Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 21 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAR MAKAFI*
Page 62
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Mallakin mijin da na aurana bayan rabuwata da Mahmoud dan bazan iya zama ba aureba, to kuma sakayyar abinda nayiwa Mahmoud kanta ya sauÆ™a last year mai gadinmu yayi mata fuaÉ—e, ba yadda banyi in rabata da shiba amman abun ya gagara a Æ™arshe muka gane sihiri yayi mata, sanin haka yasa hankalin mijina tashi, haka yasa muka bar Lagos muka koma Ibadan wlh har can ya bimu yanzu haka cikine da ita a wannan shekarun nata, ni nasan al'haÆ™in Mahmoud ne ke bibiyata shiyasa nazo da ita dan Allah Mahmoud ka yafe min ko dan in samu tseratar da rayuwar yarinyataâ€. Kusan duk a tare suka sauÆ™e ajiya zuciya tsoron da suke ciki duk ya sake musu zuÆ™ata jin cewa yarinyar ba yar Mahmoud bace basu da alaÆ™a da ita na nesa ko na kusa duk dama ba wata alama ta kama ko ta jini, jiki, fuska, da zata nuna yar Mahmoud ce.
Cikin sanyi Abba yace.
“Ni dai kam kin cutar dani cuta mafi muni dani da É—ana, amman na yafe miki domin Allah, saura in sunga zasu yafe su yafe in bazasu iya yafewaba, bazan tirsasamusu baâ€. Cikin sanyi da zubda Æ™wallan murya a sanyaye tace.
“Ɗan Allah dan Annabi da tsarkin Alkur'ani mai girma ku yafemin, ba don halinaba sai dan Allah da yace yana son masu yafiya.â€
Cikin Sanyi Ummi tace.
“Kije ko yanzu Allah ya saka min kinji yadda naji dan haka na yafe, Goggo Dada Sulaiman Salim ku yafe mata.â€
A tare sukace. "Allah ya yafe manaâ€. Amina ce ta miÆ™e tsaye tare da kallon Fariyda dake magna cikin rawan murya mai cike da rauni kuka na danne mgnar tata tace.
“Abba Ina jin zuciyata kamar zata fashe zan tashi in kamin izini bana son kallontaâ€. Ta Æ™are maganar tana kallon yadda Mahmoud É—in ke kuka mai tsuma zuciyar duk mai imani. Da sauri Amina tace.
"Ni dai bazan yafe ba, kuma Mahmoud kaima karka yafe mataâ€. Ta Æ™are maganar dana jan hannun Fariyda tada ita tsaye. Jin Abba yace. “Ba komai Fariyda kuje kawaiâ€.
Da sauri Salim ya miƙe yana kallon Idaya jin Mahmoud ɗin yana magna cikin cushewar numfashi yace.
"Abba bana son ganinta dan Allah Salim ka fitar da ita a gidan nan karka sake kawo min ita ko kusa da inda nakeâ€. Ya Æ™are maganar yana riÆ™e kansa da hannu bibbiyu sabida wani irin azabebben Headache da ya azzabeshi.
Kukaka mai sauti ta saki tare da kallon Salim dake cewa. "Mu tafi Idaya in sha Allah zasu yafe miki suma shi da Amina yanzu dai mu tafi baya son ganinki, mu tafi idan ya mike zai miki abin baki zatabaâ€. Daga nan suka fita, yayinda su Ummi duk suka rakashi da ido.
Fariyda kuwa da Amina É—akin Ummi suka wuce dan Hafiza da Samira na É—akin Goggo Dada, Huzaifa kuma yana parlour yana game a wayarsa.
Riƙe hannun Fariyda tayi tare da ci gaba da bata labarin yadda hankalin su ya tashi a wannan lokacin da yadda Yah Amin yayi ta bibiyar abin da irin addu'ar da Ummi tayi masa da azabar jinyar da yasha, da yadda yake gigicewa duk sanda ya kusanci wata wanda da nan suka gane yana wata rayuwar ta da ban, haka tai ta mata bayanan da Idaya bata san da su ba tunda a nan a gida akayi , ido cike da kwalla tace.
