Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 5 of 35
Nawane kud'in manka?"
kafad'i ko nawa ne sai na biyaka."
D'an taxi yayi murmushi yace "dubu biyu ne tsohuwa."
Tsohuwa ta kama bakin zanenta ta kwanto dubu biyu ta mik'awa d'an taxi.
Sannan ta janyo hannun dijama had'ida wurgawa mahmud harara."
D'an taxi yace "kin fanshi jikanyarki tsohuwa, amma kija mata kunne Dan na rantse banda darajar wannan mutumin,
ya nuna Mahmud dake tsaye
da konawa kika biyani sai nayi mata dukan tsiya a wurin nan kafin na kyaleta."
Dijama ta dubeshi cike da tsewa tace "mudai Dan Allah karka cika mana kunne da suruto tunda anbiyaka kud'inka sai kaja akwalar motarka kabar mana k'ofar gida."
Ta d'aga kai ta dubi tsofafin da suka zagayesu suna kallonsu ko hak'uri bazasu iya bayarwa ba,
Ta girgiza kai tace "duk wad'anda ke wurin nan babba da yaro duk na ganku, zamu had'e daku,"
Sunajin hakan kowa ya watse ya kama gabansa, saboda sanin halinta, d'iyansu da jikokinsu bazasu zauna lafiya ba, wurin dijama."
D'an taxi yaja motarsa yayi tafiyarsa,
Tsohuwa taja hannun dijama suka nufi cikin gida."
Mahmud na ganin hakan ya fasa shiga cikin gidan saboda masifar tsohuwa shima ya kama gabansa."
Tabarma tsohuwa ta d'auko ta shinfid'a mata a k'ofar d'aki, tana jera mata sannu had'ida yimata fifita inda Mahmud ya daketa wurin duk yayi kwancin bulala gashi Abu ga farin mutum."
Tsohuwa ranta yakai k'ololuwa wurin b'aci sai masifa takeyi tana fad'in bari mamuda d'in ya shigo, yazo ya had'a kayanshi yayi yafiyarshi gidansu, ni banga amfanin tahowar nan tashiba, tunda yazo garin nan kullum cikin d'aga maki hankali yake."
Dijama ta kuma marairaicewa sai nishi takeyi kamar Wanda zata mutuwa."
Wasa wasa jikin dijama ya d'auki zafi alamar zazzab'i yakeson rufeta,
Hankalin tsohuwa ya kuma tashi ta mik'e tsaye tashiga d'aki ta d'auko mata maganin zazzab'i ta k'ak'k'are mata tabata tasha, sannan barci mai nauyi ya d'auketa."
Yinin ranar dijama ko k'ofar gida bata fitaba, jinya tajeyi."
Sai bayan sallar isha'i Mahmud ya dawo, gidan
Da sallama yashigo ya,Tarar da tsohuwa zauna,
K'asa k'asa ta amsa mashi had'ida kauda idonta gefe d'aya hushi takeyi dashi."
Murmushi yayi had'ida girgiza kai domin yasan za'ayi hakan tunda ya tab'a 'yar gidan tsohuwa."
Ya kuma kallon tsohuwa yace " 'yar tsohuwa hushi kikeyi da namijin naki, to kwantar da hankalinki na kusan tattara kayana na barmaku garinku nayi tafiyata gidanmu"
Yana kaiwa nan ya d'auki buta ya Shige ban d'aki."
Fitowar da zaiyi sukayi ido biyu da dijama dake kwance a gefen tsohuwa,
ta tsura mashi ido. Tanatana kallonshi
Ajiye butarshi kenan yaji ta saki dariya harda rik'e ciki tana kallonshi tana kallon k'ofar b'an d'aki."
Sai ta dubeshi ta dubi ban d'aki ta kuma b'arkewa da dariya.'
Anan take ya fahimci abunda take yiwa dariya, wato d'azun da ta iskoshi yana wanka, kenan
To metake yiwa dariya?"
Duk haushi ya kamashi yaji kamar yaje yasameta yayi ta dukanta amma ba hali, tsohuwa bazata bariba."
Amma kafin ya bar garin nan sai ya koya mata hankali, sannan yayi tafiyarshi."
Washe gari dijama taji sauk'i, sosai
Tafiya takeyi D'auke da allonta zataje makarantar islamiya ta d'ora allonta akai ta sha d'amara da gyalenta a k'ugunta,
Tafiya takeyi tana rera wak'arta tana rawa a kan hnya."
Karo taci da Salihu d'an mlam Mudi, Wanda ya koreta a makarantar boko,
Ta ajiye allonta a gefe d'aya,
tasha gabanshi yana d'auke da markad'en kayan miya a Kansa, ta ture markad'en ya zube,
Tace "yawwa wana nakama?"
Aidama nacewa babanka duk na kamaka sainayi maka duka, tunda har ya koreni a makaranta.
