Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 6 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 49
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Da kyar ya samu ya dawo parlour kan 3 seatter ya kwanta bayan ya kunna room heater. saboda masifeffen sanyin da yakeji har cikin hanjinsa da ƙashi da bargon jikinsa wanda yasa ko idonsa baya iya buɗewa.
Yah Saleh dake shigowa ne yayi saurin ƙarasowa ciki tare da cewa.
“Yah Salam Mahmoud lfy kuwa? Meke damunka? Ina matar takaâ€. Ya Æ™are maganar cikin kiÉ—imar ganin irin Æ™arÆ™arwa da jikin Mahmoud É—in yake da wani irin galabaitaccen yanayin ganin ba alamar zai iya magna ne yasashi saurin tallaÉ“eshi ya miÆ™ar dashi tsaye yana mai kwalawa mai PA É—in Mahmoud dake Æ™asar kira. Arda! Arda! Da gudu Arda ya iso, key É—in motarsa ya miÆ™awa Arda tare da cewa ya juyo motar.
Suna shiga ba inda suka tsaya sai tamfatsetsen Asibitin.
Acibadem Maslak Hospital.
Ita kuwa Fariyda Chart take yi da Aunty Saddiqa. “Nifa ban san inda yake bama, Aunty Saddiqa tun ranar da mukazo da ya fita bai Æ™ara shigowa ba, kuma wai Umminsa tace bai da lfy Mamy ma na tambayata ya jikinsa jiya har Baba Malam kirana yayi wai ya jikinsa Abba yace mai baida lfy yana kiran wayarsa kuma bai É—agabaâ€. Cikin kaÉ—uwa Saddiqa tace.
“innalillahi ke Fariyda bashi da lfy kuma baki san inda yake ba, baki kuma faÉ—awa iyayensa ba, in har ke bakya bukatar rayuwarsa ai su kam suna buÆ™atar É—ansu, ta yaya ma ke da bakinkifa kikace tun ranar da kuka baro India kinga kamar baida lfy, Sannan ya fita bai dawoba ai sai kiyi gaggawar gayawa iyayensa, su san cewa bakwa tare da shi wuri É—ayaâ€.
Da sauri tace.
"To ai ranar da Ummi ta kirani suna Katsina nace mata baya nan ma aiâ€. Cikin sauri tace.
“No Fariyda wannan ai ba hujja bace, ko ni da kike cemin baya nanma fa in muna waya ai a zatona kawai irin ya fita É—in nanne to ya zasu gane? yanzu kin san halin da yake ciki gashi ana kiransa baya É—aga waya kin san kuwa illar da sakacinki a kanshi zai iya jawowa wlh in wani mummunan abu ya samu Mahmoud nasan Ummi da Abba ba zasu taÉ“a yafe miki ba, ke su Zaid ma in sun girma bazasu yafe mikiba in sunji labarin sakaci da kikayi da rayuwar mutumin da ya meye musu gurbin uba ya hanasu kukan maraici ya hanasu amsa sunan agola da yin agolanciâ€. Numfashi mai sanyi ta fesar cikin jin tsoro ya É—an É—arsun mata a zuciya murya a sanyaye tace. "To Aunty Saddiqa ai ban san inda yake baâ€. Cikin faÉ—a tace. "Me amfanin wayarkiâ€. A hankali tace.
"Ai bani da number saâ€. Cikin al'ajabi tace.
“Innalillahi Fariyda mijin nakine kike cewa baki da number saâ€. Idonta na cikowa da kwalla murya na rawa tace.
"Aunty Saddiqa nifa mijina ya rasu, number Yah Amin ko a bacci aka tasheni zan faÉ—eshiâ€. Cikin faÉ—a Saddiqa tace.
“Kin shiga uku Fariyda wlh Allah bazai barki ba, wai duk wannan abun akan Aminullah da ya rigada ya bar doron duniya kikeyinsa, Wlh ko shi Aminullah da ace yana raye sai yayi fushi dake akan riÆ™on sakainar kashin da kikeyiwa Æ™aninsa, har zaki cemin ba mijinki bane mijinki ya rasu to maza sa himma shima Mahmoud É—in in ya mutu sai ki zubda ruwa Æ™asa kisha, kiyi sabon takaba in kin fita ki auri Yah Mujahid É—in da kike yawan kira. Bawan Allah ai ko dan yadda yake mutuwar son yaranki da yadda yake mutuwa akansu ya cancanci ki binciki ransa da lfyarsaâ€. Hawayen da suka fara silalo mata ta share a hankali tace.
