Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 32 of 35

Ina nufin ka kwashi kayanka kaje ka mayar dasu a inda kasawosu domin kuwa Mahmud ya rigaka, babu abunda bai sawo ya turo akawo mata taba kamar yanda ya saba a koda yaushe.
Ba kamar kai daka tsira ynxun da rana tsaka."

Khalil bazan gaji da fad'a maka a kan kacire Abunda kakeso ka fito dashi a rana tsakar nan ba."

Dan haka ka kwashi kayanka ka mayar dasu a inda kafito dasu,

Ya fahimci inda maganar Abba ta nufa. Ransa ya b'aci amma kuma ya danne yace "Abba wai menayi?" Naga kamar duk an tsaneni a gidan nan?"

Sai a lokacin mommy tayi magana tace "khalil kazo ka dakemu kawai ka huta."
Tunda har tambayar abunda kayi kakeyi, ai ina ganin kafi kowa sanin Abunda ke cikin ranka Wanda bazai tab'a yiyuwaba,
Dan Allah malam tashi ka kwashe mana kayan nan naka wad'anda suka tare mana filin wuri kasan inda dare yayi maka dasu."

Jiki ba kwari ya mik'e tsaye cike da b'acin rai idonshi ya rikid'e zuwa launin ja."
Yashiga kwasar kayansa yana xubawa a mota."

Washe gari, dijama ta kammala shirinta cikin uniform ta fito sukayi sallama da mommy, da fateema."
Abba da kansa ya d'auketa ya nufi mkranta da ita."

Bayan sun wuce ne khalil ya fito cikin da kakkiyar shadda 'yar ubansu sai k'amshi yake zubawa, ya durk'usa har k'asa ya gaida mommy, snn yace "Nana khadija tafito muwuce kawai na shirya."

Mommy ta kallesa da kyau tayi murmushi irin nasu na manya tace " ai tuni Abbanku ya tafi wurin kaita."

Saurin d'aga kai yyi ka kalli mommy Wanda itama shi take kallo, ganin b'acin rai a fuskarsa ta zaro ido tace "meyafaru ne Khalil?"

"Ba komai yace had'ida mik'ewa tsaye jiki ba kwari yace "natafi makaranta."

Mommy tace break fast d'inkafa?"

D'an juyowa yyi yace "banajin yunwa idan naje can zansamu wani Abun da zanci."

"To Allah ya bada sa'a inji mommy ta bishi da kallo tana tausayin d'an nata."

**************

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah. Yau ne ake bikin rantsar dasu mahmud a aikin soja."

In da sun kammala trening d'insu cikin nasara da taimakon Allah tare da sanya hannun Alhaji Atiku Mahmud ya fito da babban muk'ami."

Bikin rantsar dasu akeyi a garin Abuja inda aka tara manya mutane shuwa gabanni da 'yan siyasa domin shaidarwa."

Abba da mommy da khalil da fateema duk Suna wurin a zazzaune inda suke hango Mahmud zaune cikin uniform d'in soja wad'anda suka yi mashi masifar kyau sai kallonsu yakeyi yana murmushi farin ciki."

Gefensa d'aya kuma sulaiman ne, shima zaune yana hango matarsa da d'ansa yana aika masu da murmushi."

Kiran sunansu akeyi d'aya bayan d'aya, ana rantsar dasu tare da fad'in muk'amin su a kuma basu ta kardar shaida."

Abba yana tare da Abokinsa Alhaji Atiku suna fira sai godiya yake masa."

Shuru Abba yayi saka makon sunan Mahumd da yaji ana kiran tare da muk'amin da yaji ba'a kira kowa dashiba,
Ya kuma kashe kunne domin ya k'arajin abunda ake fad'i."

_"CAPTAIN MAHMUD HASSAN TOFA_ yaji ana fad'i, sai ganin Mahmud yayi ya taso yana murmushi aka Shiga rantsar dashi."

Abba bai San lokacin da ya rungume Alhaji Atiku ba sai godiya yake masa, domin duk matakin da yaga Mahmud ya taka dasa hannun Shi a ciki."

Alhaji Atiku yace "ka daina yimun godiya mahmud d'ana ne. Babu abunda bazan iya yimasa a rayuwa ba"

Idan ina da rai da lafiya mahmud sai ya hau kujerar da nake kai a yanxun ta commondent general."

Abba yaji dd'i sosai har yakejin a rayuwa babu abunda ba zai iya yiwa Alhaji Atiku ba."

