Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 17 of 35
Hakan kuma yayi wata budurwar mai suna mariam itama hakan take, kamar Salma😊
Khalil mutum ne mai yawan sha'awa sosai baya iya zaman awa biyu batare da Mace na kusa gareshiba ko ba komai yajishi kwance a kanta yana wasa da ita musamman Brest d'inta."
Amma daga yau yyi alk'awarin yabar yasmin kenan tunda har tana iya biyawa kanta buk'ata da kanta." Shi ya hak'ura
A cikin harabar makarantarsu ya shiga yayi parking FATEEMA ta fito ya juya ta madubi ya kalli dijama ta jingine da kujera sai sharar barcinta kawai takeyi."
Fuskarta ya kalla sai da gabanshi ya fad'i, yarasa dalili yin hkan,
Ya doka mata tsawa, "ke bagidajiya tashi kifito mun a mota 'yar k'auye ba sabanba sanyi Ac ya dokeki kinsaki bki kina barci."
Fitowa tayi batareda ta kulashiba, tana fitowa ya d'auki turare yashiga fesawa a motar."
Yana gamawa bai kallesuba ya wucesu yayi gaba ya nufi wurin shugaban makatantar, FATEEMA na ganin hakan tayi sauri tashige aji tana cewa dijama Allah yasa a jiyeki a jinmu."
Murmushi Dijama tayi bata tankawa fateema, tana ganin inda Khalil,
yashiga ta lallab'a takoma bayan motarshi ta tsinci k'usa a k'asa,
Ta duk'a inda ba Wanda ke iya hangota tashiga caccakar mashi Tayar mota, gaba d'aya tayarshi ta baya guda biyu sai da ta sokesu tayi mashi faci snn ta lallab'a ta nufi inda taga ya nufa."
Bayani taji yana yiwa shugaban makarantar yana fad'in "daga k'auye tafito batasan komaiba akanta, Dan haka taimaka
akaita ajin k'arshe.'
Saboda inajin lbri a bakin brother d'ina Wanda yafi kusanci da ita cewa kwanyar kifi ne gareta bata gane karatu."
Sannan batada kunya,
Allah gafarta malam kasan renon k'auye yanda Yake, Dan Allah malam karka nuna sananya ko wani abu da zarar tayi ba dai daiba ko tak'i karatu a bata kashi sosai har sai ta daina motsi."
Ya juya ya kalleta ya wurga mata harara, ya d'ebo kud'i a Aljihunsa ya mik'awa malam had'ida yi mashi sallama."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*16*
Khalil Yana wucewa shugaban mkranta ya d'aga kai ya dubi dijama yace "a gaban idonki kuma kinajin duk abunda Yayanki yake fad'a a kanki,"
To Idan har kinaso mu shirya dake ki maida hankali a karatu,
idan ba hakanba jikinkin ne zai fad'a mki snn dga k'arshe na d'aura maki mari a k'afa, kamar yanda kikaga nayiwa wad'an can yaran."
Ya nuna mata wasu yara 'yan maza da ya d'aurawa mari a k'afa har da kwad'o yasanya masu."
Zaro ido tayi waje cike da tsoro da tashin hankali tace "Dan Allah malam kayi hak'uri zanyi karatun basai kasanya mun mari a k'afaba."
Murmushi malam yayi yace "kinyi Alk'awari?"
Ta d'aga kai alamar "Eh."
Sann yayi mata tambayoyi game da karatunta anan ya fahimci cewa tana da k'ok'ari sosai rashinjin magana ne kawai yayi mata yawa."
Aji uku ya ajiyeta suka shiga karatu gadan gadan, dijama ta maida hankali sai karatu takeyi."
Khalil yashiga motarsa da Sauri ya tayar da ita, amma abun mmki tak'i yin tafiya."
Dogon tsaki yaja ya kuma kunnata amma taki tayi tafiya, da Sauri ya fito yanufi bayan motar wurin tayoyin motar domin ya fahimci matsalar a nan take."
Abun mamaki mai zai gani gaba d'aya tayoyinshi na baya guda biyu asokesu har sun fara soncewa."
Wani gumi yaji ya fara zubo mashi. Cike da ta kaici, ya rasa ynda zaiyi, gashi babu abunda ya tsana irin ya hau motar haya,
Ganinshi Ajinsa zubewa zaiyi idan a ka Ganshi a cikin motar haya."
Wani dogon tsaki ya kumaja ya sanya hankicif ya shiga goge zufar dake zubo mashi a kan fuskarshi
Ya zagaya ya shiga cikin motar ya zauna ya had'a kanshi da sitiyarin motar yana tunanin mafita,
Yana kuma tunanin Wanda yayi mashi wnn aika aika."
