Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 2 of 35
Gefe d'aya suka samu suka zauna a kusa da wani mai kifi,
Mai kifin yana ganinsu , Sai da ya kuma dallara fitila ya duba da kyau ya tabbatar da sune,
Ya sauke wani numfashi a ransa yace "Ashe yau zanyi kwantai bazan samu cinikiba. Saboda wad'an nan hatsibiban yaran."
'Dijama ta turo ido had'ida turo baki cikin tsiwa ta dubi mai kifi tace "lafiya meya faru kake haske mana ido da fitila?"
Mai kifi da saida gabanshi ya fad'i dajin maganar dijama, dan ba k'aramin aikinta bane ta bad'e basa kifi da k'asa taja masa asara kuma ba yanda zaiyi. Ya k'ak'aro dariyar dole yace "yi hak'uri 'yar gidan tsohuwa ai bansan kece ba."
Ya d'auko leda yasanya mata kifi. Yace 'yar gidan tsohuwa ga wannan kici,
Ta dubeshi ta ya mutse fuska tace "ya'u kabar kifinka kawai yau bana ra'ayin cin kifin."
Abokananta suna su, amma saboda tsoron da suke mata yasa ko wacce ta had'iya yawunta."
Ya'u mai kifi yana ganin haka yatashi tsam ya d'auki tiren kifinshi ya bar wurin ya canza wurin zama yayi nesa da su sosai."
Dijama bata lura dashiba, hankalinta yatafi wurin kallon wani saurayi da budurwa dasuke hira da alama saurayin bak'one zuwa yayi."
Dariya tayi ta girgiza kai irin yanda ta hangosu saurayin sai wani kakkab'ar jiki yakeyi da hankicif, yana wani ya mutsa fuska wai shi d'an gaye."
Gaba d'aya ta nunawa k'awayenta shi, suka tuntsire da dariya,
Dijama tace "yawwa lantana jeki d'aukomin macijin robar nan naki Wanda yayanki yaje binni ya sawo maki."
Lantana ta zuba da gudu taje gida ta d'auko ta kawowa dijama."
Tace yawwa kuzo kuji abunda zamuyiwa wancan gayen."
Suka had'a kai wuri d'aya abu na basu umurni suna girgiza kai alamar sun fahimta
[28/04, 20:50] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*2*
Dijama ta nuna masu inda zasuje su lab'e,
Sai data tabbatar da sun b'oye, sannan
A hankali ta lallab'a tanufi wurin saurayin da budurwar wad'anda suka samu wuri a gefen dakali suka zauna, suna hira suna dariya,
basu lura da itaba sunyi nisa wurin hirarsu ta masoya, ta lallab'a taje bayansu ta d'ora masu macijin robar Wanda aka sanyawa batur sai wutsil wutsil yakeyi kamar macijin gaske,
ta lallab'o ta baro wurin tayo wurin k'awayenta su lantana da suke lab'e wuri d'aya suna lekenta suna dariya."
Itama b'oyewar tayi tashiga lek'awa domin ganin yanda d'an gaye zaiyi."
Ganin basu lura da macijin a bayansu ba,
yasata fitowa tanufi wurinsu tayi kamar wucewa zatayi, sai da tazo daf dasu ta kurma ihu tana nuna bayansu "wayyo Allah maciji a bayanku."
Yahaya gaye yana waigawa yaci karo da maciji a bayanshi,
ai baisan lokacin da ya b'urka tusaba ya kurma ihu ya zubar da talkamin k'afarshi Ya zuba a guje yana fad'in wayyo Allah maciji jama'a Ku kawo min agaji."
Ladiyo dayake tasan halin dijama bataji tsoroba illah ta mik'e a hasale tanufesu,
Suna ganinta tayo kansu suka zuba a guje suna dariya harda rik'e ciki, suna fad'in wasa mukeyi
macijin roba ne."
Yahaya gaye da saida yayi nisa sosai da wurin sannan ya tsaya yana zarar ido yana maida numfashi sama sama, a can yajiyo sautin dariyarsu dijama suna fad'in wasa mukeyi macijin roba ne."
A hasale shima ya nufesu, cike dajin haushin muzantashi da sukayi a gaban budurwanshi, bugu da k'ari ga gudun da yayi harda tusa yasaki."
Aikuwa ya tunkarosu gadan gadan, dijama na ganin haka ta d'aga murya da k'arfi tace "kowa yayi ta kansa."
Suka zuba da gudu ko wannensu yanemi hanyar tsira."
Juyawar da zatayi ta gudu, taji tayi karo da mutum a dai dai lokacin da yahaya gaye yanufota, aikuwa ta mak'alk'ale mutumin wanda batasan kowaye shiba,
D'aga idon da zatayi sai taga Ashe yaya Mahmud ne."
