Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 4 of 35
Tace "yayana ina kwana, harda 'dan runsunawarta, kamar ta Allah, kallon rashin sani yayi mata cike da jin haushi yace "waye yayan naki?" Ke wai daga ina?" A ina kika sanni?"
Tace "yi hak'uri dama turoni akayi daga gida akace idan naga mai taxi nakirashi domin, yayana ne zaiyi tafiya xuwa kano kuma bayason zuwa tasha shiga mota saboda baya son jira,
gaba d'aya zai d'auki shatar mota domin ta kaishi har k'ofar gida,
kud'ine gareshi sosai."
Mai taxi yanajin hakan ya kyale abokin fad'an nashi ya maida hankalinshi a wurin dijama, yace 'a wace unguwa gidan naku yake?"
Tanuna masa hanya tace "can gaba kad'an bama da nisa sosai."
Yace "yawwa 'yar Albarka shiga mota mutafi,
Girgiza kai tayi,tace "tsohuwa ta hanani shiga mutar mutane saboda kar'a saceni."
Mai taxi da yake yaji maganar kud'i yace "to kishiga gaba kawai saiki dinga nuna min hanya."
"To tace had'ida shigewa gaba, tana tafiya."
Tana gaba d'an taxi na bayanya biye da ita, duk inda ya gifta mata matafiya sai tarenshi akeyi yana girgiza kai alamar ba aiki yakeyi ba dijama kawai yake biya."
Sunzo kwanar da zata sadasu da gidansu,
yara sunyi tsaye tsaye, a bakin hanya,
tashiga kore yaran da hannu tana fad'in "kugafara nan ga mota nan zata shigo, kujanye daga nan."
Tsofaffin unguwa da samari,
kowa sai kallonta yakeyi yana mmki,
yana kuma kallon mai taxi din dake biyeta da ita,
yana k'ok'arin shigowa kwana."
Tabb!!!
su furta had'ida rik'e baki🤔
Suka ce, yau kuma wannan hatsabibiyar yarinya mai taxi ta janyo mana?"
Ido kowa ya bita dashi saboda ba damar ayi mata magana cibi ya zama k'ari,
Domin duk wanda yayi mgna da zarar d'ansa yafito waje,
Idan ta rik'ashi sai tayi mashi shegen duka tsiya, tace "babanka ne janyo maka, idan ka koma gida kafad'a mashi ya daina sanya min ido."
Wnn dalilin yasa kowane mutum sai dai yasanya mta ido."👀
Da kyar d'an taxi yasamu yashiga kwanar,
saboda rashin kyawon hanyar, a ransa yana danasanin biyo ta da yyi,
amma kuma idan ya tuna da shata 'a ka d'aukeshi sai ya d'anji sanyi yyi murmushi yaji dad'i."
Suna zuwa daf da k'ofar gidansu ta hango yaya mahmud zaune a kan dakali,
Gabanta ne yanke ya fad'i data tuna da shigarda tayi a b'and'a ta iskoshi."
Taja dogon nishi, tace "to shi kuma wancan mugun ko zaman me yakeyi a waje?"
Shima Mahmud d'in zaman da yayi, a nan zaman jiranta ne
har zuwa lokacin da zata dawo daga makaranta,
domin yau babu Wanda ya isa ya hana yaci ubnta."
D'an taxi na zuwa sai ti k'ofar gidan tashiga d'aga masa hannu tana fad'in wait wait ya isa ga gidan nan."
Dan taxi yaja burki ya tsaya had'ida sauke ajiyar zuciya wahalar da yasha wurin shigowa wannan hanyar."
Mahmud na ganin hakan ya cika da mmki da Alajabi ya tashi tsam yashiga gida, yana mmkin dijama ko dai Aljanu sun shegeta ne?"
Tsohuwa tashiga dokawa kira tun a waje,
tsohuwa dake kishingid'e tana gyangyad'i, jin muryar dijama yasa tayi saurin bud'e idonta had'ida kai idonta ga dibon agogo,
Mmki tashigayi ganin lokacin tashinsu daga mkranta baiyi ba."
Kai tsaye ta fad'a kan jikin tsohuwa tana fad'in wash Allah tsohuwa nagaji."
Tsohuwa tace "dijama meya dawo dake gida yanzun, bayan nadiba agogo na ga lokacin tashinku daga mkrsnta baiyi ba."
Ta turo baki idonta ya cika da hawaye tace "wai malam Mudi ne yace ya koreni a mkrantar gaba d'aya,
wai sainazo da mahaifina."
Kuma na rantse da Allah tunda ya koreni, duk nakama d'ansa Salihu sainayi mashi dukan tsiya."
Tsohuwa ta rabka sallalami, tace "ya koreki mekikayi mashi?"