“Tsinenniya ce har yanzu bata da kunya a gaban mahaifinsa da mahaifiyarsa take ta maimata mana sihiri tayi masa harda cewa duk mazan da ta sani babu kamarsa hakafa muka haÉ—u da ita a Mumbai tayi ta kuranta min yadda taji daÉ—in kasancewa dashi a lokacin nayi zaton É—an iskane shima ashe sihiri tayi masa, ba kunya ba tsoron Allah a gaban Abba fa wai ai shi cikekken na mijine da ba'a samun irinsa da sauÆ™i ko tsoron Allah bataji bare kunyarmuâ€. Cikin zubda Æ™wallan murya a sanyaye Amina tace. "Akwai fa ranar da wlh Yah Amin ya samesu a hotol su biyu suka ritsashi wallahi a ranar da Yah Amin ya É—aukeshi suka dawo sai da mukayi ta kuka saboda yadda ya rinÆ™a soshe-soshen jikinsa duk yayi jazir yana kuka fa yake cewa, baya so har cewa yayi a kaishi shari'a Court a yanke mai hukuncin kisa kawai yafi masa da wannan Æ™azamar rayuwar.
Fariyda in Allah ya baki kekkyawan É—a ko Æ´a dole sai iyaye sun dage da addu'a da nema musu kariya wurin Allah ya tsare mana yaranmu da sharrin shaidan da shaiÉ—anu mutaneâ€. Ranar dai haka suka wuni gidan babu walwala, har sai bayan sallan isha Hafiz ya maida Amina Sulaiman da Mahmoud kuwa tun safe suna Parlour Abba ko salla anan sukeyi tayin jam'i dasu da Abba da Hafiz da Huzaifa, abincin da Amina ta kawo musu kuwa shine har dare dan ba wanda ya wani kula abinci.
Bayan sun raka Amina sun dawo a parlour Ummi suka zauna cikin sanyi Ummi tace.
“Fariyda kinji irin Æ™addarar Mahmoud koâ€. Kai ta sunkuyar Æ™asa cike da nauyi da kunya. Ita kuwa Ummi a hankali tace. “Ba haushe yace gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, kinga ishara akan Mahmoud dan haka ki dagewa yaranki da addu'a dan kyau ma wani lokacin masifane musamman in ya haÉ—u da kwarjini ga kuÉ—i, kuma duk girman laifin da yaranki zasu miki kar ki musu mugun fata da addu'a cikin fushi kinga Zaid sak Mahmoud ne ba inda ya barshi dan haka dashi da Zaitoon duk ki dage musu da addu'aâ€. Kai take gyaÉ—a tare da cewa.
“In sha Allah Ummiâ€. Goggo Dada ta É—auki Zaid dake kwance inda Huzaifa ya kwantar dashi ta tafi É—akintata kwantar dashi, saboda tuni Hafiza ta musu wanka ta musu shirin bacci.
“Sai da safe ko jeki kwanta dare yayi naga har goma ta wuceâ€. Cikin sanyi tace to tare da miÆ™ewa ta fita.
Mahmoud kuwa a hankali yake tafiya riƙe da kanshi ya iso parlour kukan Zaitoon da Samira da Hafiza suka barta a bedroom ɗin Fariyda ne yayi welcoming nashi.
Ido a rufe yake tafiya har lau hannunsa duka biyu na riƙe da kanshi dan zafin Headache ɗin ya ƙara ta'azzara ne saboda miƙewa tsaye da yayi da haure upstairs ɗin haka yasashi jin tamkar kan zai rabe gida biyu.
Yana shiga cikin ɗakin ya faɗa kan gadon tare da riƙe kansa gam-gam dan masifar sarawar da yakeyi haka yasa ya kasa yiwa Zaitoon komai ita kuwa ganinsa bai kulataba yasata fasa wani ihun da yasashi ƙara rumtse idanunsa dan ihun ƙara hautsina masa kai yakeyi.
Da saurinta nufi bedroom ɗin dan jiyo ihun Zaitoon ɗin ganin shi a ɗakin ne yasa ta zaro ido tare da ƙarasowa ciki ta sunkuyowa kansa ganin yadda yake wani irin jujjuya kansa da jijiyoyin sukayi ruɗu-ruɗu sai zufa da ya keto masa ya taune lip ɗinshi na ƙasa da ƙarfi.
Cikin sauri ta juya da sassarfa ta koma parlour Ummi tana faÉ—in.