Mari ya kwad'a mata, ya rik'a hannunta ya mik'awa yahaya gaye yace "gata kaci ubanta,
Domin ko mu kanmu mungaji da ita, mungaji da hali irin nata, kayi mata dukan tsiya ninace."
Yahaya gaye babu abunda yakeyi sai ruwan masifa,
Ladiyo ta matso kusa da ita ta xungure mata kai tace "kinci darajar yayanki da yau sai na lahira yafiki jin dad'i,
Dijama da sai zarar ido takeyi tana kallon fuskar yahaya gaye tanaso tayi dariya amma ba hali."
Mahmud yaja hannunta yana rankwashinta a kai yana mata fad'a, sai da sukazo k'ofar gida ta kwace hannunta da k'arfi tashige gida tana fad'in Allah ya isa mugu kawai."
Da Sauri yabita cikin gidan yana Neman ya rik'ata, aikuwa ta fad'a d'akin tsohuwa da gudu,
tsohuwa na ganinta tayi saurin tashi zaune tace "babu Wanda zaibiyoki sai mamuda domin nasan shi kad'ai ke k'ok'arin yaganki bakya motsi, hakan yayi dai dai da zuwanshi k'ofar d'akin yana huci, tsohuwa tace "karka kuskura ka shigo min d'aki
kaji na fad'a maka."
Yaja yayi tsaye a k'ofar d'aki yana huci,
Saida dijama ta kalli fuskarshi ta tuntsire da dariya harda rik'e ciki, dariya takeyi sosai, sai ta kuma kallonshi ta kuma tuntsirewa da dariya,
Ya kuma hasala, tana ganin ya hasala sosai tace "yaya kasan ko menakeyiwa dariya?"
Ya wurga mata harara had'ida girgiza kai."
Tace "ba komai yake bani dariya ba sai yahaya gaye, yanda yasaki tusa ya zuba a guje."
Shima kanshi gudun da yaga yahaya gaye nayi sai da yabashi dariya kasan Cewar duk abunda sukeyi a kan idonshi,
Dariya taso sub'uce mashi yayi saurin barin wurin, yanufi d'akinshi, yana fad'in idan kingama dariyar saiki kawo min abincina ina jiranki."
Yitayi kamar bata jishiba, tashiga bawa tsohuwa labari suna dariya."
Tsohuwa tace "tashi kije ki d'auki abincin yayanki ki kaimasa yana can yana jiranki."
Ta turo baki tace "ni tsohuwa bazanjeba saboda duka na zaiyi."
Tsohuwa tace "baxai dokeki ba aina riga nayi mashi magana, nace karya dakeki kuma kinsan mamuda yanada jin maganar mutane, Wurin nan yana burgeni."
Sannan ta tashi tana turo bki tanufi kicin ta d'auki abincin shi tanufi d'akinshi,
Kai tsaye tashiga d'akin batare da tayi sallama ba,
ta tarar dashi zaune a kan katifarshi dagashi sai best da gajeran wando, jikinshi ko ta ina gashi gashine yayi kwance akan kyakkyawar fatar jikinkinshi fara fes.
hankalinta ya tashi jikinta yasoma rawa aduniya bata tab'a ganin namiji a hakanba,
Tsawa ya doka mata wadda tasanyata tadawo natsuwarta yace "ubnwaye yabaki izinin kishigo min d'aki batare da kinyi sallama ba?"
Maxa kikoma kiyi sallama sannan ki kuma shigowa."
Da Sauri ta juya ta koma jikinta na rawa."
Yana ganin fitarta yayi saurin mik'ewa tsaye ya d'auko jallabiyarshi ya sanya."
Sallama tayi sannan ya amsa mata had'ida bata umurnin shigowa, sannan ta shigo,
Kallon yabita dashi yana harararta domin cike yake da jin haushinta, yanuna mata wni tebur yace "wuce ki ajiye a can."
Kizo inaso zanyi magana dake, kuma kika kuskura kika gudu ko kika yimin ihu saina k'arye maki hannu d'aya idan na rik'aki."
Sum sum ta wuce ta ajiye harda wani sunkuyar dakai kamar ta Allah, tazo kusa dashi ta durk'usa had'ida sunkuyar da kanta k'asa."
Ya Matso daf da ita ya kama kunnenta ya murd'a sosai saida tasaki fitsari saboda azaba,
Yace "maimaita abunda kikace d'azun.
Ni kikeyiwa Allah ya isa baki yafeba?"
Rantse rantse tashigayi ita batayi Allah ya isaba"don Allah kayi hakuri karka ciremin kunne, banyi maka Allah ya isaba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.