Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 33 of 35
Mahmud ya rik'e baki yana dariya yace "Abba mommy nan ce fa?"
Abba yace b'ace mun dagani Mahmud karna sab'a maka." Ai uwa batafi uwaba😊
Suka Sanya dariya gaba d'ayansu ya mik'e tsaye ya kalli Khalil yace muje ka rakani d'an uwa."
Ba ynda Khalil ya iya hakan ya mik'e tsaye, yabi bayansa, Abba da mommy suka bisu da Addu'ar adawo lfy."
Suka d'auki hanyar makarantar su dijama."
Suna cikin ofishin shugaban makaranta suna hira,
Mahmud nayi masa godiya hak'urin da yyitayi da dijama suka rik'eta batare da sun kuretaba."
Shugaba dariya kawai ykeyi, Khalil kuma yana zaune gefe d'aya yana murmushin da yafi kuka ciwo."
Wata siririyar murya tayi sallama ta shigo, ciki natsuwa, Wanda Khalil yanajin muryar sai da gabansa ya fad'i domin yasan mai wnn muryar ko ba'a fad'aba dijama ce."
Cikin uniform dinta take Wanda sukayi mata kyau tana shigowa cikin natsuwa ta fara cin karo da Khalil ta had'e fuskar had'ida murgud'a baki domin bata lura da Mahmud ba dayake zaune a kusa da Khalil duk a tunaninta Khalil ne yazo ya aika akirata."
Mahmud kuma ya tsura mata ido yana kallonta saboda mmkin ynda yaga ta canza masa kasa yin magana yyi."
Idonta ta wurga cike da tsiwa ta kalli kusa da Khalil d'in tayi ido biyu da Mahmud,
Wata kalar dariya tasaki tare da ihu cike da murna tayi kansa ta fad'a kan jikinsa tana fad'in oyoyo yaya Mahmud I miss you."
Runtse idonsa Khalil yyi ynajin wni Abu na masa yawo a zuciyarsa."
Mahmud bai San lokacin da ya maida ita a jikinsa ya rungumeta tsaf yana sauke ajiyar zuciya Wanda bai San yana yintaba cike da farin ciki. Ya lumshe idonsa."
🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar Gidan tsohuwa_)😅
Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*30*
Sai da suka d'auki kusan minti biyar a hakan snn mahmud ya cireta a jikinsa, had'ida rik'e mata hannu still idonsa a kanta yana kallonta yana murmushi."
Gefensa taje ta zauna a kusa dashi akan kujera ta zuba mashi ido tana kallonsa tana murmushin farin ciki."
Can ta nisa taja dogon ajiyar zuciya tace "shine ka kawoni nan kayi tafiyarka inda bnsan kowa ba, bayan kayi mun alk'awarin cewa danayi wata d'aya zakazo ka d'aukeni ka cireni ka cireni a wnn mkrantar.
Meyasa katafi ka barni?"
Bata barshi yayi maganaba taci gaba da cewa, had'ida kallonsa "tab yaya kaga ynda kayi kyau kuwa?"
Dama hakan aikin soja yake sanya mutum yayi kyau ya zama kamar balarabe?"
Dafe kai yayi, yace "dijamah halinki yana nan har ynzun baki canxaba."
Ta marairace fuska cikin shagwab'a Wanda ta kuma yi mata kyau tace "Allah na canza ka tambayi uncle kaji. Ganinka ne kawai sanyani nishad'i Dan Allah yaya karka tafi kabarni kai fa kayimun Alk'awari."
Magana takeyi amma kallonta yakeyi irin ynda take shagwab'a abun yyi mta kyau saiji yyi ta kuma shiga ransa,
Tunda aka haifi dijama yake sonta domin duk a cikin qannenshi yafi sonta a kan kowa, rashin jin da takeyine da rashin karatu yake had'ashi da ita, yake nuna mata kamar baya sonta domin kawai ta tsaya tayi karatu.
Ya kuma rik'o hannunta ya mik'ar da ita tsaye zuwa jikinsa,
hakan ya yasanya khalil yasaki wayar hannunsa bai saniba,
saka makon wani a zababben bugun zuciya da yaji k'irjinsa nyi masa.'
Mahmud bai lura da shiba hankalinsa na wurin dijama sai zuba masa shagwab'a takeyi tana kan k'afarsa zaune."
Labari take bashi na Anty rukayya irin karamcin da tayi mata da taimako."
Mahmud yace "wnn Anty rukayyah Allah ya biyata,
Akira mun ita nayi mata godiya."
Tasaki dariya Wanda sai da khalil ya runtse idonsa,
Tace "yaya Ashe kaga wnn turaren a d'akinka."