Ai kuwa ta kamashi da kokawa, saida tayi mashi dukan tsiya,
Sannan ya duk'a ya d'auki robar markad'ansa yanufi gida yana kuka."
Dijama kenan, ita ba girma garetaba sai fitina, kwata kwata shekararta goma sha hud'u a duniya."
Sai da taga yayi nisa yana tafiya yana kuka sann ta d'auki allonta tanufi mkranta."
Gafda zata isa makarantarsu
Ta kuma cin karo da Buba d'and'an mai gari tare da tawagarsa 'yan tauri."
Buba d'an maigari kowa a cikin garin tsoronsa yakeyi, Domin ya kama mutum yayi masa duka saiya karkayashi ba wani abun bane gareshi."
Allah ya d'ora mashi son dijama saboda hatsabibancinta da k'arfin hali irin nata, bugu da k'ari tafi duk 'yan matan garin kyawo."
Gabanta ya Tara, yayiwa yaransa nuni da hannu da suyi tafiyarsu zaiyi magana da masoyiyarshi."
Ita kuma dijama a duniya babu Wanda ta tsana kamar Buba, saboda shaye shayen da yakeyi, bata son ganin fuskarshi ko kad'an."
Buba ya bud'e baki yana dariya bak'ak'en hak'oransa da sukayi bak'i suka dafe wurin shan sigari🤒 suka bayyana,
Yace "dijama 'yar gidan tsohuwa matar buba duk Wanda ya tab'aki a garin nan zanci........
Murmushi tayi masa Wanda bata tab'a yimasa ba,
Domin tasamu wata dama da zata sanya buba ya rama mata dukanta da yaya mahmud yayi mata jiya."
[28/04, 20:50] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*5*
Ganin murmushin da takeyi ne, a kan fuskarta
ya kuma bawa Buba damar k'ara bud'e baki yana dariya,
Yace "dijama ki amince dani naturo magabatana a d'aura mana aure."
Dijama najin hakan ta had'e fuska had'ida ya tsine baki,
Ta dubeshi da kyau tace "Buba kanaso nadinga kulaka?" Har na aureka?"
Buba yace "abunda nake fata kenan dijamata."
Ta karkace kai tace "kasan bak'on da yazo gidanmu?"
Buba yace "mahmud kike nufi?"
Tace "kwarai kuwa, to kasani yasanya mun ido, kullum sai ya dakeni
bansan abunda na tare mashi ba.
So nakeyi ka tsoratar dashi ya daina dukana, domin kuwa duk abunda yaga inayi sai ya sanya min ido, kuma ya dakeni."
Buba ya d'aga hannu
ya zunduma ashar yace "Alk'awari nayi duk Wanda ya tab'amun ke a garin nan sai nayi gunduwa gunduwa da namansa."
Dijama tadinga tsallen tana jin dad'i tace "yawwa Buba,
Amma karka dakeshi, karkayi mashi illah, kawai dai so nake ka tsoratar dashi saboda ya daina dukana."
Buba ya kuma b'arkewa da dariya ya na kuwa ya fadin "saini na dije "yar gidan tsohuwa kowa yatab'aki agarin nan bazai kwana lafiya ba,"
Dijama najin hakan ta dinga dariya tana zugashi
"Gaskiyar Buba sai kai na dije "yar gidan tsohuwa,
nan fa tadinga zugashi yanajin dad'i saboda mahaucin son da yake mta."
Sai kuwa yakeyi yana zage2
Ita kuma ta k'ara gaba tana cewa "sakarai wawa, waye zai auri d'an shaye2, tajuya ta hngeshi yayi nisa, taja dogon tsaki had'ida murgud'a baki."
Wani gefen dad'i yacikata tana za a dakar mata yaya mahmud,haka dai har ta kai makarantar tasu",
Tana zuwa tasamu wuri a gefe d'aya ta zauna batare da ta tsokani kowaba
A Can ta dubi wani yaro ya hangame baki ya na bacci aiko tasanya hannun ta ta d'allamai baki sai da sauri ya bud'e idonshi yarik'e Baki yana kuka,
Anan take bakin nashi yayi tudu, ya kunbura."
Ta dubeshi tana dariya tace "yaro ubanka yajamaka tunda yana gani d'an taxi zai tafi dani amma ya kasa bada hak'uri sai dai yaja yayi tsaye yana kallonmu Dan haka nacire jin haushinsa a kanka."
Ta kuma matsawa gefe d'aya ta zauna,
ko wanne yaro yana zuwa afad'a masa karatu,
amma ban da ita, domin acewar ta kotaje an fad'a mata ba ganewa zatayi ba garama tayi zamanta",
Can itama sai tafara gyan gyad'i mlm dayaga tana bacci ya d'aga bulalar hannunshi ya doka mata a jiki, yana fad'in
" aikin ki kenan bacci, baki gane komai
mai kwanyar kifi keda jaki banga babban cin kuba,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.