Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 12 of 35
Mahmud da khalil sukayi sallama saka shigo, sannan fateema tareda dijama suma suka shigo, suka zauna a gefen momy."
Babu abunda khalili yakeyi da yayi ido biyu da dijama sai ya mutsa fuska kamar Wanda yaga kashi."
Dijama na lura dashi, ta wurga mashi harara had'ida murgud'a mashi baki,
Karaf sai a kan idonshi, zaro ido yayi yana kallonta cike da mmki."
Abba ya katse masa tunani da yafara magana
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*11*
"Abunda yasa na taraku a nan sai Dan in gabatar maku da 'yar uwarku, Ummie ya nuna dijama dake zaune a gefen mmy."
Yanuna khalil "Musamman kai khalil da bakowa kasani ba a cikin dangi, saboda baud'and'en ra'ayinka,
Amma kasan ko wacece dijama, kasan matsayinta a gidan nan,
Baka buk'atar na kuma yi maka wani dogon bayani a kanta."
Ya kuma maida hankalinshi a kan Mahmoud, yace "Mahmoud ga k'anwarka nan nasan kafi kowa farin cikin dawowarta gidan nan baki d'aya."
"Abunda nakeso daku Ku d'auketa kamar yanda kuka d'auki fateema a wurinku, kubata kulawa kamar yanda kuke bawa fateema,
kai inma son samune Kubata kulawa fiye da ynda kuke bawa fateema saboda Ummie marainiyace."
Sai a lokacin mahmoud yayi mgna yace "Abba meyasa ka d'auko mana dijama?"
Abba dijamar da kasani a da ayanxun ta canza hali,
Na rantse da Allah dijama tana iya tayarda gidan nan da unguwar nan gaba d'aya saboda hatsabiban cinta."
Nidai Abba dazakaji sha'warata da anmayar da dijama can Tofa Dan tafi ganewa can, kowa ma sai yahuta."
Dijama tayi saurin d'ago kai ta dubi yaya Mahmoud ta murgud'e mashi maki cike da tsiwa, ta karkace kai tace "lallai ma yaya nan wai a mayardani tofa to sannu."
Khalil yayi saurin nufarta ya sanya hannu ya buge mata baki, dama yana ganin take takenta saitayi rashin kunya."
Dijama tayi saurin rik'e baki, tana fad'in wayyo Allah na ya fasa mun baki"
"Yace k'azama 'yar k'auye, yaya muhmoud d'in kike yiwa rashin kunya?"
Abba ya doka masu tsawa cike da b'acin rai yace "kar in kuma ganin d'aya daga cikinku ya kuma dukanta, bana son hkan,
Na rantse akan Ummie zan iya sab'awa da kowa a cikinku,
domin ganin farin cikinta, na kuma rik'e Amanar d'an uwana."
Ya maida kallonsa zuwa wurin mahmuod yace "Kai Mahmoud yaushe kuka fara 'yar hakan da kaida Ummien taka?"
"To koma dai me takeyi a can k'auye ba ruwanku,
Domin yanxun ta baro k'auye ta shigo birni."
Rayuwarta zata canza, kuma banason tsangwama da hantara a tsakaninku."
"Idan Allah ya kaimu gobe kaje makarantar su fateema, Kasan yanda za'ayi ayo mata takardun shedan ta kammala primary sannan, sai a sanyata a jss1 sai suci gaba da karatunsu tare da fateema."
Kai kuma khalil kaje islamiyarsu fateema ka yanko mata form a d'unka mata uniform sai ta tafara zuwa."
Batare da sun musaba suka amsa da "to Abba."
Ya dubesu yace "Allah yayi maku Albarka."
Suka amsa da Amin."
Sannan ya dawo wurin fateema yace "fateema ga 'yar uwarki nan Ku had'a kanku, kiko ya mata wasu abubuwa wad'anda batasaniba,
Kuma ina so ki d'auketa tamkar 'yar uwarki Asma'u da kika rasa,
Allah ya jikan Asma'u da rahama suka amsa da amin gaba d'ayansu."
Sannan ya basu umurnin kowa ya tashi,
Bayan sunfita ne ya kuma kiran Mahmoud ya dawo ya tsuguna,
Yace "ya kukayi da baban naka Alhaji Atiku?"
Mahmoud ya sunkuyar da kai, yace "zuwan danayi Abuja wurinsa ya karramani sosai, sannan ya turani mukayi jaraba."
Yace kuma "nafad'a maka musanya ido daga nan zuwa wata biyu za'a lik'a sunayen mutanen da sukaci, sannan zai kirani mutafi wurin trening
Abba yayi murnushi yace "karka damu indai Alhaji Atiku ne kasanyawa rayuwarka har kazama soja."