Mahmud tare da abokinshi Auwal sunfito daga wurin yiwa dijama siyayyar kayan makaranta domin ya shirya mata komai har uniform ya d'unka mata batare da Abba ya saniba."
Labarin dijama mahmud yakebawa Auwal, Auwal sai dariya yakeyi,
Mahmud yace "wnn ai ba abun dariya bane illah kawai ataimaka mana da Addu'a domin ina ganin kamar Aljanune suka shigeta,
Auwal ya kuma shek'ewa da dariya yace "Mahmud nida kabani dijamar nan na aureta inasonta a hakan."
Mahmud yanajin hakan yaja bakinshi yyi shuru bai kuma yin mgna."
Karya kwanar da zasuyi Mahmud ya hango motar khalil a bakin makarantarsu fateema ya kuma kallon motar da kyau,
ya hango shi cikin motar ya had'a kai da sitiyari ko motsi bayayi da alamar akwai abunda ke damunshi."
Muhmud yayi saurin nufa wurinshi yayi parking a gefen hanya ya fito ya nufi wurinshi tare da abokin nashi."
Khalil da bai lura dashiba sai ji yayi ana kwankwasa mashi glass din mota,
Idonshi ya d'aga da suka soma komawa launin ja saboda b'acin rai da takaici, ido biyu yyi da Mahmud murmushi ya sakar mashi had'ida sauke ajiyar zuciya ya
Bud'e motar ya yafito
, mahmud ya tsura mashi ido yana kallonshi had'ida tambayarshi meke faruwa?"
Meyasa yayi parking wuri d'aya kuma ya had'a kanshi da sitiyarin mota yana tunani meke damunshi?"
Khalil ya nisa yace "tayar motata CE narasa Wanda yayi mun hakan kuma lfy k'alau na d'auko FATEEMA da wnn yarinyar Wanda tazo daga k'auye na kawosu makaranta, abunda mmki daga shigata mkrantar na fito, na tarar gaba d'aya an farfasa mun tayar mota ta baya,
Ni Abun yana bani mmki."
Murmushi Mahmud yayi ya dubi khalil yace " muguntar me kayiwa dijama kafin kuzo nan?"
Khalil ya ya mutsa fuska yace "Niko meye had'ina da ita da har zanyi mta wani abun?
Kawai dai muna cikin tafiya tasaki baki tana barci na tayar da ita, had'ida zubawa mota ta turare saka makon jin da nayi motata ta canza wani wari naji yana fitowa a ciki kamar tayi mun tusa a ciki, kasan mutumin k'auye yanda yake da k'azanta, kawai shine."
Mahmud yasan za'ayi hakan domin yasan dijama bata barin bashi."
Ya dubi khalil ya yace "mundun baka daina shiga harkar dijama ba saita daza maka fitinar da bazaka mnta da itaba a rayuwarka,
domin kuwa dijama bata barin bashi kuma bata yafiya da zarar kayi mata abu komai girmanka saitabi ta wata hanya ta rama abunda kayi mata,
Dan haka KA daina tunanin Wanda ya aikata maka hakan bakowa bane face dijama ce."
Khalil ya zaro ido waje yana mmki a fusace ya juya zai shiga cikin mkrantar Dan yaci ubanta."
Mahmud yayi saurin rik'oshi ya dawo dashi yace "yi hkri KA kyaleta ai nasamo maganinta gobe gobe nan makarantar barci zan turata kowama ya huta."
Khalil ya kuma har zuk'a yace brother Dan Allah KA barni natafi naci ubnta Dan wlh nafita iya rashin kunya da tujara."
Nafita iya k'auyanci wlh zan kakkarya mata hannu idan na rik'ata."
Mahmud ya kuma rik'eshi yana fad'in " KA natso mana kayi hak'uri dibeka 'yar k'auye duk ta da kula maka lissafi."
Auwal shima ya shiga bashi hak'uri snn ya hk'ura ya bisu suka shiga motar Mahmud suka nufi gida da cewar zasu turo mai gyaran mota tare da direba idan ya gyara sai a dawo mashi da motarshi gida."
Sai da suka fara ajiye Auwal gida snn Mahmud yaja motar suka nufi gida."
Kai tsaye wurin ajiye motocin gida mahmud yayi parking da sauri khalil ya bud"e murfin mota ya fito ranshi a dagule, kai tsaye d'akinshi ya nufa batare da ya bi takan kowa ba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.