Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 3 of 35

"Idan kika kuskura aka kuma sake kawo k'ararki a gidan nan saina farfasa maki baki kinyarda."
Tayi saurin d'aga kanta alamar "eh." Idanta na zubar da hawaye."

Ganin fitsarin dake d'iga a zanenta yasa yayi saurin sakinta yaja da baya da sauri ya d'auko bulala yanufota yace "koki goge fitsarin nan ko yanzun na lahira yafiki jin dad'i."

Da Sauri ta mik'e tsaye, saiga takarda ta fad'o a zanenta, ya doka mata tsawa yace "ke zonan takardar meye?"

zaro ido tayi waje takai durk'ushe tana matsar hawaye tana fad'in dan Allah yaya kayi hak"uri bazan sakeba."

Tsawa ya Doka mata yace "ba kuka nace kiyi ba tambayarki nayi."

Cikin rawar murya tace "Anty bushira ce antyn suwaiba k'awata tace nakawo maka."

Ya wurga mata harara yace "bud'e karanta abunda ke ciki,
Da sauri ta bud'e takardar tashiga karanta masa, jin kalaman soyayya ne alamar tana sonshi, yayi saurin doka mata tsawa yace "rufe min bakinki kiyi min shuru,
Bari nafaracin k'aniyarki ke 'yar aiken kamun naje ga Wanda ta aikoki."
Ke fitsararriya marar kunya ke ake aikowa da takarda kikawo min?"
Tashi ki kama kunnanki."

Tana hawaye tana fad'in "Dan Allah yaya kayi hak'uri bazan sakeba."

Yasin sai kin kama kunnenki, yayo kanta da bulala a hannunshi,
Tana ganin hakan tayi saurin mik'ewa tsaye takama kunnenta sai kuka takeyi tana bashi hak'uri."

Abincinsa ya jawo ya fara ci, yana kammalawa ya haye katifarshi yajawo jarida ya Shiga karantawa, ganin ta wahala sosai ya dubeta yace "tashi kiwuce kiba mutane wuri."

Tayi kuka idanunta sunyi jajir har sunfara kumbura, ya dubeta yace "ko gobe idan wata ta kuma aikoki da takarda da sunan kikawo min kika karb'a abunda zanyi mki sai yafi wannan, sannan idan kika kuma yimun Allah ya isa saina karye mki k'afa d'aya da hannu d'aya."
Wuce kibani wuri kinyi tsaye kin kafeni da ido kina kallona saikace Aljanah."

Sum sum tafita tana kuka, a bakin k'ofar d'akinshi ta tsaya tace anfad'a d'in "Allah ya isa ban yafeba,
Lokacin da kake zuwa k'ofar gidansu zance na sani ne?" Dan kawai ta aikoni da takarda saika sanyani kamun kunne saboda mugunta,
to banyafeba wuta balbal kuma sai dai idan Kaine Aljanin baniba."

Ganinshi tayi ya nufota ta zuba a guje tayi cikin gida, karo taci da Kaka zaune a tsakar gida, yanajinta a zaure tana Allah ya isa, dama yana da takaicinta ya sanya sandar hannunshi yashiga zungurarta da ita, yana fad'in mamuda kikeyiwa Allah ya isa marar kunya.'

Kuka takeyi sosai Wanda yasa tsohuwa tayi saurin fitowa daga d'aki ta ceceta
Tana fad'in yanzun malam saboda Allah akan mamuda kake zungurar dijama da sanda, ai dole jidama tayi masa Allah ya isa saboda baya raga mata, baya tausayinta ko kad'an."

Ta rik'a hannun dijama tace tashi mutafi ko gobe mamuda ya kuma zaluntarki kice masa baki yafeba."
[28/04, 20:50] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)

Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

*3*

Shiri takeyi zataje makarantar boko. Kasan cewar Wannan shine zangonta na k'arshe da zata k'are pramary school."

Ta kammala shirinta cikin riga da wando blue
ta sanya hijabinta fari, ta d'auko jakarta ta goya a bayanta,
ta dubi tsohuwa dake zaune gefe d'aya tana kallonta."

tace "ni dai tsohuwa nagama shiryawa zantafi."

Tsohuwa tace "to "dijamar tsohuwa Allah ya tsaremin ke kidawo lafiya,
Karki tsaya ko ina, kuma karki kula kowa a kan hanya kiyi tafiyarki dan karkiyi latti."

Tace "to tsohuwa, had'ida fitowa tasanya takalminta ta fita."

Saida ta kai k'ofar gida,
Sannan kuma ta juyo ta dawo a guje saka makon fitsarin da ya matseta,

Da sauri ta sunkuya ta d'auki buta a guje ta fad'a ban d'aki."

