Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 26 of 35

Kai tsaye suka shiga babban falon gidan kowanne ya nufd'akinshi domin watsa ruwa ya huta."

Abba bayan ya kammala wankanshi sanye yake da jallabiya, ya kwanta rigigine a kan gado yana tunanin abubuwan da suka yita faruwa tsakanin khalil da dijama da irin magagganun da khalil yayita yi."

Momy ta turo k'ofa tashigo da sallamarta, ya amsa mata ta nemi wuri ta zauna a kusa da shi."

Ta dubeshi cike da kulawa tace "Abban yara, katashi Inaso zamuyi magana.".

Abba ya mik'e zaune had'ida da kallonta."

Itama d'in shi take kallo suka fuskanci junansu,
Snn tayi kyaran murya ta kwantar da murya cikin lumana, tace "Abba yarah, meka fahimta tsakanin khalil da Ummie?"

Abba yace "ban fahimci komaiba illah sakarcinsa da yakeso ya fito mana dashi abunda bazai tab'a yiwoba."

Domin bai isa ya sanyani na karya Alk'awarin dana d'aukarwa d'an uwanaba, kafin yabar duniya,
Tun lokacinda aka haifi Ummie na d'auketa nayi mata hud'uba, na sanya mata suna nana khadija,
marigayi ya furta da bakinshi 'yace "Allah ya rayaki Nana khadija matar mahmud,

Ya juyo ya kalleni mukayi ido biyu da shi, ya dafa kafad'ata yace "yaya ko bayan bana raye,
nana khadija matar mahmud ce Mahmud shine mijin khadija."

A lokacin naji dad'i nayi murna, sosai, hankalina bai kuma kwanciya ba sai bayan mutuwar d'an uwana naga ynda Mahmud yake kula da ummie da irin son da yake nuna mata, bayan gaba d'ayansu ba wnda yasan da wnn mgnar har zuwa ynxun da nake fad'a mki."

Karyane khalil yaxo daga baya ya karyamun Alk'awarin da na d'aukarwa d'an uwana. Bai isaba wlh sai dai soyayyar ummie tasan ynda zatayi dashi, ko kuma keda kike mahaifiyarshi ki lurar dashi kibashi hak'uri, Dan wlh ko hkri bai isa na bashiba."

Momy taga Abba ya d,auki zafi sosai, taja doguwar ajiyar zuciya tace "Allah yabaka ikon ai watar da wasiyyar d'an uwanka."

Yace "Amin cike da sanyin murya."

Ta kuma kallonshi cikin taushin murya tace "har ynxun bazanyi k'asa da murya ba wurin nemawa khalil Alfarma a wurinka akan ka amince ya fitar da matar da yakeso a aura mashi ita,
domin samun kwanciyar hankalinshi da namu baki d'aya."
Idan har kayi dibo da yanda yake yiwa 'yan mata wani kalar kallon a gaban ni da kai ya isa ya tabbatar maka da khalil ba irin mazan da za'a jamasu dogon lokacin da zasuyi aure ba."

A razane ya d'ago kai ya dubeta, yace "wai ni ko hajiya Bilkisu meyake damunki ne?"
Sau nawa kikeso nayita fad'a mki khalil bai isa aureba,

Kina hana saurayi mai lafiya yak'i kallon 'yan mata?"
Ko kuma so kikeyi da zarar yaga macce ya rik'a sunkuyar da kanshi k'asa,
Ki kuma zuwa kicemun kina ganin yaron can baya da lafiya mutashi tsaye munema mashi magani."

To bari inyi maki mai kankaf, ko bayan raina banyafe khalil yayi aure yanzunba har sai ya kammala karatunshi ya samu aiki Wanda zai zama madogara gareshi da iyalinshi baki d'aya."
na gama magana tashi Dan Allah kitafi d'akinki ina buk'atar Hutu."

_tofah Abba ya d'auki zafi_🤔

Bata kuma yin maganaba illah ta mik'e tsaye ta nufi d'akinta ranta duk a dagule."

*****************

Akwana a tashi ba wuya, mahmud har yayi wata uku da fara trening d'inshi,

A kullum Yusra da sonshi take kwana take tashi,
Duk wata hanya da macce zatabi domin ganin taja hankalin d'a namiji a waya ko a chat amma a banza takeyi."

Kullum da sabon photon da take tura mashi a chat tare da kalaman soyayya masu sanyi,
wanda da ita da wanda yake zindir basuda wani banbaci."

Duk lokacin da mahmud ya bud'e pic d'inta sai ya runtse idonshi saboda tsaraicinta da yake gani, tareda tsine mata Albarka, daga k'arshe yyi blocking d'inta,
Dama kuma baya d'aukar kiran wayarta."

