Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 35 of 35

Shima cike da murna ya kuma k'ank'ameta yana mata oyoyo suna dariya,
Tajuyo ta kalli mommy tace hy mommy snnu da gida."

Kallo d'aya mommy tayi mata ta kauda kanta, domin ta tsani rayuwar da 'yar tata take gudanarwa Dan hakan take cewa bata sonta daddy ne kawai yake sonta."

Mahmud na ganin hakan, yayi Allah wadai da rayuwar da suke gudanarwa ya kuma jin tsanarta da ta mahaifinta ya mere baki had'ida Jan dogon tsaki ya bar wurin."

Wuri yasamu nesa dasu ya zauna amma duk abunda ake gudanarwa yana gani."
Zaune yake yana latsar wayar hannunsa pix d'in dijama yake kallo wad'anda yayi ta d'aukarta tana sanye da uniform a lokacin da ya je makarantarsu, kallo yakeyi yana murmushi har ya mnta da b'acin rain yusra."

Sallama yaji anyi masa a gefensa d'aga kai da zaiyi wazai gani fareeda ce matar sulaiman janye da yaronsu."

Cikin fara'a da sakin fuska ya suka gaisa har da d'an zolayarta yyi, yana fad'in bata iya kwana biyu idan bata sanya sulaiman a idoba."

Tana dariya tace "eye naji Dan Allah jeka ka kiramun shi."

Shima dariyar yakeyi yace bara na taimaka mki nkira mki shi."

Ya mik'e tsaye ya nufi inda sulaiman yake a can kusa da Alhaji Atiku ya take masa baya hannunsa rik'e da bindiga saboda tsaro."

Sulaiman mutum ne Wanda baya wasa da aikinsa a cewarsa aikinsa shine gatansa shine uwarsa shine ubansa marayane gaba da baya, a hannun k'anin mahaifinsa ya tashi Wanda shima talaka ne abincin da zasuci wuya yake masu."
Kuma a hakan ya aurawa sulaiman 'yarsa fareeda Wanda suka tashi cike da soyayyar junansu."

Da taimakon Allah kamar da wasa aka fitar da form d'in soja fareeda ta sayar da kayan d'akinta tabawa mahaifinta ya sayawa sulaiman form d'in,
Cikin ikon Allah sunansa ya fito, wnda gashi a yanzun ya fara wadata a aikin soja, domin ya sayawa k'anin mahaifinsa k'aton gida ya kuma bud'a masa babban shago na sayar da atamfofi."

Kai tsaye mahmud ya tunkari wurin inda akeyin liyafar domin kiran sulaima, yusra tana ganinsa takar masa murmushi tana Neman ta bar wurin tazo wurinsa,
Alhaji Atiku na ganin hakan yayi saurin rik'o hannunta ya dawo da ita a inda take yana mata magana k'asa k'asa Wanda su kad'ai sukasan abunda suke cewa."

Mahmud bai damu dasuba kai tsaye wurin sulaiman ya nufa yashiga yimasa magana cikin harshin turanci cewa fareeda tazo gata can tana jiransa."

Jin hakan sai da yasaki murmushi jin dad'i yacewa Mahmud ya kaita masaukinsu da ke nan cikin gidan can layin sojoji, ya ajiyeta,
Had'ida kawo mata ruwa da abinci tasha kafin yazo."

Murmushi Mahmud kawai yyi ya juya ya tafi,
Idon yusra akansa tanajin wata kalar wutar k'aunasa tana ruruwa a zuciyarta domin mahmud jarumi ne daga ganinsa zaiyi jarumta wurin tafiyar da macce a kan gado."

Tunshigowar fareeda wurin idon Alhaji Atiku ya sauka a kanta, yana ganinta yaji gaba d'aya hanlinsa ya tashi so yakeyi kawai yajishi ya kad'aice da ita."

Mahmud na tafiya ya kalli sulaiman ya masa nuni da hannu a lamar yaje wurin matarsa ya kuma zaro kud'i cikin aljihunsa dubu ashirin ya mik'a masa yace kasaya mata kayan motsa baki."