"To ta ina zan nemeshi ni da ban wani san garinba kuma ko na nuna zan taimaka mishi gwatsaleni yakeyi yayi ta hantara yace na addibi rayuwarsa in fita harkata fa yace min wai in daina kallonsa har mayyafa yake ce minâ€.
A faÉ—ace tace.
"Ki dai ji tsoron Allah ai kince wayar Aminullah na hannunsa ba sai ki kirata ba, kuma wlh yanzu zan kira Mamy in gaya mataâ€. Da sauri tace.
"To ai zan kira dan Allah karki gayawa Mami wlh yanzu zan kirashi karki gaya mata zatayi fushi daniâ€. Daga nan ta katse kiran.
Ido ta zuba wa number Yah Amin da a ƙalla watanni goma zuwa sha ɗaya kenan rabanta da kira tun washe garin rasuwarsa. A hankali ta manna wayar a kunnenta, numfashi ta fesar jin har tayi ringing ta gama ba'a ɗagaba, kai ta jujjuya tana kuma kiransa a karo na uku shima ba'a ɗagaba kwallon daya cika mata ido ta zumbu da Yah Amin ne ringing ɗaya ma bazaiyi na biyu ba yake amsawa.
Aunty Saddiqa ta kuma kira ta gaya mata baya amsawa.
“Shike nan ai hankalinki ya kwanta, tunda Malam ma yace baya amsa kiransa kema kin kira baya amsawa sai ki shirya abinda zaki gayawa iyayensa na cin amanar da suka baki na É—aya-É—ayan É—ansu da ya rage musu, wlh ko Amina yanzu na kirata tace min yanzu kam ma wayarsa bata shiga tace ta kiraki wayarki kina waya, nace mata dani muke waya.â€
A hankali ta miƙe tsaye tana kallon su Zaid dake wasa haɗe da kiran sunansa Appiy owo owo Appiy. Sai kuma ta koma ta zauna cikin sanyi ta katse kiran Aunty Saddiqa saboda kanta daya cushe so take ta nitsu ko zata samu mafita.
Gashi duk masu kawo mata kaya da abincinma bata da ko numbersu iyakarta dasu gaisuwa sai su tambaye ta ko tana buƙatar wani abu.
A hankali ta kalli wayar ganin kiran Amina ba tare da ta amsa sallamar Fariyda ba tace.
“Fariyda wai ke É—in a ina kike ne to?â€. Cikin sanyin murya tace.
“Homey Airport hotel inda mukayi transit har yanzu a nan nakeâ€. Cikin tashin hankali tace.
“To shi kuma Mahmoud É—in fa inaga yana gidane matsalata wayarsafa bata shiga sai ta Yah Amin ita kuma baya É—agawa kuma su Yah Saleh da matarsa basa Istanbul sun É—anyi tafiya Ankaraâ€.
A hankali tace.
“Nima ban san ina yake ba Aunty Amina ina ta kiran layin Yah Amin baya É—agwaâ€. A hankali tace. “Tun ranar da yace min baida lfy na kira Yah Saleh dan in gaya masa ko zai faÉ—awa mai aikinsu ya shiga ya duba mana shi, dan number Arda da muke da ita ma bata shiga to kuma shima Yah Saleh yace tare suka tafi da mai aikin nasu kuma ya kira Arda É—in baya shiga a ranarâ€. Cikin sauri ta miÆ™e tsaye tare da cewa.
“To bari inje gidan in dubaâ€. Amina tace. “Yauwa yi sauri dan Allahâ€.
Shiru Abba yayi yana sauraron jawabin Yah Saleh dake gayawa Abba masa sun dawo daga Ankara ya shiga gidansu dan duba Mahmoud É—in saboda kiransa da ake baya shiga dashi da Arda sai layin Aminullah kuma da ba'a É—aga kiran shine ya dawo dashi daga inda ya tafi da iyalan nasa, sai kuma ya É—aura.
Da mishi bayanin mawuyacin halin da ya samu Mahmoud É—in haÉ—i da cewa.
“Abba kuma kunce da matarsa suke tare da ita kuke magna aji ya jikin nasa, to kuma ba kowafa a gidan shi kaÉ—aine ba kowa ban gantabaâ€. Cikin fargaba Abba yace.
