Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 14 of 35
Ta jawo hannun dijama dake tsaye wuri d'aya tana cije baki had'ida girgiza kai, ranta ya b'aci matuk'a."
Mahmoud dake tsaye a inda yake, ya had'e fuska,
yayi saurin waigawa ya wurgawa khalil harara cike da jin haushinsa."
Mmy ta rik'o hannuta tace "zo nan 'yata na gyara maki fuskarki karki damu da abunda khalili yayi mki hka halinshi yake."
Momy tashiga gyara mata fuskarta, ta goge mata janbakin da 'yar gira, ta kuma rage mata hudar fuskarta,
Sauran kwallin da tashafa a idonta ne yak'i goguwa. Gudun karsuyi latti momy ta barta haka suka tafi."
Bayan sunfita ne Abba ya maida kallonsa ga momy yace "nafara ganin take taken khalil a gidan nan a kan ummie zan d'aukar mashi mummunan mataki idan hakan ta kuma faruwa a kan idona."
Inason Allah yabani iko da nisan kwana nacika Alk'awarin da nayiwa d'an uwana kafin ya mutu,
na aurawa muhmud Ummie idan ba hakan ba a yanda naga khalil na kyamatarta a gidan nan da bbu abunda zai hana na aura mashi ita, domin kawai naga iya karshi."
Hak'uri momy kawai take bashi domin ganin ranshi ya b'aci sosai."
A bayan mota suka shiga mahmud bai kulasuba, fuskarshi a had'e, ya tayar da
motarsa yaja yanufi makarantarsu."
Suna shiga cikin makarantar yayi parking d'in motar shi a cikin harabar makarantar,
, tun kafin ya fito dijama ta rigashi fitowa harwani sauri takeyi k'asa na tashi,
Da sauri ya doka mata tsawa yace "ke 'yar k'auye da Allah malama ki dawo ki tsaya."
Kina wata tafiya k'ura na tashi sallan ki b'atawa mutane jiki da k'asa, 'yar k'auye kawai
Takkwala mai kwanyar kifi, kamar da gske sai kace ganewa kikeyi.
To bari na fad'a mki nan ba k'auye bane mudun kikayiwa malamai rashin kunyar da kikeyi a k'auye tsinanen dukan tsiya zakici kuma ba Wanda zai rama maki."
Juyowa tayi tana kallonshi ta sunkuyar da kanta k'asa, a rayuwar ta bbu abunda ta tsana irin yaya Mahmud ya kirata da mai kwanyar kifi, ta d'aukarwa kanta Alk'awarin cewa zata maida hankali tayi karatu Wanda yaya Mahmud sai yayi mmkinta,
a lokacin zata bud'e baki ta mayar masa da raddin takkwalar da yake kiranta da ita."
A fusace ya juya wurin fateema da mmkinsa bai gantaba sai ma hangota da yayi ta kusan shigewa class."
Gaba ya shige dijama na biye dashi, office d'in shugaban mkranta ya shiga ya gabatar da dijama, sann daga k'arshe gaban idonsa aka kaita class,
Aji d'aya aka ajiyesu da fateema kamar yanda ya buk'ata, saboda fateema ta dinga koya mata wasu abubuwa wad'anda bata saniba."
Sai da yaga shigarta aji sann ya shiga motarsa ya dawo gida."
Da shigarta ajin d'alibai sai kallonta sukeyi ganin yanda ta tsurawa silin roba ido sai kallo takeyi, gaba d'aya sai k'arewa ajin kallo takeyi da kujerun dake ajiye a cikin class d'in."
Fateema ta hango a can zaune tayi saurin bud'e baki tare da d'aga murya tace "lah fati Ashe aji d'aya aka ajiyemu ai kuwa naji dad'i."
Gaba d'aya ajin suka tuntsere mata da dariya, wata 'd'iyar chiyaman d'in garin,
Wanda suke mak'otaka da Abba, tace "amma dai ke 'yar k'auyece wlh."
Suka kuma shek'e mata da dariya, wata d'aliba daga cikinsu tace "dubi yanda ta shafa kwanli a idonta, ta fad'i hakan had'ida nuna idon dijama suka kuma shek'ewa da dariya."
Dijama taji haushi sosai, fateema ta mik'e tsaye ta kama hannun dijama da tayi tsaye takasa zama saboda jin haushi, ta zaunar da ita a kan kujera kusa da ita."
Dijama taja wuri d'aya ta zauna tana sake sake a ranta,
Malam mai English ya shigo ya fara yi masu karatu ta kashe kunne ta kwantar da hankalinta tana saurare kuma tana fahimta."
