah Barka da isa lfy, ya Gombe da mutanen Gombe duk ka samesu lfy koâ€. Salim É—in ya faÉ—a bayan ya amsa kiran Sulaiman da ya koma Gombe yau.
Jim kaÉ—an yayi kana yace. “To a huta gajiyaâ€.
Yayi magnar yana kallon Salma data kira Fariyda suna magna daga bisani tace in sha Allah gobe zanzo in yah Salim ya barni.
Bayan kwana uku tun ranar da abun nan ya faru bai sake shigowa parlour Ummi ba, iya karsa parlour Abba in sun dawo sallan asuba anan yake gaida Ummi da Goggo Dada.
“Har yau fa baya cin abinci, yadda Hafiz ke kai masa haka ya É—aukowa da alamun ko taÉ“awa bayayiâ€. Goggo Dada ta faÉ—a tana amsar Tray da Hafiz É—in ke miÆ™a mata. Ummi tace.
"Ni ai cewa nayi ki fita harkarsa, ki daina mishi girki ba dai yayi yadda yake soba ya samu nasarar sawa a bashi izinin sakin Fariyda, ni bazan Æ™ara shiga kitchen dan yi masa girki ba, in ya damu ya nemi mata yayi aure ta rinÆ™a mishi girkiâ€. Hafiz ya É—an juya ya kalli bayansa a hankali yace. "Ai Mom na turo masa abinci, kullum in Huzy zai zo yana zuwa masa da abinciâ€. Kwaffa tayi tace. "Ai wato Amina ko ya zanyi sai ta nuna min sunfi kusa, na lura ita tausayinsa takeji bayan koma menene shi haka yakeso kuma tsarinsa neâ€. Goggo Dada tace. “Naji ai Abba na cewa zasu tada mgnar aurensa da Jiddaâ€.
Rufe ƙofar bedroom ɗin tayi tana jujju kanta dan ta tabbatar ba kowa a ɗakin.
Kiran da a ƙalla shine na 23 da yayi mata tunda jiya zuwa yau amsa kiran tayi tana faɗin.
"Nifa ka daina kirana bana so, ka rubuta min shaidar sakin da kayi min ka bawa Hafiz ya kawo min shine yasa na amsa kirankaâ€. ÆŠan guntun Murmurshi gefen baki yayi haÉ—i da cewa.
“Hafiz zaizo ya É—aukeki kizo mu haÉ—u a Office na zan baki shaidar a rubuceâ€. Da sauri tace.
"Allah ya kiyaye Æ™ara zuwa inda kakeâ€. A hankali yace.
"Ni kuwa in baki zoba bazan bayarba, kuma dai kin sani in kowa ma bai san auren nan damaram ba ke kin sani ai ko, nasan kuma ke ba jahila baceâ€. Kuka ta saki haÉ—i da katse kiran, watoma dabaibayi yayi mata kenan.
Washe gari da dare Salma ne zaune a parlour Goggo Abu cikin sanyi tace.
"Ayyah Yah Mujahid ya jiki da sauÆ™i sosai koâ€. Hannunsa dake suntume tim an saÆ™ala masa igiya a wuya yana tallaÉ“e da hannun dan É—aurin gargajiyar da akayi masa cikin yaÆ™ini yace.
"Alhamdulillah ai ni tunda aka cemin ya saki Fariyda naji na warke, kuma na yafe masa tunda dai ya sakar min matata, Alhamdulillah nan da wata É—aya uku zuwa huÉ—u dai za'a É—aura mana aureâ€. Salim dake kallonsa ne yayi saurin yin Æ™asa da kansa yana danne dariyar Æ™eta dake taso masa dan ganin yadda wawulumon bakinsa keyi in yana magna dan har yau ba'a sa masa haÆ™orin robarba sai wurin ya warke tunda fitar Æ™arfin akayi musu, har lau kuma ga bakin a kumbure a rashi yace.
"Guy nan hegene har yanzu yana nan da muguntarsa ai in dai da Mahmoud kace zakayi ka shiga uku duk sai ya sauyama kamanni mutumin da duk salon mugunta da rashin mutunci ya iyataâ€. Sai kuma ya É—an danne dariyarsa yace.
