Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 11 of 35
Ganinta sukayi zaune a k'asa warwas dafe da k'ugu tana kuka tana fad'in wayyo dijama kin lahantani wayyo k'uguna."
Dijama na ganinsu taja da baya ta koma hanyar gida, ta arce da gudu, basu ankaraba sai ganinta sukayi tana gudu kamar filfilwa ta kusan shanye kwanar gidansu." Dijama ba dai guduba kamar mai Aljanun gudu."
Saurayin Antyn lantana yace "nayi Alk'awarin tunda dijama tashigo gonata saina saita mata hankali A garin nan."
Yashiga taimakon budurwanshi ya mik'ar da ita tsaye ya rakata yarakata har k'ofar gida sannan ya juya ya tafi."
Dijama na shanye kwana gidansu sai hango motar Abban kano tayi a jiye a k'ofar gidansu, murna tashigayi tun daga nesa ta dinga stalle Tana "Abba oyoyo."
Kai tsaye taje kan jikinshi ta fad'a tana dariya tana murna ganinshi domin Abban kano yana sonta sosai,
Murna yayi da ganinta yashiga shafar bayanta yana fad'in "Iye Ummie na ta girma, kina nan kina karatu kuwa?"
Taji gabanta ya fad'i domin Abba baya wasa idan akazo fagen karatu."
Tayi saurin kauda maganar da cewa "Abba ina su fateemah?"
Yayi dariya yace sunanan lfyrsu glau, suna gaisheku."
Anan suka shiga shirya Kaka domin a d'aukeshi a tafi dashi asibity dake cikin garin domin a kuma diba mashi lfyar k'afarshi."
Alhmdulillah anyi mashi aune aune angano ciwon k'afar da sauk'i, aka rubuta mashi magani Abba yasawo mashi sann suka dawo gida."
Anan Abba yace zai kwana sai gobe idan yaga ynda jikin Kaka ya kwana snn sai yatafi gida ko da marecene yatashi safiyar _Monday_ a garin kano."
Tun zuwansa garin bai hutaba, mutane ne cingim a k'ofar gidan tsofaffi da samari,
Abba sai rarraba masu kud'i yakeyi suna godiya tare da sanya mashi Albarka."
Abba mutum ne mai taimako da tausayi, wannan dalilin ne yasa mutanen cikin garin tofa suke mutuntashi da darajashi."
Washe garin ranar lahadi da safe, misalin k'arfe goma na safe,
Abba yana stakar gida zaune, tsohuwa na gefensa d'aya gefensa Kaka ne zaune da sandarsa gefensa a jiye, Abba yana b'are mashi ayaba yana bashi yanaci had'ida sanya mashi Albarka."
Dijama na cikin d'aki zaune ta fito daga wanka tana tsara kwanliya." Fuskarta tasha kwalli da jambaki da hoda."
Tsohuwa tashiga kiran sunanta tana fad'in "dijama kiyi Sauri Ki shirya kizo na aikeki gidan kuluwa ki kaimata tsarabarda bbnki yazo da ita."
To dijama tace had'ida mik'ewa tsaye ta d'auki kayanta tasanya
Snn ta fito."
Tsohuwa ta mik'a mata Leda cike da ayaba da lemu tace "ungo ki kai mata kuma Dan Allah karki tsaya a kan hanya."
Tace "to." Ta karb'a had'ida fita, Abba ya dubita yayi murmushi yace "Ummie ba dai wayoba."
Tsohuwa tayi dariya,
Kaka kuma yace "hmmm yaja bakinshi yayi shuru."
Bayan ta dawo aiken datsohuwa tsohuwa tayi mata tana tafiyarta a hanya tana wak'a tana rawa, tana d'an karkad'a k'ugunta."
Wazata gani Buba tagani a gabanta yana wasar Baki yana fad'in dijamata kinyi kyau wnn kwanliya hkan."
Bakin buba ta kalla inda har ynzun bai iyar da warkewa ba daga kumburin da yayi."
Batasan lokacin da dariya ta sub'uce mata ba,
Ta dubeshi tana dariya tace "Wai amma dai Yaya mahmud ya iya duka."
Wai kai Buba kana aikin me harya kumbura baka Baki, ta kuma shek'ewa da dariya, ta dubeshi
Tace a hkan kake cewa zaka aureni. Allah ya tsaran da auren ragon mutum kamarka,
Ni nafison na aure jarumin namiji mai firgita 'yan maxa, amma kai ai macce ne."
Ta rab'ashi ta wuce tana dariya,
Buba yaji haushi ya k'ulu iya k'uluwa, idonsa ya canza launi zuwa ja, ya zunduma ashar, Wanda yasa dijama saurin juyowa da sauri tana kallonsa."