K'araurawa taji an buga alamar antashi break fast, hakan yayi dai dai da fitar malma mai English, d'alibai suka fara fita waje domin cin abinci."
Da sauri dijama ta duro a kan kujera ta shagaban 'yar gidan chiyaman
karon farko mari ta fara kai mata, ta cire hijabin jikinta tasha d'amara cikin d'aga murya tace "ubnwa kike cewa 'yar k'auye?" Tashiga nusarta, baji bagani, saida bakinta ya fashe da jini,
gaba d'aya ta b'ata gaban hijabinta,
D'aya yarinya wanda harda ita wurin yi mata dariya,
ta matso wurin dijama ta cimuimuye mata riga a bayanta,
Dijama tasanya k'afa ta bayanta ta shure mata baki, aikuwa yarinya ta kwatsa ihu ta duk'e ta rik'e bakinta da jini yaketa zuba."
Ihu 'yan aji keyi da gudu suka fita suka kira shugaban makarantar."
Babu abunda fateema keyi sai aikin kuka,
Dama kuka baya mata wuya, saboda kwata kwata fateema bata da fad'a batason tashin hankali,
sanyin hali ke gareta."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*14*
12:30pm Abba ne zaune a Palo ya dawo daga office Mahmud zaune a gefensa yana shaida masa cewa Alhaji Atiku ya kirashi a waya akan cewa ya xama cikin shiri satin nan ya shirya kayansa ya sameshi Abuja domin sunansa ya fito zasu wuce wurin trening."
"Alhmdulillahi Abba yace,
Yana murmushi cike da jin dad'i da farin ciki, ya dubi Mahmud yace "Alhaji Atiku mutumin k'irkine abokina ne tare muka tashi mukayi makaranta d'aya dashi,
A rayuwata ta duniya bbu abunda Alhaji Atiku zai nema gareni banyi mashiba indai baifi k'arfinaba, saboda yanda yake nunamun k'aramci da k'auna."
Mahmud inaso idan kaje ka kula da kanka,
Kabishi sau da k'afa kayi mashi biyayya kamar yanda kasan kanayi mun Allah yayi mka Albarka."
Bai rufe bakinsaba fateema tashigo ko sallama bbu idonta yayi ja alamar taci kuka,har ta gaji."
Mahmud ya dubeta cike da kulawa yace "fateema meyasameki?"
Abba yace "ina Ummie take?"
Kafin tabasu amsa sukajiyo jiniyar motar 'yan sanda a k'ofar gida,
Saiga Baba maigadi yashigo da saurinsa ya zube k'asa gaban Abba yace "ranka ya dad'e 'yan sanda na sallama da kai a waje."
Abba ya zaro ido cike da mmki yace "yan sanda?"
Meyafaru?"
Mahmud shima hakan,
Fateema ta kuma fashewa da kuka tace "wlh sune,
Momy ta taso tashiga girgixata tana tambayarta "sune suwa?"
Meya faru?"
"Sune wad'anda suka kama dijama suka tafi da ita,
Mahmud yayi saurin juyowa ya kalleta, ya kuma kallon Abba da momy, yace "dijama tayi halinta kenan tajanyo mana fitina."
Suka d'unguma gaba d'ayansu suka fita,
Mahmud ke gaba sai Sauri yakeyi Abba na biye dashi snn momy da fateema."
Yana tukarar motar ya hango dijama zaune a bayan mota sai zarar ido takeyi"
'Yan sandan na ganin Abba sukayi saurin fitowa suna gaisuwa gareshi kasan cewar Abba ta fito takarar d'an majalisa na jahar kano,
A garin na kano, kowa yasanshi babba da yaro, kuma Abba mutum ne mai yawan Alheri ga jama'a."
Tambaya yashigayi meke faruwa?"
Anan sukashiga yi mashi bayani cike da girmamawa."
Hak'uri Abba yashiga basu, snn dga k'arshe ya d'aga waya kira ciyaman da kassila yashiga bsu hkri ya kuma shaida masu da cewa 'yarsace ta aikata hakan a bisa kuskure."
Ko wannensu mmki ykeyi,
Gnin basu san dijamaba."
Anan sukayi sallma da cewa ko mai yawuce Allah ya tsare gaba."
Snn aka fito da dijama daga cikin motar,
Abba ya d'auki kud'i masu yawa ya mik'awa 'yan sandar suka amsa suna godiya snn sukaja motarsu sukayi tafiyarsu."
Mahmud yayi kanta da sauri, ya rik'o hannunta yashige da ita d'akinsa ya sanya key yashiga jifgarta yana dukanta ba girma ba arxik'i,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.