"To Yah Mujahid Allah ya Æ™ara sauÆ™i mu zamu wuceâ€. Ya Æ™are maganar da ajiye masa kuÉ—i ya miÆ™e tsaye Goggo Abu da bayan sun gaisa ta tafi kitchen kawo musu dan abin taÉ“a wane tace.
"A'a Salim har kun tashi ne ko ruwa baku shabaâ€.
Cikin yin ƙasa da kai yace.
"Mungode Goggo dayake zamu isa mu duba su Zaid ne gashi dare ya farayi shiyasaâ€. Tana zama tace. "Ayyah to mun gode Allah ya kiyaye hanyaâ€. Daga nan suka fita. Dariya mai sauti yakeyi harda riÆ™e ciki sai yayi kamar ya tsagaita sai kuma ya kwashe da dariya in ya tuna yadda Mahmoud É—in ya sauyawa Mujahid kamanni. Cikin dariya itama Salma tace.
“Yah Salim kairfa ka turamu cikin kwalbati ka bar dariyar nan haka, kaga tuÆ™i kakeyiâ€. Yana karya kwana yace.
"Ai wlh gwara da muka fito da wurin dan na kusa yi masa dariya a gabansaâ€. Tana kallonsa tace. “Ya kuma naga ka sauya hanya ba gidan Malam zamuje baâ€. Cikin kwaÉ“e fuska yace.
"Kiyi haÆ™uri sai gobe yanzu so nake in ji É—umun jikinki shiyasa, mu koma gida gobe sai kije ki wuniâ€. Cikin sanyi tace.
"An gama Yah Salim yadda kakeso ai haka za'ayiâ€. Kanta ya shafa yace. “Allah yayi miki al'barka tawan! jarumar maceâ€. Washe gari da safe zaune yake gaban Abba, plate É—in abincin da Ummi tasa mishi ya miÆ™awa Mahmoud É—in da cewa.
“Matso kaci!â€. Yana gyara É—aurin net É—in wuyansa da yake cikin shirin tafiya office kai a ya É—an jujjuya a hankali yace. “Alhamdulillah Abba nayi breakfast yanzuâ€. Ido ya É—an zuba mishi sai kuma ya gyara zamansa tare da cewa.
“Mun gama magna da É—an uwana bappanku Lawan ya baka auren yarsa Jidda tare da yardarta, da kuma tawa yardar da ta mahaifiyarka in sha Allah za'a É—aura aurenku 23 January wannan hukunci ne na yanke da tattabartawa ba shawara ko neman yardarka ba, dan bazan lamunci zamanka ba aureba bayan sanin ka samu lfy, sanin halinki da gudun kar kaje kaci gaba da sheÆ™e ayarka kamar baya in kafaÉ—a tarko mata dan haka za'ayi bikin a ranar da nace makaâ€.
Tunda Abba ya fara magna kansa na sunkuye har saida yaji ya ambaci Jidda ne ya É—ago idanunsa da tuni sun sauya launi, lokaci É—aya jikinsa ya fara tsuma jin Abba na maimata fadin abinda ya aikata dasu Idaya a baya. Murya na rawa yace.
“In sha Allah bazan sake wannan rayuwarba Abba koda ace buÆ™ata zata kasheni bazan sake kusatar haram ba, nayiwa mahaliccin na alÆ™awarin ina kuma roÆ™on kariyar sa da shiryarsa gareni kaima kuma nayi maka al'Æ™awarin har gaban abadan bazan Æ™ara kusantar zinnaba, in akwai Æ™addarar zina a rayuwata ta gaba Allah yasa ajali ya cimmin mutuwa ta É—aukeni kafin lokaci yin zina ta riskeniâ€. Ya Æ™are maganar hawaye na cika idonsa haÉ—i da yunÆ™urin tashi, cikin sanyin jiki da murya Abba yace.
“Ka shirya gobe Jidda zata zo kuje kuyi.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.