Yace "duk son da nake maki dijama yau bazai hana naci ...... Ya zunduba wani kalar shar ya dafawa dijama da saurinshi cikin hushi."
Dijama na ganin hakan ta zuba da gudu ai kuwa buba ya dafa mata, da yaranshi."
Gudu takeyi tana kuwa tana fad'in "wayyo Allah jama'a kutaimakeni 'yan fashi wayyo Allah 'yan fashi.da makami"
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*10*
Gafda da sallar magariba suka isa gida,
Horn Abba yakeyi baba maigadi yafito da saurinshi ya bud'e mashi get yashigar da motar sa."
Dijama sai waige waige takeyi tana kallon yanayin tsarin ginin gida."
Abba da kansa ya bud'e mata murfin mota tafito, ya zagaya but ya d'auko jakar kayanta ya rik'e mata suka jera a tare suka shiga ciki."
Gaba d'aya family gidan suna kan dinner table suna cin abinci cike da burgewa, Abba yayi sallama da gudu Fatima ta rugo ta rungumeshi tana oyoyo Abba."
Ba Wanda ya lura da dijama a gefensa, yaya muhmud daya kai lomar tuwon shinkafa miyar a gushi a bakinsa ya d'aga kansa sama yana murmushi zaiyiwa Abba sannu da zuwa karaf yayi da dijama a tsaye a gefen Abba."
Kasa iyar da had'iye tuwon yayi, ya rik'e baki yana nuna dijama batare da yayi maganaba."
Sai a lokacin hankalin kowa ya tafi wurin dijama dake tsaye sai zarar ido takeyi,
Khalil na ganin hakan yatashi yaje wurin Abba yayi mashi sannu da zuwa, had'ida kallon dijama ya mere baki☹
Ya ranb'a ta gefensu yayi tafiyar shi."
Khalil dama hakan yake ko oho gareshi, a rayuwarshi bbu abunda ya tsana sama da mutumin k'auye bagidaje, ko kuma yayi ido biyu da mummunar mace,
Wnn dalili. Yasa baya zuwa Tofa gurin Tsohuwa,
Ya kuma yiwa kansa Alk'awarin bazai tab'a auren macce mummunaba, ko bagidajiya, sai Wanda ta amsa sunanta macce ta ko ina."
Fateema tayi saurin sakin Abba taje ta rungume dijama tana fad'in oyoyo dijamar tsohuwa kai amma. Naji dad'in zuwanki."
Hakan itama momy tazo ta kama hannun dijama gaba d'aya suka zauna a kan kujera har da Abba."
Mahmud dake zaune a kan dinner table ya kasa motsawa kamar wani mattance saboda ankawo masu fita a gida."
Muryar Abba ta ankarar dashi dayaji yana cewa "mahmud lfy kake kuwa ka k'ame wuri d'aya kamar Wanda baya motsi,
Bakaga 'yar gidan taka bace Ummie?"
Bayan nan tukuna tashi mutafi masallaci mu farayin sallah sann mudawo muyi magana."
Mik'ewa sukayi suka nufi masallaci domin gabatar da sallar magariba."
Da fitarsu momy ta kama hannun dijama cike da kulawa tace "ummie ya hanya?" Ya kuka baro Kaka da tsohuwa?"
Dijama tace "lafiya glau sunce a gaisheku."
Murmushi momy tayi, ta kai dibonta ga fateema tace "fateema d'auki kayan 'yar uwarki ki kaimata d'akinki, kibata ruwa tayi Arwala kuyi sallah ki kuma taimaka mata ta cire kayan jikinta kibata d'aya daga cikin kayanki ta sanya sannan kufito taci abinci."
Cikin ladabi da biyayya fateema ta "amsa da to mmy, sann ta d'auki jakar kayan dijama had'ida rik'a hannunta suka nufi d'akin fateema. Ita dai dijama biye take sai zarar ido takeyi tana kale kale."
Suna tafiya momy itama ta tashi tayi Arwala tayi sallah, tana kammalawa yayi dai dai da shigowar Abba da mahmud."
Abba ya dubi Mahmud yace "kaje kafad'awa khalil da zarar munyi sallar isha'i kuzo gaba d'ayanku inaso zanyi mgna daku."
Mahmud ya d'an runsuna yace "to Abba."
Yana so ya tambayeshi dalilin da yasa yazo da dijama masifa amma baiga fuskaba a wurin Abba hakan yanufi d'akinshi da yana sak'awa yana kwancewa a ransa."
Bayan Abba yayi wanka yaci abinci yayi sallah isha'i yana gincire a tsakar falonshi momy na gefenshi tana yanka mashi kankana tana bashi yana sha suna firarsu cike da kulawa da sha'awa."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.