Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 13 of 35
Su momyn basu dawobane?"
Mahmoud yace "fita sukayi ne?
"Khalil yace "sunje gidan gaisuwa tare da Abba."
Ya mik'awa Mahmoud wani takarda Mahmoud ya karb'a yana dubawa yana cewa "takardar meye?"
Khalil ya yamutsa fuska yace form d'in islamiyar wnn bagidajiyar nan ne, wadda Abba yasanyani karb'owa, nagama cika komai sunanta ne kawai bansaniba,
Wlh bnsan abunda yasa Abba ya dawo da ita gidan nan ba, da zarar munyi ido biyu da ita jinakeyi kamar zanyi amai."
Mahmoud ya dubeshi yace "khalil 'yar uwarka face, gakya ya kamata ka canza hali Kuma ka canza rayuwa, kadaina ganin 'yan matan Jami"a kyawawa wayayi suna rud'arka har kake kyamatar jininka. To kasani asalinka k'auye a can Abbamu ya tashi a can ya girma har gobe mahaifansa suna k'auye."
Wani saurin ja da baya yayi yana duba bayansa, ganin baiga kowa a wurinba yace "haba brother bazaka gane bane, nagodewa Allah da bakowa a kusa dani lokacinda kake fad'in hakan daka sanyani naji kunya."
Ido Mahmoud ya tsora mashi yana mmkinsa domin yanda ya d'aukeshi sai yaga ya wuce nan."
Takarda ya mik'a mashi yace "ynda bakasan sunantaba nima bnsan sunantaba, kabari idan Abba ya dawo shida ya sanyaka saika tmbayeshi sunanta kagani sai ya fad'a maka."
Yana kawowa nan yayi tafiyarshi ya barshi nan tsaye zuciyarshi cike da mmkin khalil."
Khalil yabi mahmoud da kallo yace "ya za'ayi na tambayi Abba sunanta, nasan yanda yakejinta a gidan nan yana iya kafsamin a gabanta
Zan dai jira har lokacin da fateema dawo daga mkranta saina tambayeta."
Yajuya yanufi d'akinshi yana mamakin mohmuod ganin yanda shima yakeji da wann bagidajiyar a gidan nan☹
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*13*
Da sauri shugaban mkranta ya nufo ajin har da tuntub'e. Yakeyi domin lbrin da ya isar mashi anjiwa 'yar ciyaman da 'yar kassila ciwo."
Ganin saurin da yakeyi yasa sauran malamai suka fahimci a akwai abunda ke faruwa, suka rufo mashi baya."
Ganin jinin dake zuba a bakukansu ya d'agawa malamai hankali. Anan take aka Shiga basu taimakon gaggawa."
Shugaban makaranta ya d'aga waya ya kira ciyaman da kassila yake shaida masu abunda ke faruwa."
Ko wannensu cikin tashin hankali suka bugawa jami'an tsaro waya, anan take mota biyu ta 'yan sanda kamar had'in baki, motar ciyaman da motar kassila."
Suka shigo cikin mkrantar sai jiniya kukeji kamar za'a tashi makarantar, 'yan sandan kowanensu da zungureriyar bindigarshi a hannunshi."
Sai tambaya sukeyi ina yarinyar da taji masu ciwo, a wuce da ita atafi da ita a hukuntata."
Dijama dake tsugune gefe d'aya sai Zarar ido takeyi ta karkace kai duk Wanda ke magana tana binshi da kallon tana kallon bakinshi."
Turanci kawai takeji yana tashi Wanda bata san abunda suke cewaba kallonsu kawai takeyi."
Can taga shugaban makaranta ya nunata da yatsa yana fad'i da Hausa yana cewa "kunganta can itace, yau yau d'in nan da zuwanta makarantar nan amma har ta fara dazamun bala'i."
Shekarata goma sha d'aya da bud'a makarantar nan hakan bata tab'a faruwa daniba sai zuwan wann fiti nan niyar yarinya."
Tsawa aka dokawa dijama Wanda yasa tayi saurin mik'ewa tsaye saboda ganin zungureriyar bindigar dake hannun d'an sandar."
Tashiga ja da baya tana "fad'in Dan Allah kuyi hak'uri karku harbeni sune suka fara tsokanata."
Fateema kuma babu abunda takeyi sai aikin kuka, Wanda a cikin mutanen wurin bbu Wanda ya lura da ita tana gefe d'aya a tsaye."
Kuma doka mata tsawa d'an sandar yayi, yace "ba kasheki zamuyiba tafiya zamuyi dake sai munji ko waye ubanki a garin nan snn mu d'aukar mki hukunci."