Hkan dai akayita rantsar dasu, d'aya bayan d'aya, snn daga k'arshe aka sallamesu da cewa kowa yatafi gida sai nan da wata d'aya idan kud'insu suka fito za'ayi posting d'insu wurin da zasu fara aiki, domin su fara yiwa k'asa aikinta."

Gidan Alhaji Atiku su Abba suka nufa, gaba d'ayansu,
A inda aka shirya masu liyafa kala kala, cikin karamci."
hakan suka taru gaba d'aya har Alhaji Atiku da matarsa suka shiga cin abincin."

Abba ya duba baiga yusra ba ya dubi Alhaji Atiku yace "Alhaji Atiku wai ni ina 'yata ne yusra bngantaba?"
tun a can nakeson na tambayeka hankalina ne ya d'auku."

Dariya Alhaji Atiku yyi yace 'ai Shalele ta tafi England wurin hutawa, .d'azun da muke waya da ita nake gaya mata yau ne ake bikin rantsar da yayanta Mahmud rigima ta sanyamun tana kuka wai meyasa ban fad'a mata ba, domin ta shiryawa mahmud kyautar da zata bashi domin tayashi murna."

Abba yace "gskya ba'a kyautawa yusra ba mutum da yayanshi."

Suka Sanya dariya gaba d'ayansu."

Mahmud bai kulasu ba sai cin abincinsa yakeyi Wanda yakejinsa kamar yana cin magani."

Domin gaba d'aya ya tsani Alhaji Atiku da duk wani Abu da yafito daga gareshi sboda yafiya son kansa da yawa."

Hakan suka kammala cin abincin ko wannensu ya mik'e tsaye had'ida yi masu sallama, Abba sai godiya kawai yake tare da mommy suka fito."

Motar Khalil Abba yashiga tare da mommy,

Khalil kuma ya shiga motar mahmud tare da fateema da mahmud d'in gaba d'aya suka d'auki hanyar kano."

K'arfe goman dare suka sauka garin kano,
Gaba d'ayansu ko wannensu a gajiye yake."

Suna sauka kai tsaye ko wanensu ya nufi b'angarensa domin ya watsa ruwa ya huta."

Mahmud yana shiga d'akinsa kai tsaye toilet yashiga yayi wanka yafito ya shinfid'a abar sallah yayi sallah sann ya fad'a kan gadonsa ya kwanta tare da sauke ajiyar zuciya, babu abunda ya fad'o masa a rai a dai dai wnn lokacin sai dijamah."

Murmushi yayi domin shi kansa ya so ya ganta, yga ynda ta koma Allah yasa dai tayi hankali ta kuma daina rashin ji."

Da tunani gobe idan Allah ya tashesu lfy zaije har mkrantar ya kaimata ziyara."

Washe gari bayan yayi shirinsa cikin k'ananun kayansa wad'anda suka karb'i jikinsa suka fitar masa da mazan takarsa na jirumin maza, cikakken soja,
Inda yake ajiye turarensa yanufa, sai ganin wani kalar turare yyi Wanda shi bai San yana da irinsaba, baima tab'a ma'amala da irin turarenba."

D'auka yayi ya fesa a jikinsa saiji yyi wani k'amshin dad'i yana fita a turaren."
Lumshi idonsa yyi domin k'amshin turaren ya sanyashi farin ciki, da har yna tunawa da wasu abubuwa da sukayita faruwa na farin ciki."

Cikin nishad'i ya fito yanufi babban falon gidan, kowa da kowa ya hallara domin k'aryawa shi kad'ai akejira."

Durk'usawa yayi har k'asa ya gaida maihaifansa, snn khalil da fateemah suma suka gaidashi cike da girmamawa, yana murmushi ya amsa masu."

Anan ya jawo kujerar da ke kusa da Khalil ya zauna suka fara yin break fast,"

Bayan sun kammala ne mahmud yace wa Abba,

Abba zanje makarantar su dijama na dubata."

Gaban Khalil ya fad'i yayi saurin d'aga kai ya dubi mahmud ya kuma sunkuyar da kansa k'asa."

Abba yyi murmushi yace "ya kamata kuwa, amma idan kayi ido biyu da ummie na zakasha k'orafi."

Snn idan kadawo, ya kamata ka shirya katafi tofa wurin tsohuwa ka gaida ita, domin tana yawan yi mun k'orafi a kanka."

Dariya mahmud yyi yace "tsohuwa matsala ni har na mnta da ita."

Abba ya turo ido waje had'ida kallon mommy ya nunata da yatsa yace "wnn ce matsala,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.