Wa zata gani yaya Mahmud ne,
ya juya bayansa yana wanka,
ihu ta kurma. Tana fad'in wayyo Allah k'ato ba wando,
Tafito a guje cikin tashin hankali da tsoro, had'ida sakin butar hannunta tazuba aguje."

Mahmud dajin ihunta yasanyashi Sanin shigowarta band'akin,
ransa yayi matuk'ar b'aci
Yashiga tunanin lallai wannan yarinyar bakad'an ta rainashiba tunda har take iya iskoshi band'aki." Tana kiranshi da k'ato ba wando."

Gudu take falfalawa kamar filfilwa,
bata zame a ko inaba sai makarantarsu,
Da shigarta makarantar ta cikin,
Taci karo da yara yan mkrtar tsugunne alamar latti sukayi,

Da gudu ta wucesu Batabi ta kansuba tayi shigewarta Aji."

Malam sani, mai hukunci yana ganinta ya rufa mata baya yana masifa,
kai tsaye ajinsu ya nufa,
ya tarar da ita zaune a kan kujerarta,

Kujerar da ba Wanda ya isa ya zauna akanta sai ita,
koda kuwa ranar da bataxo makaranta bane,
idan taji lbrin wani Wanda tsotsayi yasa shi ya zauna a kanta to sai tayi mashi shegen dukan tsiya."

Malam sani yashigo ajin a hasale, yadubeta
yace "ke dijama fito nan waje,
Wato kinyi latti saboda rashin kunya irin taki kika wani wuce mutane kika wuto aji,
Sai kace kinfi kowa to kisani hukuncinki ya k'aru dana sauran d'alibai."

Bata kulashiba sai ma tayi kamar bada ita yakeyiba,
Tsawa ya doka mata "ke dijama wai bada ke nake maganaba,?"

sai a lokacin ta dubeshi had'ida turo baki tana gunguni."

Cike da jin haushinta ya nufeta da bulala a hannunshi, bai tsaya b'ata lokaciba yashiga zuga mata bulalar."

Ihu ta kurma ta doka wani irin tsalle tashige mashi a babban Riga,
kasan Cewar malam sani ma'abucin sanya babban rigane.
Kokawa yashiga yi da ita yana k'ok'arin ya yakwace kansa daga gareta,
amma ina, idan yayi nan gefen ta dawo masa nan gefen, sai ihu takeyi kamar Wanda ake cirewa ido."

Malam sani ya jigata sosai zufa sai karye masa take, duk zufa ta wanke masa fuska,
ga dijama cikin babban rigarshi yakasa cireta, sai jujuwashi takeyi kamar zai fad'i k'asa."

Yashiga fad'in 'fito dijama nafasa dukan naki, kije kiyi zamanki,
amma ina ta cimuimuyeshi tana ihu tana fad'in
"wlh bazan fitoba."

Suna hakan Allah yakawo malam mudi,
Yashiga tmbyar mlm sani abun da kefaruwa?"
ganin ya had'a zufa sai jujuwa shi akeyi, bai samu damar bud'e baki yayi maganaba illah yyi mashi da hannu zuwa cikin rigarshi."

Aikuwa malan mudi yana lek'awa ya hango dijama ta cimuimuyeshi sai ihu takeyi, da kyar aka samu aka b'anb'ari dijama a jikin malam sani, sai nishi yakeyi kamar wanda yayi wasan tseren gudu."

Ai kowa yana samu ancire mashi ita,
bai kuma bi takan kowa ba yafita daga ajin da saurinshi,

.dijama kuma na gefe d'aya tsugunne sai zarar ido takeyi tana turo bki cike da tsiwa,
malam mudi yace "tashi kiwuce kitafi gida na koreki daga nakarantata sai kinzo da mahaifinki."

Da sauri ta mik'e tsaye,
Tana magana k'asa k'asa tana cewa "to sai me?"
Kuma wlh duk nakama salihu sainayi mashi shegen dukan tsiya tunda har ka koreni makaranta."

Salihu babban d'an malm mudi ne Wanda yake duk sa'a nine da dijama, tana kaiwa nan tafita waje tayi tafiyarta."

Malm mudi dake tsaye yaji duk abunda tace yace "to idan kika kamashi karki barshi da rai kikashe kinji
, kaji min hatsabibiyar yarinya."

Tafiya takeyi akan titi duk inda taga mota ajiye
saita lek'a kanta ta glass d'in motar ta hango abunda ke cikin motar sannan ta k'ara gaba."

A can taci Karo da yan taxi su biyu suna rigimar fasinja a tsakaninsu, tsayawa tayi tana kallonsu, sai da ta fahimci a kan abunda suke yiwa fad'a,
sannan ta k'arasa wurinsu ta rik'o rigar d'aya daga cikinsu wadda ya fahimci yafi fitina,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.