Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 20 of 35

Munshiga damuwa mai tsanani da nida mahaifiyarta,
Amma ba yarda zamuyi sai dai muka tashi tsaye da yimata addu'a, Allah ya fito mata da Wanda takeso ya aureta,
Abun mmki sai gashi abun yazo gidan sauk'i kaine Wanda yusra tagani taji tana so.

Alhaji Atiku ya taso daga Inda yake zaune yaxo daf da mahmud ya zauna,
Wanda yayi mutuwar tsaye, saboda mmki, da Al'ajabi,
ko a shirin film bai tab'a ganin rayuwa irin ta wnn gidan ba mai shinfid"e da rashin tarbiya.

Ya dafa kafad'arshi yce "mahmud bazan yi maka doleba, amma nasan bazakak'i 'yataba domin nasan 'yata Yusra ta tara duk wani Abu da d'a namiji yakeso ya samu a jikin macce,
Yusra cikakkiyar macce lafiyayya Wanda bata illah ko ta ina."

Kaje kayi shawara kuma Ku fahimci junanku Allah yayi maka Albarka, tashi kaje ka huta ka kwana da shirin gobe fitar asuba zakuyi."

Mahmud bai samu bakin yin maganaba saboda gaskiyar tayi mashi yawa, hakan ya tashi jiki ba kwari ya fito, ya nufi masaukinshi."

Jiki ba kwari ya shiga d'akinsa Wanda aka ware mashi,
shi kad'ai Wanda yake d'auke da katafaren gado da duk wani abun more rayuwa."

Ajiyar zuciya yasaki ya'ajiye akwatin kayanshi gefe d'aya, ya fad'i zaune a kan gadon yana tunanin, "Alhaji Atiku dake fad'a mashi wai 'yarshi a duniya babu abunda ta rasa."
Kuma ta cika macce ta ko ina, to ya akayi yasan da hakan?"

Babu abunda ta nema ta rasa Wato harda shi kenan yana nufin harta sameshi,
Hmmm lallai kuwa zai nunawa Alhaji Atiku ba komai ake nema a gidan duniyar nan a sameshi ba."

Zai nunawa yusra cewa ba komai take iya samuba a duniya, musamman ni kaina da kwatata bata cikin tsarin matan da nakeso, Asalima koda nayi ido biyu da ita bntab'ajin na tsani wani mutum ba kamar yanda naji na tsaneta."

Mik'ewa yayi jiki ba kwari ya cire kayan jikinshi yafad'a toilet domin yayi wanka yayi sallah la'asar ko zaiji dad'in jikinshi."

Fitowa yayi sanye da jallabiya ya shinfid'a abar sallah ya yatayar sallah."

Bayan ya kammala sallar ne yaji yana da buk'atar Hutu, yatashi daga kan abar sallar ya haye kan gado ya kwanta.

Yashiga tunani Dijama ta fad'o mashi a rai, murmushi yayi ya kuma mirginawa da ya tuna da rashin jin da takeyi a gida."

Koya zata kasance a boarding school?
yasan dai muddun tayi ba dai dai ba a can dukan tsiya zata sha domin bakarantar kwana ba uwa ba uba dole kayi biyayya ga senior dinka."

Yana kwance ruf da ciki. Sai mutum yaji a gefenshi a kwance yana shafa kyawawan k'afafuwanshi da suka lullub'e da gashin jikinshi,
a kan farar fatarshi mai cike da santsi da laushi."

A razane ya mik'e zaune cike da fargaba da b'acin rai ya kai dubonshi wurin wazai gani *Yusra* ce cikin shiga ta wasu k'ana nun kaya riga da siket Wanda iya kacinsu a kan cinyarta rigar kuma mai kamar best duk gaba d'aya Rabin k'irjinta a waje yake." Kanta ba d'an kwali ta zubo gashinta a kafad'a

Kallo d'aya yayi mata ya runtse idonshi had'ida kauda kanshi gefe d'aya,
yayi saurin durowa daga kan gadon cike da b'acin rai."

Ya doka mata tsawa yanuna mata hanyar waje yace "xoki fita d'akin nan shed'aniya kawai."

Zaro ido tayi waje tana mmkin kalamanshi gashi kyakkyawa ajin farko
tana tunanin ya waye Ashe kansa a cikin kwali yake." To meye a ciki Dan tazo d'akinshi ta tab'a jikinshi?"