“Ummi! Ummu!! Appiy fa ba lfy Ummi zo kiga yadda yake yi faâ€. Kusan a tare Ummi da ke kitchen ita da Sulaiman suka fito, Goggo Dada data fito É—akinta na biye dasu.
Suna shiga Goggo Dada ta É—auki Zaitoon dake watsa ihu, Sulaiman kuwa saurin tallabo Mahmoud É—in yayi, sai kuma ya kwantar da shi da sauri saboda jin sautin da ya saki tare da cewa. "Kaina zai fasheâ€. Da sauri Ummi ta juya ta koma parlourn Abba dan gaya mishi. Jim kaÉ—an da fitarta suka dawo tare da Abba. Da Yah Nasir a bayansu yana cewa Abba. “Dama ina anan waje a pharmacy na, yau nazo na É—an dudduba yanayin kayanmu kafin inzo kuma Malam ya bani zuma wai in kawowa su Zaid a rinÆ™a lasa musu da safe, to da naga kamar dare yayine nace bari dai in kira Fariyda inji in batayi bacci a tura ko Hafiz ya karÉ“a, dana kiran ne na jita a rikice tace min Mahmoud ba lfy kanshi na ciwo in zo da Allah inzo da First Aidbox.†Ya Æ™are maganar da saurin Æ™arasawa cikin É—akin saboda ganin yadda Mahmoud É—in ke riÆ™e da kansa da hannu duka biyu duk jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruÉ—u-ruÉ—u gwanin ban tsoro hakama na hannunsa daya damÆ™e kan dasu, da sauri ya zauna a gefensa tare da buÉ—e first Aid É—in abin gwada Bp ya É—auka ya jawo hannunsa da taimakon Sulaiman ya gwada jinin nasa, sai kuma yayi saurin É“alle wani É—an Æ™aramin mgnin a bakinsa ya sama tare da cusashi kasan harcensa, É—an Æ™aramin ledan drip É—in da ya É—auko a pharmacy É—in nasa yaja ya haÉ—a allurai, kana ya maÆ™ala mishi Æ™arin ruwan. Fariyda dake zaune gefe ta kife kanta jikin gadon, a hankali Sulaiman ya gyara masa kwanciya saboda ganin ya sake kan nashi ya fara sauÆ™e ajiyan zuciya.
Goggo Dada dake goye da Zaitoon ta sauƙe numfashi cikin sanyi tace.
“Alhamdulillah yayi bacci koâ€. Kai Dr Nasir ya gyaÉ—a yana mai gyara zaman hannunsa É—aya É—aurawa karin ruwan yace.
“Jininsa ne ya haufa Abba me ya tayar mai da hankali har haka? Dama yana da hawan jinine? Me ya É“aya masa rai har haka?â€. Kai Abba ya jinjina a hankali ya ce.
"Eh to yana da hawan jini tun lokacin rasuwar Aminullah ya sameshi,
Amman daga nan bai Æ™ara hawaba, sai kuma yau É—in dai ya tashi, saboda matsalar yar damuwar da ya samu kansa a cikiâ€. Yana tattara kayan aikin nasa yace.
"Gskya Abba a kula dashi sosai domin kare lfyarsa jininsa fa ya hau mataki mafi muni, dan Allah a kiyaye É“acin ransa, Fariyda ki kulaâ€. Ya faÉ—a yana kallon Fariyda da tayi zuru ta zuba mishi ido, gyara masa kwanciya Sulaiman yayi kana ya sauÆ™o yabi bayan Nasir da Abba dake fita, a hankali Ummi tace. “Allah ya sauÆ™a ya bashi lfyâ€. Cikin sanyi Fariyda tace. “Amin yah Allahâ€. Goggo Dada na gyara masa rufuwa ta juya ta jawo remote É—in Ac gudun AC ta Æ™ara tare da cewa.
“To saida safe ko Fariyda, su Zaid a barsu wurina nima in samu abokan kwana, kinga ke ga mara lfyâ€. Cikin sanyi ta gyaÉ—a mata kai tare da binsu da ido.
Kan bedside drawer ta zauna bayan duk sun fita, yana kwance lup alamun baccin yayi masa nannauyan kamu sai dai lip ɗinshi na ƙasa da har yanzu yake datse dashi.