Ya kalleta cike da mmki yace "kece kika ajiyeshi?"
Ta langwab'e kai Wanda yin hkan ya k'ara mata kyau tace "tsarabarka ce Dana ajiye maka, lokacin da akayi mana hutu,
saboda nasanka kana da son turare, shine na ajiyema a d'akinka Dan kadda fateema tace nabata."
Khalil najin hakan hnkalinsa ya kuma tashi wayar hannunsa ta kuma sub'ucewa ta fad'i a karo na biyu, duk ta farfashe glass d'inta,
wnda yasa hankalin mahmud ya dawo Kansa,
Yace "subuhanallah."
D'an uwa meke faruwa?" Ya akayi hakan ya faru?"
Khalil da idonsa yyi masa ja, gaba d'aya duk haushin mahmud yakeji, wato bai Masan ko maike faruwa ba kenan."
Dakewa yyi ya k'irk'iro murmushin Dole yace "nima bnsaniba tana hannuna ta fad'i."
Dijama ta kallesa sukayi ido biyu ta wurga masa harara ta kawar da idonta."
Khalil na ganin hakan ya mik'e tsaye yace brother bari natafi mota na jiraka kaina keyimun ciwo."
Mahmud yace "eyya sorry to kaje ka zauna kajira yanzun zanfito sai mutafi gida."
Mahmud ya kalli dijama yace "bakiyiwa yayanki sannu ba?"
Ta shagwab'e fuska tace " ai shine."
Khalil najin tace hakan tun kafin ta k'arasa fad'in abunda zata fad'a yayi saurin ficewarsa, ya bar wurin domin duk a tunaninsa tonawar zatayi."
Mahmud yace "ai shine me?"
Meya mki?"
Ta turo bki tace "ai shine ya tsaneni baya son ya bud'i ido ya ganni."
Mahmud yyi murmushi yace "wnn kuma saboda bakyason karatu shiyasa kowa yake nuna mki baya sonki."
Amma tinda ynxun kina karatu kowa zai shirya dake."
Khalil yana shiga mota ya had'a kansa da sitiyarin mota, zuciyarsa na k'una, wani kalar azababben son dijama yakeji a ransa Wanda idan ya rasata jiyakeyi kamar zai iya rasa rayuwarsa."
Photon dariyar da takeyiwa Mahmud da shagwab'a da yanda suka rungume juna yake gani a idonsa, ko ba'a fad'a makaba da zarar ka gansu a hakan zaka tabbatarwa kanka da cewa masoya ne suna son junansu kuma sun shak'u da junansu."
Mahmud bai fito ofice d'in shugaba ba sai da yayi masa kyauta ta ban mmki snn ya nemi Alfarma da amayar da dijama aji uku tunda ya fahimci cewa tana da k'ok'ari sosai kuma tayi girma aji d'aya."
Anan take Shugaban mkrnta ya Amince domin shi kansa yyi wnn tunanin domin ya yaba da karatun dijama domin tana d'aya daga cikin d'aliban da makaranta take Alfahari dasu."
Anan sukayi sallama mahmud yafito tare da dijama ta biyoshi tayi masa rakiya sai shagwab'a take zuba masa tare da yimasa k'orafin ita dai a fitar da ita a mkrantar nan."
Murmushi kawai mahmud yakeyi tare da bata hak'uri."
Ahakan har ta kaishi bakin Mota, khalil ya had'a kansa da sitiyari yanajin duk abunda suke fad'a zuciyarsa na suya."
Mahmud ya shiga mazaunin direba ya zauna had'ida yimasa sannu snn yaja motar suka tafi, tare da yiwa dijama Alk'awarin cewa zai dawo nan da sati d'aya."
Cike da farin ciki yake tuk'i,
ya rasa dalilin farin cikinsa sai murmushi yakeyi yana shafar sajansa."
Khalil yana lura da hakan, sai ji yayi kansa ya kuma Sara masa."
Ahakan har suka kawo gida kai tsaye khalil ya bud'e murfin mota ya fito batare da yabi ta takan mahmud ba bare ya kallesa kai tsaye b'angarensa mahmud yaga ya nufa."
Ido Mahmud ya bisa dashi yana mmki, tare da tambayar kansa duk ciwon kan ne hakan?" Ko dai da akwai abunda yake damunsa."?
******************
Wata d'aya da rantsar dasu mahmud a aikin soja kud'ad'ensa suka fito,
masu yawa wad'anda har ya rasa abunda zaiyi dasu.
Snn kuma anyi posting d'insa a inda zai fara aikinsa a nan cikin garin Abuja tare da commondent general, dashida abokinsa sulaiman."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.