“Yanzu dai ya jikin nasa, ina Arda É—in kumaâ€. Yana kallon Æ™ofar É—akin da suka dashi yace.
“Har yanzu basu fito da shiba, Arda kuma muna tare yacemin ai shike kula dashi, wayarsa kuma ta É“acine shiyasa layin baya shiga kuma baya son fita ya kai gyara ya bar Mahmoud É—in shi kaÉ—ai lokacin da najema ya shiga toilet ne shiyasa na samu Mahmoud É—in shi ka É—ai, yace bai san meyasa kuma wayar Mahmoud É—in bata shigabaâ€. Cikin sanyi yace. “Ka tambayeshi yasan inda Fariyda take ne?â€. Kai Arda ya gyaÉ—a masa bayan ya tambayeshi a hankali yace.
“Abba yace a hotel takeâ€. Cikin nazari Abba yake kallon Ummi dake jin duk abinda suke tattaunawa tace. “Ita Fariyda a hotel take yanzu Amina ke gaya min wai ai dama tuntuni da muke waya dasu basa tareâ€. Cikin gamsuwa Abba yace.
“Saleh a duba inda Fariyda take da yaran, in sha Allah gobe zan taho in na samu damaâ€. Ya Æ™are maganar cikin damuwa da yake dannewa a zuciyarsa, da sauri Yah Saleh yace.
"In sha Allah Abba ba sai ka zoba, inaga abin ba wani mai tada hankalin bane.†nan yayi ta kwantar masa da hankali har saida yaji Abban ya ɗan samu natsuwa.
Rungume su Zaid tayi kumayi da ƙarfi tare da rumtse idonta saboda sanyin weather ɗin da suka fito duk da cikin motane amman sanyi na ratsasu, wasu zazzafan hawaye ne taji suna ciko mata ido lokacin da Amina ke ce mata.
“Fariyda Mahmoud baida lfy sosai, Yah Saleh yace suna Acibadem Maslak Hospital zan tura miki location É—in Asbitin da room number da aka medasu, kiyi sauri kije can kada kije gida baya canâ€.
Seat din Driver ta ɗan taɓa ta faɗa mishi sunan Asbitin, hakan ne yasa ya karya kwana ya sauya hanyar tafiyar tasu. ƙara rungume Zaid da yafi ƙarƙarwa tayi duk da Sweater and Scarf Socks gloves dake libge a jikinsu. A hankali hawayenta da suka cika mata ido suka sauƙe dan yadda suke haɗa baki wurin kiran Appiy! Appiy!! A haka suka isa Asibitin.
A gajiye take É—aga kafarta sabida nauyin su Zaid dake hannunta na dama Zaitoon a na hagu.
Tafiya takeyi tana É—an duba rooms number É—in.
Numfashi mai sanyi ta fesar tare da shan wata kwanar.
Da sauri ta nufi Æ™ofar inda ta hangi Yah Saleh ya fita da sauri. tana isa bakin Æ™ofar Sajida Æ™anwar Yah Saleh yar Aunty Firdausi da Maryam matar Yah Saleh da Æ™anwarta Amira suka iso, cikin sauri Sajida ta nufi Fariyda tare da miÆ™a hannunta ta amshi su Zaid duka biyu tana rungumesu da faÉ—in “Aunty Fariyda kin isoâ€. Kai Fariyda ta gyaÉ—a mata da sauri tabi bayan Aunty Maryam da ta kalleta a yatsine ta wuce ciki Amira na biye da ita tana yiwa Fariyda wani irin kallo kishi.
Da sauri duk suka kutsa kai ciki.
Arda na tallaɓe dashi kan gadon asibiti wani irin gigitaccen kakarin amai mai dukan ƙirji yake yi wanda yake haɗe da shaƙuwa mai ƙarfi, sai ƙarƙarwa da jikinsa keyi tamkar mazari yunƙuri yake yi tamkar zai harar da hanjin cikinsa.
Cikin sauri Sajida ta juya ta fita ido cike da hawaye saboda tsoron yanayin data hangoshi yasa ta kasa tsayuwa a wurin sai kiran Amina data amsa.
Cikin nuna kulawa Aunty Maryam É—in ta iso bakin gadon tana faÉ—in.
“Innalillahi Mahmoud jikin har haka ne?â€.