Cikin jin sanyin na ratsata ta shiga bathroom wanka tayi tare da goge bakinta tayi al'walan kwanci bacci, A hankali ta fito tana ɗan leƙo fuskarsa, bacci yake sui haka yasa ta fara kimtsawa a hankali a hankali tanayi tana waiwayenshi, kullacar sirri ta shafa ta kimtsawa cikin tattausan riga da wando iya guiwa na bacci Black collor irin baƙi mai sheƙin nan daga ɗan saman rigar net ne har zuwa jikin hannun rigar da yake iya guiwar hannu, wondon ma daga ƙasa kusa da guiwarta net ɗin ne, hula tasa ta naɗe dogon gashinta ta tura a ciki bayan ta fesa turaren gashin sosai tayi wani irin mashahurin kyau ta fito kamar yar tsanar zinari bakin kayan bacci ya ƙara fidda asalin farar fatarta da ba algus sai glowing takeyi kamar star ƙirjinta cike cur da ɗan ɗakalellen cikinta ya taimakawa bayyanan kafaffun ƙirjinta sai mazaune da ƙugu da ya fita tamkar kalangu yan jajayen lips ɗin sai sheƙi sukeyi.
A hankali ta juyo ta kalleshi a karo na uku, har lau bacci yake baya ko motsi illa motsin numfashi.
Juyawa tayi ta buɗe Wordrobe ɗinta, shiru tayi tana kallon inda su Amina suka mayar mata dasu Beshid duvet blanket duk sun meadasu can sama, ɗan ɗigirgire tayi wai ko tsawonta zai kai ta samu ta jawo duvet ko blanket Amman ina ko na ƙasa da stap ɗin da suke ciki hannunta bai kai ciki sosai ba, juyowa tayi tana fuskantarsa bayan ta maida marfin Wordrobe ɗin ta rufe.
Dardumar sallanta ta shimfiɗa kan Turkesh carpert dake gaban gadon, sai kuma ta ɗauko babban hijabin sallanta ta ƙara yaryaɗa mai turaren Hayatii da Oud Ma'aroop, ta zurashi jikinta da sauri dan sanyin dake busota na ac da aka ƙure masa, pillow ta jawo ta wurga kan dardumar ta kwanta bayan tayi addu'a ta shafa.
Ƙarfe biyu dai-dai ya tashi zaune, yana mai lumshe idanunsa saboda hasken da ta bari a kunne sai kuma ya buɗe idon cike da mmkin ganin inda yake, ido ya zuba mata ta wani duƙunƙune jikinta ta haɗe wuri ɗaya har guiwowinta na taɓa ƙirjinta, ta tura ɗan lip ɗinta na ƙasa na sama kuma ta kamashi ta ciki tana tsotsa a hankali, na ƙasan sai sheƙi yake yi da ɗaukar ido yayi irin jannan mai jan hankali saboda ɗan tattarewa da yayi alamun sanyin yayi mata yawa.
A hankali yake jujjuya kanshi yana kallon ɗakin tunowa da kukan Zaitoon ne ya kawoshi ya sashi ɗan waige-waige ganin babu Zaitoon ɗin ne yasa ya miƙe a hankali yana shaƙan ni'imtaccen ƙamshin sai kuma ya rufe idansa dan sarawa da kan nasa yayi wanda hakan ya tuna mishi lokacin da ta shigo da fita da tayi da gudu da shigowarsu Ummi bathroom ya shiga bayan kamar 6 minute ya fito da alamun yayi alwalar kwanciya da baiyiba gashi nafila yakeso yayi kuma sarawan kan yafi tsananta in yana tsaye, kanta ya sunkuya tare da ɗagata ciɗak da sauri ta maƙale wuyansa haɗe da manna kanta a ƙirjinsa, kwantar da ita yayi ɗaya gefen ya jawo duvet ɗin ya rufe ta yana kallon yadda take shan lip ɗinta sai kuma ya kalli na ƙasan.
Baki ya taɓe ya komai ya kwanta ɗaya gefe.
Ƙarfe biyar dai-dai ta farka, cikin mmki take kallon inda ta kwanta da kuma inda ta farka sai kuma ta kalli inda yake kwance baya nan, motsin ruwa da taji a bathroom ne ya tabbar mata shine.