Cike da murna sulaiman ya runsuna ya karb'a yana godiya, yatafi wurin fareeda."

Da isarsa mahmud yana fitowa daga d'akin,
Cikin murna sulaiman ya tareshi yana dariya yana fad'a masa Alherin da Alhaji Atiku yayi masa."

Gaban mahmud ya fad'i ya zaro ido yace "ina fatan baiga shigowar fareeda ba?'

Sulaiman yasaki dariya yace "maiya faru idan har ya ganta?"
Mahmud yace "no bakomai tambaya ce kawai nayi, yayi wucewarsa, yana tunanin tambas Alhaji Atiku fareeda yagani tunda har yabawa sulaiman kyautar kud'i, Dama hakan yakeyi da zarar ya kyallara ido yaga matar yaronsa in dai har ta kwanta masa zai dinga yiwa yaron nasa Alheri na Jan hankali."

*******************

Bayan an watse daga wurin liyafar kowa yakoma wurin aikinsa,
Alhaji Atiku da shalale sai zuba mashi shagwab'a takeyi akan wutar son mahmud dake ruruwa a zuciyarta."

Ransa ya b'aci ganin ynda shalele take zubar da hawayenta akan wani d'a namiji kuma yaronsa, Wanda yake da iko dashi har da mahaifinsa."

Janyota yayi a jikinsa ya shiga share mata hawayen da ke zuba a fuskarta yace "daga yau kukanki ya k'are indai akan mahmud ne."

Wayarsa ya d'auka yashiga kiran number Alhaji Hassan mahaifin mahmud."

Abba yana ganin wayar Alhaji Atiku tunkafin ya d'auka sai da yasaki dariya snn ya daga wayar had'ida sallama,
Alhaji Atiku ya amsa masa yana mai sakin fara'a a fuskarsa."

Bayan sun kammala gaisuwar ne Alhaji Atiku yake shaida masa gobe yyi sauri yazo garin Abuja akwai meeting da zasuyi game da harkokin siyasa."

To Abba yace yana mai d'auke da fara'a da jin dad'i a fuskarsa, snn sukayi sallama ko wanne ya kashe wayarsa."

Ya juya ya kalli yusra yasaki dariya mai sauti yace "nayi mki Alk'awarin bazaki tab'a Neman wani Abu kirasaba, ki sanyawa rayuwarki a gobe za'a tsayar da ranar aurenki da Mahmud ko yaso ko baya so wnn matsalarsa ce."

Washe gari bayan Abba ya sauka garin Abuja sunshiga meeting da manya yan siyasa, anan take da San hannun Alhaji Atiku aka tsayar da Abba a matsayin d'an takarar gwamna. Kasan cewar Alhaji Atiku shikeda jama'a dan haka ko wanne d'an takara yakeyi masa biyayya."

Sauran mutunen wurin sun Amince da zab'en Alhaji Atiku anan aka umurce Abba da ya biya kud'in k'ungiya naira milyan talatin."

Abba yayi shuru domin baya da miliyan talatin, ganin shurun da yayi yasa Alhaji Atiku ya fahimce cewa baya dasu, yasaki murmushi a ransa domin hakan yakeso ya gani."

Anan take Alhaji Atiku ya cika cak d'in kud'in ya bayar."

Zaro ido Abba YAYi cike da mmki zaiyi magana Alhaji Atiku ya dakatar dashi alamar yayi shuru idan aka tashi akwai maganar da zasuyi."

Bayan kowa ya watse daga meeting d'in akabar Alhaki Atiku da Abba a office d'in Abba sai godiya yake zuba masa wanda har yarasa abunda zai fad'a."

Alhaji Atiku ya dafa kafad'arsa yace dainayi mun godiya hakan ta isheni, kasani duk abinda nayi maka ban fad'i ba saboda kai abokinane kuma aminina na gaskya. Komai nawa ina iya mallaka maka shi a kyauta"

Wnn dalilin yasa saboda mu kuma dank'on zumunci mu ya d'ore har d'iya da jikoki na yanke shawarar mu had'a 'ya'yanmu Aure mahmud da yusra."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.