Cikin rausaya da jan hankali ta nufeshi da nufin kai mashi runguma, yayi saurin zaro ido waje had'ida ja da baya, da sauri
Ya d'aga hannu ya kai mata mata mari a fuska har sau biyu,

Yana huci yana fad'in karki kuskura kice zaki had'a jiki na da naki
Domin ni ko a mafarki bana Fatan Allah ya nuna mun wnn nakasanshin jikin naki mai d'auke da najasa."
Kifita a d'akin nan nace karna tattakaki."

Murmushi tasaki mai cike da takaici tana shafar gefen fuskarta a inda ya mareta duk ga shatin ya tsun hannunshi Nan ya kwanta a gefen fuskarta

Tunda Allah yasa a ka haifeta har ta girma babu wnda ya tab'a yimata fad'a bare tsawa bare har a xo ga dukanta,

Amma gashi abun mmki yau itace wani d'a namiji ke d'aga hannu ya mareta har sau biyu."

A maimakon taji zafin Marin, saima jitayi sonshi da k'aunarshi ya kuma lumkuwa a cikin zuciyarta."

Still idonta a kanshi tana mashi kallon sha'awa.
Tana shafar kunci, murmushi tasaki tace "ina sonka Mahmud,
kuma kasani zan iya jure komai akanka."

Ya kuma kallonta a hasale yace " ni kuma banasonki, ke barima kiji bantab'a jin na tsane wani Abu a rayuwata ba kamar yanda nakiji natsaneki."

Kalamanshi sunyi mata zafi sosai, tasaki dariya mai Sauti tace "kasanyawa zuciyarka sai na aureka domin bantab'a Neman Abu na rasaba a rayuwata, dan haka dole ka soni kuma ka aureni tunda kana k'ark'ashin mahaifina,
Kama d'auka daga yau na zama matarka."

Tana kaiwa nan ta fito idonta yana xubar da hawaye."

Kai tsaye palon daddynta ta nufa, tana zuwa kai tsaye ta fad'a kan jikinshi ta fashe da kuka mai sauti,

Abunda daddy bai tab'a ganiba a idon 'yatshi,

tace daddy ina sonshi, katai makamun ka aura munshi."
Wlh Mundun narasa Mahmud xan iya rasa rayuwata."

Cikin razana ya janyota ya rungumeta yace daina kuka shalele bazaki mutuba a kan wani,
"indai INA da rai da lafiya INA numfinshi a doron k'asa baxaki tab'a Neman wani abun kirasaba, shalele daina kuka ki d'auka har kin aure mahmud,
Har Mahmud ya zama mallakinki."

Dariya tasaki tace "Ngd daddy nah."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅

Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)

*18*

Mahmud yana komawa gida dama ya shirya kayanshi yau zai wuce Abuja zasu fara trening."

A kwati kayanshi ya d'auka tare da duk wani Abun da yake buk'ata yafito,
Abba yayi mashi rakiya tareda Sanya mashi Albarka yana kuma jaddamashi akan yayiwa Alhaji Atiku biyayya ya d'aukeshi tambakar mahaifinshi."

Mahmud yayi murmushi yace "insha Allah Abba bazaka samu wata Matsala daga gareniba."

Suka had'a baki tare da momy sukace Allah yayi maka Albarka yabaka sa'a aduk abunda kasanyawa gaba."

Yaji dad'in Addu'ar tasu,
ya runsuna k'asa yace "Amin Abba da Momy ngd, Allah ya barmun ku, naci gaba da kyautata maku har k'arshen rayuwata,
idan
khalil ya dawo mmy kice masa na wuce."

Yana fad'in haka yabud'e mota yashiga yatayar suna d'aga mashi hannu har ya yafita get d'in gidan ya d'auki hanyar Abuja."

****************
Bayan antashi break fast Kowa ya fito daga aji yanufi wurin cin abinci dijama kuma taja wuri d'aya gefe d'aya ta rakub'e babu abunda takeyi sai ruwan hawaye."

Tana tunanin tsohuwa, tana nan zaune tana tunani tana hawaye batasan kowa ya watseba ya ba kowa a wajen duk ankoma class."

Bata ankaraba sai saukar bulala taji a bayanta a firgice ta zabura ta mik'e tsaye cike da tashin hankali da tsoro tana kallon wanda ya daketa."

prefet ce tsaye a gabanta tana fad'in ubanme kikeyi a nan kowa ya koma aji ya barki, sai magana ake maki kin kyale mutane."

Zuciyar dijama takawo mata a wuya, dame zataji da kad'aici ko da mugunta,
Prefet taga dijama bata da niyar motsawa daga inda take ta kuma d'aga bulala cike da jin haushi ta kuma doka mata a tsakiyar baya." Sai da dijama ta gantsare saboda axabar zafi, tunda Allah yasa aka haifeta ba'a tab'a yimata irin wnn dukanba."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.