Da sauri tayi ƙasa da kanta lokacin da ya fito da alamun wanka yayi dan taji ƙamshin showergel ɗinta, a ɗan fakaice ya kalleta ganin yadda take kallon inda ta kwanta da kuma inda ta tashi ta samu kanta towel ɗinta dake hannunsa yana goge sumar kansa ta kalla sai kuma ta sauƙa kan gadon ta raɓa gefe ta shiga bathroom.
Wanka tayi da brush kana tayi alwan ta maida kayan jikin nata.
Kan gadon ta hangoshi kwance ya rufe jikinsa duka har kanshi saboda zazzaɓi da ya rufe shi ko Azkarul Sabah bai samu yayiba da ya idar da salla ya hau gado ya kwanta yana azkar ɗin, kunne ta ɗan ƙasa saboda jin kamar yana sambatune, sai kuma ta buɗe Wordrobe ɗinta tattausar Turkish Abaya ta zura kan kayan bacci tare da yin Rollin kanta da mayafin.
Bayan ta idar da salla tayi azkar ne ta miƙe a hankali dan jin har yanzu yana sambatun da rawan sanyi a hankali ta ƙara matsowa ta inda yake sosai, cikin sanyi tace.
“Appiy zazzaÉ“i koâ€. Ba tare da ya buÉ—e kansaba ya gyaÉ—a mata kai alamar eh, hannu tasa ta É—an ja duvet É—in ta fidda fuskarsa a hankali ta kuma cewa.
"Wanka kayi da ruwan sanyi koâ€. Yana É—an buÉ—e idonsa yace.
“Uhmmmâ€. Tana kallon yadda ya takure tace.
"In kashe Ac ne?â€. Fuska ya kwaÉ“e tamkar zaiyi mata kuka a É—an faÉ—ace yace.
"Ban saki baâ€. Baki ta taÉ“e a ranta tace. “To Ayagi sarkin faÉ—a naji ai dama ance in baka da lfy kafi bala'i da iya baÆ™ar mgna, a fili kuma tace.
"In kawo ma teaâ€. Bai kulata ba kuma bai rufe idonshi ba bai kuma juya kanshi ba sai fuskarta da ya tsare da kallo more Especially lips É—inta dake sheÆ™i, ganin yadda yake kallonta ne haka yasa ta juya ta fita parlour a kan Centre table É—in su na parlour ta samu Tray É—auke da kayan tea da cups biyu da flacks da bread mai taushi bisa dukkan alamu Goggo Dada ne ta kowo musu É—aukowa tayi.
A kan bedside drawer ta ajiye tare da zama bakin gadon cikin ƙosawa da sanyin tace.
“Appiy in haÉ—ama tea kasha kafin kasha mganinka sai ka maida baccinâ€. Da sauri ya jujjuya mata kai alamun a'a bazai shaba, sai kuma ya lumshe idanunsa, bayan kamar 4 minutes ya buÉ—esu saboda jin shiru, har yanzu tana zaune ta jingina bayanta da kan gadon idonta da suka lumshe alamun bacci takeji ya É—an kalla cikin baccin da ya fara É—ibarsan yace.
“Kwanta kiyi bacciâ€. Kai ta jujjuya mishi tare da gyara zamanta tana kallonsa, shi kuwa baki ya taÉ“e ya maida ido ya lumshe jin shiru bata tashiba bata kwanta bane ya kuma buÉ—e ido tana zaune a wurin tana lumshe da ido 47 seconds to one minute ta kuma buÉ—esu, da hannunsa yayi mata alamun ta matso kusa ta kwanta, kai ta jujjuya alamun a'a, É—an tsaki yaja ya rufe kansa da duvet.
Bayan 16 minute ya buɗe kai yana kallonta tuni tayi bacci a zaune mayafin Abayar ya zame yayi ƙasa gashinta ya zubo kan kafaɗarta, kwaffa yayi yana mai lumshe manyan idanunsa haɗe da shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinta yasa hannunsa ya jawota jikinsa da hannunsa ɗaya, ɗaya hannun kuma ya miƙar dashi yayi mata pillow ya ɗaura kanta a kan damtsen hannunsa numfashi mai nauyi ya fesar haɗi da sa ƙafarsa ya...........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.