Amira kuwa gefenshi ta matso gab dashi tana mishi mayataccen kallon so cikin kirsa da yauƙi tace.
“Wash Allah na, Aunty Maryam a kira Dr suzo su duba min shi ga yadda yake kakari faâ€. Ta Æ™are maganar tana yiwa Fariyda wani irin mugun kallo. Ita kuwa Fariyda cikin tsinkewar zuciyar ganin mawuyacin halin da yake cikine yasa ta Æ™ara matsowa bakin gadon kusa da Arda dai-dai kanshi ido cike da Æ™ollah ganin wani sabon yunÆ™urin daya taso masa mai haÉ—e da shaÆ™uwa da rawan sanyin da yayi masa rubdugu.
“Innalillahi Appiy sannuâ€. Ta faÉ—a da narkekkiyar muryarta da yasashi É—ago kanshi da sauri, cikin rawan jiki ya fara motsa lips É—inshi dan yin mgna amman ina kakarin ya hanashi sukuni, hannunsa da ya É—aga yake yafitota da yatsunsa alamun ta zo kusa ne yasa tayi saurin matsowa gab dashi saboda matsawa da Arda yayi.
Da ƙarfi ya fizgo hannunta tare da fizgo magna.
“Ina s...†sai kuma mgnar ta carke saboda shaƙuwa da kakari rawan sanyin da yake yi ya tsananta.
Kai ya rinƙa jujjuyawa dan jin numfashinsa na carkewa cikin shaƙuwar innalillahi shine abinda Yah Saleh da ya shigo Doctors na biye dashi a baya ya faɗa.
Da sauri Nurses É—in da suka shigo suka cewa su Maryam su basu wurin.
Haka ne yasa Arda saurin matsawa.
Aunty Maryam ta kalli Fariyda a yatsine tace.
“Ki matsa a wurin ki barsu suyi aikinsu mana tunda ke dai ba likita bace. Amira ke ki matso kusa tunda ke Nurses ce bazaki rasa taimakon da zakiyi masa baâ€.
Da ƙarfi ya ƙara damƙe hannun Fariyda dake cikin nasa tare da fara jujjuya kansa, alamu a'a karta tafi, ganin haka ne yasa ɗaya Dr yace Fariyda ta tsaya.
Yah Saleh kuwa da Arda gefe suka tsaya haka ne yasa Aunty Maryam zuwa kasa dasu, Amira kuwa wurin sawunsa ta tsaya.
Da sauri Dr ya haÉ—a wata allurar yayinda É—ayan kuma ke haÉ—a wasu na'urorin, sai Nurses É—in da ta tsaya ta É—aya gefen tana sa mishi drip tare da É—aga kan gadon.
Cikin karkarwa da yunƙurin da yafi duk sauran gami da rawan jiki ya ƙara matse tafinta hannunta cikin nasa da suka zama tamkar ƙanƙara murya a naɗe yace.
“Zaid Zaitoon i... In ... Ina suke!?â€. Ya dire mgnar da karfi. Idonta dake malalar da hawaye ta rumtse cikin subcewar kuka mai sassayan sauti ta fara girgiza mishi kai tare da fara murza tafin hannunsa cikin nata murya na rawa tace.
"Kayi shiru ka daina magna numfashinkaâ€. Kai ya fara jujjuya mata ido a birkice ya kuma fizgo mgnar cikin shaÆ™uwar yana mgnar cikin karyayyiyar murya yace.
“Ina son ganinsu, kice musu Appiy yayi missing nasu ki rinÆ™a gaya musu ina sonsuâ€. Yadda muryasa tayi Æ™asa ne yasa basa jin me yake faÉ—a sai ita kaÉ—ai ke iyajunsa itama sai da ta sunkuyo kanshi sasai kunnenta na kusa da bakinsa. Sassayan kuka mai sarÆ™afe da kiÉ—ima gigita gami da tashin hankali mai fidda nutsuwar mutum ta saki lokacin da taga duk jikinsa ya sake indonsa sun fara wani irin lumshewa murya can Æ™asan maÆ™oshinsa yace.
“Fariyyha zan mutu zan barki da maraicin su Zaid waye zai tayaki riÆ™e mana su. Please Farriyyha dan Allah karkiyi aure ki kaisu gidan wasu ki zauna a gidanmu har sai sun girmahâ€. Sai kuma kawai yaja wani dogon numfashi tare da sake hannunta.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.