Haka aka sanya k'eyar dijama a gaba tare da shugaban mkranta aka sanyasu a mota aka tafi dasu."
Dijama sai Zarar ido takeyi wuk'i wuk'i a bayan mota, shugaban makaranta da juya ya kalleta sunyi ido biyu da ita sai ya wurga mata harara."
A zuciyarshi yana da yasani karb'arta da yayi a matsayin d'aliba."
Fateema na ganin antafi da dijama, ta kuma fashewa da kuka,
tayiwa wani malami magani tace "dan Allah uncle kabani Aron wayarka zankira Abba na na fad'a mashi abunda ke faruwa."
Zaro ido yyi cike da mmki yace "dama kinsanta ne?"
Ta d'aga kai alamar "eh tace yayata ce uwarmu d'aya ubanmu d'aya."
Uncle ya xaro ido waje yace "kina nufin 'yar Alhaji Hassan Adam CE?"
To ya akayi bansanta ba a cikin gidanku?"
Cike dajin haushin tambayarshi fateema ta turo baki tace "bazaka Santaba saboda ba'a garin nan takeba,
dan Allah uncle kabani aron wayar mana."
Yace "Ayyah fateema kiyi hak'uri banada waya a hannuna, amma nasan za'aje da ita ta nuna gidansu."
_kuyi hk'uri d wnn pls yau sai a hnkli_
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*12*
7:30am. Shiri sukeyi domin zuwa makaranta,
tasanya uniform dinta, wad'anda sukayi mata kyau sunfito mata da fuskarta sak 'yar fillo."
Fuskar nan tata tasha hoda da jambaki,
fateema dake gefenta zaune,
ta dubeta tace "dijama ki goge wnn kwanliyar ta fuskarki tayi yawa sosai idan mukaje Anty tana iya sanya hijabinki fari ta goge mki ita."
Ta murgud'a baki tace "bazan gogeba, a hakan zanje kuma bata isa ta gogemun kwanliya taba."
Fateema zata kuma yin magana tajiyo sautin muryar yaya Mahmoud yana fad'in "wai bazaku fitoba lokaci fa na tafiya, Allah duk kuka kuskura kuka bari na hawo saman nan sai jikinku ya gaya maku."
Da sauri fateema ta d'auki school bag d'inta ta goya. Bata kuma bi takan dijamaba don tasan halin yaya Mahmoud ba sauk'i ne dashi ba."
Dijama da ke k'ok'arin sanya sendel a k'afarta tana turo baki cikin magana k'asa k'asa tace "to idan ka hawo karka barmu da rai ka kashemu."
Ido fateema ta zaro waje tace "yayan kike cewa hakan lallai dijama bakisan halin yaya Mahmoud bane, tana fad'in hakan tayi saurin bud'e k'ofa ta fita, tabar dijama na sanya takalmi."
Tana gama sanyawa itama ta biyo bayanta, ta fito tana tafiya harda wani rangwad'a takeyi wai ita 'yar boko."
Gaba d'anyansu Suna babban falo zaune suna Brest fast, Abba da shirinsa na zuwa Office khalil shima da shirinsa zuwa makaranta BUK."
Mahmuod a tsaye da key d'in mota a hannunshi yana jiran fitowarsu ya kaisu, yadawo yana da inda zaije, har sun b'ata mashi time."
Fateema ta fara fitowa sann dijama ta biyo bayanta,
Abba na ganinsu cikin uniform yaji dad'i sosai sai murmushi yakeyi a fuskarshi,
Momy itama murmushin takeyi tana fad'in "iye 'yan matana lallai kunyi kyau musamman 'yata ummie."
Mahmoud dake tsaye gefe d'aya yanayi yana kallon agogon gwal dake d'aure a hannunshi."
Khalil ya d'aga kansa yana ya mutsa fuska yana kallon dijama. Da take k'ok'arin k'arb'ar flast d'in break d'insu. Wanda momy ke mik'a masu,
Ido biyu yayi da fuskar dijama datasha kwalliya,
mai zaiyi idan ba dariya ba,
Dariya yakeyi yana nuna fuskarta yana fad'in tab "mutumin k'auye baiyi ba wlh ke wai kwanliyace kikayi hakan ko meye?"
Brother wlh karka bari wnn abar ta shigar maka mota, ai sai kuzama abunda kwatance duk inda kuka gifta."
Cikin zafin rai Abba ya doka mashi tsawa da k'arfi yace "khalil tashi kafita karna na sab'a maka wlh."
Momy Itama tabishi da harara tana fad'in "ni bansan irin rayuwar khalil ba a cikin gidan nan."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.