Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 6 of 35

Ai kuwa d'alibai suka d'auki yimata dariya,
ta hasala sosai taji haushi tashiga gun guni tana mgna k'asa k'asa,
Ni dai ban daiji metake fad'aba

Can ta nisa, tace mlm zanyi fitsari?
Yace "tashi kitafi dama aikin kenan daga kashi sai fitsari, ko aci akwanta, amma kai kam wayam ba komai acikinsa sai rashin kunya,
Da kuma majina, ya mere baki yace
"ALLAH dai ya kyauta."

Rab'awa tayi ta Wuce tagefen malam, ta dubeshi ta sakar masa murmushi,
Mlm kuma harara ya kuma wurga mata,
Hmm kun dai San dijama bata murmushin banza."

bata zarce ko inaba sai cikin wani kango dake nesa da makarantar kad'an a hankali tashiga kangon tana waige waige, can ta hango leda fara,
Ta duk'a ta d'auki ledar,
Can nesa kad'an ta hango ramin cinnaka tashiga tsinta tana zubawa a cikin ledar,
Tana tsinta tana fad'in
Yau zaka ci ubanka mlm ni zaka zaga har kasa ayimun dariya,hmmmmm yau kaima za'ayi maka dariya."

sai da ta tsinci mai isarta ta zuba a ledar, ta saki dariyar mugunta sannan ta mik'e tsaye. Ta fito,
hannunta goyo a bayanta sai da tazo kusa da mlm
Ya juya bayansa yana gayawa wad'ansu d'alibai karatu,
ta faki idonsa ta lallab'a a hankali saiti rigarsa ta d'aga ledar cinnakan ta zuba mashi cikin riga d'alibai na ganinta amma ba halin yin magana."

Dama sun san za'ayi hakan, tunda malam ya zageta, tayi shuru ta nuna alamar bata damuba,
Kowa yashiga mamakin "dijama ce za a zaga bata tankaba hmmmm, akwai wata a k'asa

Mlm da yaji anfara mintsinarshi, yafara sosawa,
tun yana Sosawa a hankali harya ya zabura ya mik'e tsaye nan fa yakama susar jikinsa da sauri

d'alibai me zasuyi inba dariyaba,
kuwa takeyi tana tsalle tana tab'i da hannunta tana dariya,
tasanya d'alibai najansa tana masu wak'a suna amsawa

Itake fad'in cinnaka yaci jeshi
Sunafad'in tashi kar ya k'arama

😅
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)

Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

*6*

malm sai so she2_ yakeyi, yana hararar dijama had'ida da yimata dakuwa🖐🏿
har yakai sai da ya cire rigar sa, ganin cinnakun basu fita ba daga k'arshe ya tub'e wandon sa ya , yashiga kakkab'a ya koma daga shi sai gajeren wando."

Can saiga cinnaku suna fad'owa d'aya bayan d'aya."

tsaye yayi ya kasa magana yana sauke ajiyar zuciya,d'aya bayan d'aya
Yakasa d'aga ido ya dubi d'alibansa saboda kunya domin ya fahimci cewa duk shairin dijama ne."

Dijama tayi tsaye tana kallonshi tana dariya, ya dubeta da kyau cikin b'akin ciki da jin haushinta yace " dijama kitafi gida nakoreki karki k'ara zuwanmin mkrnta,

Ta b'arkewa da dariya had'ida rik'e ciki tana nunanshi tace
"toh saimi Dan ka Koreni,
ainaga kai kafara zagina ni kuma narama,
Harda yimin gorin ilimi, kuma ai naga shi ilimi Allah ke badashi nima ba Dan ya manta daniba,

Kuma ai naga itama 'yartaka jakace bata San komiba sai jakanci,kuma doluwa ce,

Idan ina da kwanyar kifi ita kuma kwanyar kwad'd'i ke gareta,

Ta k'are maganar had'ida mur gud'a baki, tayi tafiyarta."

Sai da tayi nisa da tafiya snn ta waigo a lokacin malma yana k'ok'arin maida kayan jikinsa tace "kuma sai naci uban Larai idan muka had'u rafi,
Tunda ka koreni, daga makarantarka, sann ta juya rik'e da Allonta, tayi tafiyarta."

Koda ta isa gida tana gunguni,
Tsohuwa ke tmbayarta lfy?
Meya dawo da ke gida ynzun?"

Idonta ya cika da hawaye tashiga fad'awa tsohuwa abunda yafaru tun daga farko hark'arshe saboda dijama duk rashin jinta bata k'arya."

Tsohuwa taja bakinta tayi shuru na minti goma, sannan tanisa tace "toh zauna kihuta, gaskiya dijama banji dad'in korarki da malam d'ahiru yayi ba."