"Wai saboda kawai nayi latti ."
Tsohuwa zata kuma yin magana taji ana rangad'a orda da mota a waje ba kafkaftawa, duk a rud'a mata kunne."
Sai kuma ga yaro yashigo yana fad'in wai a waje wani mai mota yace yana kiran dijama."
Tayi sauri ta fito da kayan sauri yakeyi."
[28/04, 20:50] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*4*
Tsohuwa ta juya ta dubi Deejama, itama Deejama tsohuwa take kallo."
Tsohuwa tace dijama a ina kika samo mai mota kuma?" Sann Wad'anne kaya ne naji ance kiyi sauri kifito dasu?"
Dijama ta turo baki cikin shagwab'a tace "yaya Mahmud ne nasamowa mota, domin ya kwashi kayansa yayi tafiyarshi garinsu, saboda nagaji da zaman da yakeyi a gidan nan kullum sai ya zalunceni,
Ko kuma ya dokeni."
Tsohuwa tayi tagumi🤔 tace "dijama waye yasanyaki ki taro motar mutane, shin kinada labarin cewa direbobi wasunsu basu da mutunci?"
Ai kuwa bata rufe bakiba taji ankuma danna wata irin orda da k'arfi,
had'ida dukan k'ofar gidan iya k'arfinsa,
sai da tsohuwa da dijama suka razana."
Da sauri tsohuwa ta mik'e tsaye ta janyo mayafinta had'ida Sanya talkaminta, ta dubi dijama tace "karki kuskura kifito, kibari nafara tafiya na bashi hak'uri, har musamu yayi tafiyarshi,
amma dai yau dijama kin janyo mana fitina da bala'i 'yan taxi."
Duk abunda akeyi mahmud yana d'akinshi yanaji bai fitoba, jira yakeyi a k'are da d'an taxi, ya rik'ata yaci ubnta, la'ada waje."
Tsohuwa tafita waje ta tarar da mutane sunyi cincirindo manya da yara, kowa sai fad'in Albarkacin bakinsa yakeyi a kan dijama, suna fad'in indai dijama ce har abunda yafi wannan zata iya aikatawa."
D'an taxi na ganin tsohuwa ta fito, yabita da kallo ya nufo wurinta, yana fad'in "tsohuwa fito min da yarinyar gidanki,
yau na rantse da Allah tunda iskancinta ya kawo kaina, to ta kai k'arshen rashin kunya, domin ni a tasha nake kwana."
yau zanyi mgnin rashin kunyar da takeyiwa mutanen garin."
yanxun nan a bakin mutanen unguwa, nkejin labarinta tsaf, to tunda rashin kunyarki takawo gareni tazo k'ashe."
Tsohuwa tashiga bashi hak'uri. Tana masifa da mutanen unguwa tana fad'in "dama tasani an dad'e da tsanar dijama a garin nan to ta Allah batasu ba, kuma bazasu iya komai da dijama ba."
D'an taxi shima sai ruwan masifa yakeyi yana dukan mota yana fad'in bazai bar unguwar nan ba sai yayiwa dijama shegen dukan tsiya,
ko kuma a biyashi kud'in mansa da ya k'one wurin shigowa wannan unguwar."
Mahmud dake d'akinshi zaune yanajin duk abunda kefaruwa ganin fad'an ba mai k'arewa bane, yasashi fitowa, yanufi cikin gida kai tsaye d'akin tsohowa ya shiga ya tarar da dijama zaune a kan kujera abincinta kawai takeci, hnkalinta kwance."
Ganin Mahmud da tayi yashigo ya sanyata sakin kwanon abincin had'ida zaro ido waje cike da tsoro,
Tun kafin yakai wurinta tashiga matsar hawaye tana fad'in "dan Allah yaya kayi hak'uri bazan sakeba."
Dank'ota yayi yashiga kwad'a mata mari yana dukanta, dama yana da takaicinta,
Dukanta yakeyi ba girma ba arziki, sai ihu takeyi, tana neman tsira,
sannan daga k'arshe ya rik'a hannunta yafito da ita,
Yana jayen da ita yanufi k'ofar gida da ita, kai tsaye d'an taxi ya mik'awa ita yace "gata kaci ubnta, idan da hali dan Allah katafi da ita, domin ko mu kanmu ta addabemu ta zamar mana fitina."
D'an taxi ya rik'e hannun dijama yana Neman ya turata a mota,
Dijama ta kurma ihu tana fad'in nashiga uku tsohuwa kina gani d'an yankan kai zai tafi dani?'
Tsohuwa tayo kansa tana masifa ta rik'e hannun dijama tace "na rantse da Allah ba inda zakaje min da yarinya."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.