Hakan da yyi mata ba k'aramin d'aga mata hankali yyiba, a rayuwarta bbu d'a namijin da ya tab'a wulak'antata kamar Mahmud,
kuka takeyi sosai irin yanda soyayya Mahmoud ta addabeta a zuciyarta"

Idan ya San wata ai bai San wataba."

K'arfe d'aya da rabbi na dare tashiga shirya birthday d'inta gobe takeso zatayi shi misalin k'arfe biyar na yamma kuma harda mahmud take buk'atar yazo,
Ko Dan saboda ta kalle kyakkyawar fuskarshi taji sanyi a ranta."

Tunda k'arfe 6:30am ta dura d'akin daddy baiko tashi daga barciba ita ta tasheshi, tana shiga shaida mashi yau ne ranar zagayowar ranar haihuwarta."

Zumur ya mik'e zaune yana murmushi yana fad'in happy birthday my daughter, ya janyota zuwa jikinshi, yace mekikeso na shirya maki natayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki?"

Ta kuma shagwabe masa a jiki tace "daddy Abu d'aya nakeso kayi mun."

Yace fad'eshi shalele kinfi k'arfin komai gareni."

Tace "daddy so nakeyi mahmud yazo yau d'in nan domin ya tayani murnar zagayowar ranar haihuwata idan kayi mun hakan daddy to ka gama bani gift d'ina na wnn shekarar wanda zanfi jin dad'insa a kan komai."

Murmushi daddy yayi ya d'anyi Jim kad'an yana tunanin fitowar mahmud a yanzun suna cikin trening dai dai yake da rugujewar wata uku da yayi yana wahalar trening d'insa
Kuma bayason ganin b'acin ran shalele gwara ya faranta mata rai,
Ran kowa ya b'aci daga ciki kuwa har da ranshi."

_BARKA DA JUMA'A DA FATAN KOWA YA WAYI SAFIYAR JUMA'A LAFIYA_
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅

Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

*24*

Can kuma yaja dogowar ajiyar zuciya ya kalli Yusra ya sakar mata murmushi,
da ya tuna _weekend_ akeyi su mahmud a yanzun basa aikin komai sai hutu."

Yace "shalele indai wnn ne bkida matsala kisanyawa ranki kamar kina tare da mahmud a yanzun hkan."

Barima kijiyewa kunnenki."

Ya lalubo wayarshi a k'ark'ashin pillownsa,
Yashiga contacts d'inshi,
ya danna lambar shugabansu mahmud wanda yake kula da duk wani motsinsu da lafiyarsu."

Hands free ya sanya wayar ynda zata iyajin maganar da ke fitowa daga cikin wayar."

Cikin girmamawa oga yake gaida Alhaji Atiku,
Cike da kulawa yake amsawa,
Snn ya shaida mashi yana buk'atar mahmud Hassan yazo Abuja yanzun nan yana nemanshi."

Zubewa k'asa oga yayi kamar Alhaji Atiku na ganinshi, yashiga bashi hak'uri,
Yana cewa "idan wani laifi yayi ranka ya dad'e ina rok'ar mashi Alfarma dan Allah ayi mashi hak'uri kar a d'auke manashi a nan,
Yaron hazik'ine yana da kwaxo sosai wurin trening gashi da son Addininshi."

Ranka ya dad'e mahmud yana Neman yafiyarka tuba yakeyi bazai sakeba."

Alhaji Atiku ya saki dariya, yace "ba abunda Mahmud yayimun sai Alheri,
Neman da nake masa sak'o nkeson na bashi _hand to hand_
Batare da kowa yasan komaiba, karka damu gobe zaidawo gareku, abunda nakeso da kai kabashi mota lafiyayya ayimata full da mai.
wanda zai iya kawoshi Abuja ya kuma maidashi batare da wata matsalaba."

Oga ya sauke ajiyar zuciya yace "angama ranka ya dad'e."

Snn Alhaji Atiku ya kashe wayar, yana kallon shalele had'ida kashe mata ido d'aya,
Dariya suka saki gaba d'ayansu ta kuma fad'awa jikinshi ta rungumeshi tana fad'in nagode daddyna kana faranta mun rai, kana yimun duk abunda nkeso, Allah ya k'ara maka yawancin rai da nisan kwana ."

*****************

Mahmud yana zaune tare da sulaiman suna hirarsu kamar ynda suka saba idan basuda aikinyi."

_massage_ yagani ya shigo a wayarsa, kamar bazai duba ba kuma dai ya tsinci kansa da yanaso yaga ko wanne irin sako ne."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.