To yanzu yazanyi? An koroki a mktantar boko, gashi yanxun islamiyar ma ankoroki.

gashi kuma ke ba k'ok'ariba,
allonki sai yayi wata ukku bakiyi wankiba, haka boko baki ganewa, to ni yanzun miye mafita?"

Dijama tayi shuru sai zarar ido takeyi Can taja dogon nishi tace

"yauwa tsohuwa tunda kinga baganewa nakeyi ba shawara kawai ki sanyani makarantar koyon sak'e sak'e, watak'ila a can nafara ganewa kinga saina koyi sak'a
dama nafison can."

Mahmud dake tsaye yana jinsu tun shigowarta me zaiyi inba dariyaba,

Yace kinko kawo shawara mai kyau, tunda da keda kwad'o bakuda wani banbanci,
Bako mai a k'wak'walwarki sai rashin kunya da gidadanci,
babu abunda kika iya, sai k'auyanci da jakanci takwalla me kan kifi me idanun mujiya." Idan har ba canxa hali kikayiba mki gama yawon makarantuba."

Murgud'a baki tayi cike da jin haushin kala mansa tace "sai naga ai kamar gado nayi a wurinka tunda kamarmu d'aya da kai."
Kuma k'wak'walwarmu d'aya,
kaga kuwa gareka na gada, yayi saurin ja da baya
yace wah?"
Ni ?Allah ya tsaren Dake."

Yana fad'ar hakan yayi waje abinsa domin ida yabiye mata zata hasalashi Dan yasan dijama badai bakiba."

Ai kuwa tsohuwa ta hau masifa, tana fad'in "da kake ce mata kwanyar kifi gareta ai dai 'yar uwarka CE, kuma jininka CE, ni dai bansan irin tsanar da kake yiwa dijamaba."

Mahmud baima San tsohuwa na masifaba yayi ficewarsa abunshi."

tafiya yakeyi yana dariyar dijama saboda rashin kunya da tayi mata yawa akai ita da kanta tasan bata gane karatu, kai Allah dai ya kyauta."

Yana shanye kwanan gidansu, bai ankaraba yaji ankwad'a masa sanda akai, waiga warda da zaiyi wa zaigani, Buba ne da yaransa sun zagayeshi suna shan taba."

Cike da mmki Mahmud yake kallonsu, zai bud'a baki yayi masu mgna suka kuma yunkurin kuma buga masa sandar a karo na biyu,
Hannunsa ya kara suka yashiga jujuwa yaron Buba ya yarb'ar dashi gefe d'aya,
nanfa danbe yakaure tsakaninsu."

Nanfa Mahmud ya shiga dukansu, baji ba gani
,duk suka zube warwas wasu kuma suka tsere a guje,
Daga cikin masu gudun harda Buba😅

D'aya daga cikinsu daya daku ya kasa iya gudu, Mahmud ya shak'o wuyanshi ya mak'areshi, yashiga tmbyarsa, "waye yasanya Ku?" Menamaku kukeso kuga bayana?"
Jinkinsa na rawa yace dijama ce tasanyamu."

"what dijama?" Yace cike da mamaki,
yanzu dijama bayan rashin kunya harda ta'addaci takeyi?"
Ya wurgar dashi gefe d'aya yayi tafiyarshi, zuciyarsa cike da bak'in ciki d mmki."

Haka ya koma gida Rigarsa rataye a kafad'arsa,
Yana shiga cikin gidan, ya ta rar da dijama tsakar gida zaune,
Tana ganinsa ta tashi da gudu ta tafad'a d'akin tsohuwa.

Baibi ta kantaba yayi shige warsa d'akinsa, yashiga har had'a kayansa, cikin akwati.
Saida ya d'auki komai nashi. Ya tallabo akwatinsa yafito."

Lokaci da yafito janye da akwati, yayi dai dai da fitowar
Tsohuwa daga band'aki ta dubeshi cike da mmki tace "Mamuda lafiya?" Ina zakaje da akwati?"

Mahmud ya dubi tsohuwa yace "gida zantafi tunda naga har anfara turomin "yan iska su dakeni
,watara na maganin b'era za a sanya min a abinci domin naci na mutu,
Dan haka tsohuwa kinga tafiyata sai wani lokacin."

Ya kai dubansa ga dijama dake zatsaye a bakin k'ofar d'aki, ta marairaice fuska,
duk bataji dad'in tafiyar da yace zaiyiba
, yace " toh meye kuma na tsayawa kina kallona?"
Zaki turosu ne su kuma tareni a hanya?",
.
Bata tanka masaba illah ta kuma sunkuyar da kanta k'asa,
, tashiga tunanin kaddai ace Buba sanyawa yayi aka daki yaya Mahmud."

Bai kuma bi takan kowaba ya Yakama hanya yayi tafiyarsa." Tsohuwa ta bishi da Addu'ar Allah ya tsareshi ya saukeshi lfy."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.