Momy tace "Allah ya taimaka ya tayaka rik'o da gaskya."
Suka "Amsa da Amin."
Sannan yayi masu sallama yatashi ya fita."
Abba ya dubi momy da sai murmushi takeyi d'auke a kan fuskarta,
Yace momyn yara babu abunda zance maki a rayuwa sai dai Addu'a domin kinsamarmun farin ciki a cikin zuri'ata Allah ya barmu tare dake, babban burina shine na faranta maki har k'arshen rayuwarta."
Ya Matso daf da ita, yarik'a hannunta ya shiga murzawa yana kallonta had'ida kashe mata ido d'aya."
Yace "kinsan wani Abu kuwa?"
A kasalance ta dubeshi ta girgiza kai alamar A'a."
"A kullum idan ina tare dake jinakeyi tamkar ina tare da yarinya yar shekara 17,
saboda komai naki na dabanne a koda yaushe yarinya kike komawa."
Ya kuma shege mata a jiki yana shishinar daddad'an k'amshin jikinta,
had'ida sab'ule mata d'ankwalin kanta yana shafa gashin kanta dayasha gyara da mayunka masu Sanya laushin gashi da santsi uwa uba kuma k'amshi."
_Ina ganin hakan nayi saurin fitowa cike da mmkin su Abba da momy ba'a tsofa🤔_
Mahmoud yaje makarantarsu fateema yayi duk abunda Abba ya umurceshi,
ya k'arb'o mata uniform d'inta da littafanta yataho mata dasu,
Ranar Monday zata fara zuwa makaranta."
Da sallamarshi ya shigo cikin babban falon gidan,
ba kowa a cikinsa, sai tausin k'arar TV kawai yakeji yana tashi, gefe d'aya yaji sai dariya akeyi harda buga k'afa.'
Koba'a fad'a masaba yasan dijama ce."
Mmki yashigayi yanufi wurin TV yayi saurin kashewa,
Ya juya ya kalleta, sukayi ido biyu da ita,
ta turo baki tana hararsa k'asa k'asa."
Cikin fushi yace "lallai d'an k'auye yashigo birni yafara wayewa,
Tomu a nan gidan ba'a mana kallo a k'urema volume, anan gidan karatu akeyi a koda yaushe ba zaman shashnciba da rashin kunya, takwala kawai Wanda bata gane karatu."
Ya jefa mata ledar kayan makarantarta yace "gasu nan ki kwana da shiri gobe Monday zaki fara zuwa makaranta, kuma nizan kaiki da kaina, zan shaida masu cewa baki gane komai kwakwalwar kifi ce dake, kuma da zarar kinyi masu irin rashin kunyar da kikeyi a k'auye, zance suyi fata fata da naman jikinki su jefar dake a bula."
Dama tsohuwa ke tare maki yanxunfa?"
Kallonshi tayi idonta cike da hawaye domin a rayuwarta bbu abunda ta tsana irin yaya Mahmoud ya kirata da takkwala mai kwanyar kifi."
Shima yayi mmkin ganin zubar hawaye a idon dijama anan take lokaci d'aya."
Zata bud'a Baki tayi magana kenan ya matso daf da ita, yace "muddun kika bud'a baki kikayimun rashin kunya saina tattakaki."
Ta fasayin maganar ta sunkuyar da kanta k'asa tana aika mashi da Allah ya isa a zuciyarta.'
Mik'ewa tayi tsaye ta d'auki ledar uniform d'inta, saida ta kwatanci saiti wurin k'afarshi ta
sakar mashi remote d'in TV a babban d'an yatsan k'afa, sai da yayi sarin runtse idonshi yace "washh."
Saboda zafin dayaji wurin namasa."
Ta zuba da gudu ta haiye sama tanufi d'akinsu, taja tayi tsaya a bakin k'ofar d'aki, tana kallonshi tana burgud'a baki tace "kuma bani bace takwala sai dai inkaine."
Kuma tunda kakeyimun gorin karatu saina baka mamaki mugu kawai, dan kana ganin nazo gidanku, to kasani duk abunda kakeyimun a rubuce yake a kaina saina fad'awa tsohuwa."
Ganin ya nufota tayi saurin shigewa d'akin had'ida sanyawa k'ofar key."
Tsaye yayi yakasa tafiya yana kallon babban d'an ya tsanshi da ya somayin ja,
Yana tunanin dijama wato bata daina halintaba kenan lallai akwai aiki a nan gaba."
Yana nan tsaye wuri d'aya saiji yayi andafashi a bayanshi, Khalil yagani yace "brother lfy kayi tsaye a nan?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.