Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya
Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt
Chapter 28 of 35
*25*
A wann ranar ta d'agawa kowa hankali, mu samman mahaifinta da hankalinshi yyi mummunan tashi. Sai lallashinta yakeyi da ban hak'uri."
Sai da tasamu natsuwa ta tsagaita kukanta snn yashiga tambayarta, "shalele meya faru?" Waya tab'aki?" Meke maki ciwo?" Me kikeso?"
Rinannun idanuwanta ta d'aga sukayi ido biyu da mahaifin nata wnda take kwance a kan jikinsa,
"Daddy zaka bani abunda nakeso kamar yanda ka d'aukar mun Alk'awari?"
"Zan bki shalele duk abunda kike buk'ata."
Hawaye ya kuma ciko idanunta tace.
"Daddy Mahmud nakeso,
Daddy inaso ka aura mun mahmud nan bada jimawaba, daddy Mahmud yaci mutum cina ya wulak'antani cikin bainar jama'a sai dai duk da hakan bnji soyayyar sa ta ragu a zuciyata ba sai ma buri da shauk'in na mallaki namiji irin sa."
Yyi murmushi "haba shalele Dama akan wnn kike b'ata ranki?
Mahmud kinzama matarshi bazan gaji da fad'a maki hakan ba
Ki sa aranki kece matar mahmud,
Mahmud bashida wata mata bayanke ko yanaso ko baya so."
Abunda nakeso dake karki kuma kiran wayarshi, duk ynda kikeji a kan sonshi a ranki ki danne ki sanyawa zuciyarki dangana kibani nan da wata uku kigani a lokacin Mahmud, zai zama mijinki zaki mallakeshi cikin kwanciyar hankali da lumana."
Mik'ewa tayi tana tsalle tare da tsananin murna ganin tasamu abunda takeso, domin da zarar daddy yayi mata Alk'awarin zaiyi mata Abu tabbas ba makawa saiya matashi koda rayuwar wani zata salwanta."
Mahmud zan nuna maka iya karka, ta fad'a tana murmurshi snn ta tashi ta tafad'a d'akinta."
*******************
Allah ka d'ai ya saukeshi garin ibadan lafiya irin yanda yake gudu a mota."
Misalin k'arfe 10pm ya sauka, kai tsaye d'akinsu ya nufa ya Tarar da sulaiman a kwance yana waya da matarsa uwar d'ansa, abin sonsa, sai dariya yakeyi cike da jin dad'i."
Bai lura da Mahmud ba sai ganinshi yayi ya shigo ya fad'a toile."
Da sauri yayi mata sallama ya kashe wayar yashiga zuba ido yana jiran fitowar Mahmud."
Mahmud dake cikin toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi sai sauke ajiyar zuciya yakeyi tare da lumshe idanuwanshi."
Sulaiman yaji shurun yayi yawa ya kwankwasa masa k'ofa,
Sai a lokacin mahmud ya sauke ajiyar zuciya yayi arwala ya fito da jallabiya sanye a jikinsa sai da ya fara gabatar da sallolin da ake binsa snn ya mik'e ya je kusa da sulaiman da ya k'ura mashi ido yana kollonshi ya zauna "
Sulaiman ya kasa hak'ura ya kalleshi cike da kulawa yace "abokina wai meyake faruwa ne?"
Mahmud ya juya ya kalleshi yayi murmushi, anan yashiga fad'a mashi duk abunda ke faruwa."
Sulaiman yace "babu abunda ya kamata muyi shine Addu'a domin bayan tafiyarka oga ya dawo yake tambayata katafi?"
Nafad'a mashi "eh katafi amma ranka baiso tafiyarba. Oga yayi murmushi yace "Allah ya tsareka, Allah yasa baka fad'a tarkon commondent ba, domin ya fiya Son kanshi."
Mahmud yace "komai son Kansa da yakeyi bazai tursasani akan nayi abunda bana so bana k'auna ba
Wlh in har saina aure "yarshi nafison na ajiye aikin sojan da nkeyi,
Dama ni bana ra'ayin aikin soja Abba ne da momy sukeson hakan, kuma na d'auki Alk'awarin duk abunda su keso znyi masu,
zanyi biyyah garesu koda kuwa ni banaso, kai koda daga aikatashi shine silar rasa rayuwata indai akan mahaifana ne naji na gani."
Yana cikin maganar ne wayar hannunshi ta d'auki k'ara yana dibawa yaga shugaban makaranta ne."
Sai da yaja dogon nishi ya kalli sulaiman yace "dijama ta janyo mana wata fitina wata k'ilama ya koreta daga makarantar."
Sulaiman ya saki dariya domin shi har ga Allah labarin dijama dariya yake bashi,
Yace ka d'auki wayar mana meyasa zaka yanke hukunci a kan abunda baka sani ba."
Jiki a sab'ule ya d'aga wayar had'ida yimashi sallama."
Tunkafin shugaban makaranta ya fara magana mahmud yafara da cewa "dan Allah shugaba kayi hak'uri karka koreta na fad'a maka duk lokacin da tayi wani abun abata kashi Wanda zai sanya dole ta shiga hankalinta, idan akwai ma abunda yafi duka ayi mata shi."
Shugaba yyi dariya yace "kwantar da hankalinka Mahmud ai yanda kasan Nana khadija a da yanxun ta wuce nan bbu wani Abu da takeyi a yanzun bayan karatu domin kuwa idan kaji yanda bakinta yake fitarda turanci sai ka rantse da Allah kace ba ita bace."
Abunda yasa nakiraka a dai dai wnn lokacin, kiranka nayi domin na fad'a maka gobe ne akeyi masu hutu Wanda nasan bakusaniba sai kuzo Ku d'auketa da misalin k'arfe 10am
Murmushi mahmud kawai yakeyi a fuskarshi godiya yashiga yiwa shugaba har lokacin ya kashe wayar,
Duk abunda ake fad'a sulaiman ya naji a waya, shima dariya yakeyiwa mahmud jin tunkafin shugaba yafara yin magana mahmud ya rigashi yana bashi hak'uri.'
Saboda anriga da ansan dijama matsalace,
Mahmud yace dijama anyi hankali?
Tab da sake wata k'ila dai kwanto ne tayi masu saboda dijama fitina ce."
Sulaiman yace nidai ina rok'on Alfarma da abani dijama na aureta nayi ta biyu da ita,
Koda dai nayiwa wife d'ina Alk'awarin baxan mata kishiyaba."
Mahmud yace "ai kuwa idan kanasonta na baka amma ka shirya rabuwa da matarka ta girma da arxiki idan ba hakan ba to zakuyi rabuwar rashin arziki,
Dan na rantse maka dijama saita cinnawa gidanka wuta dakai da mtarka da d'anka duk sai kun k'une tana gefe tana kallonku saboda fitina."
Sulaiman ya kuma sakin dariya yace " wnn dijama na matsu na ganta."
Mahmud yace ai ganinta zakayi, a hakan sukaci gaba da firar dijama har bacci ya d'aukesu gaba d'ayansu."
*******************
7:30am Mahmud ya kira Abba yake shaida masa yau ne akeyiwa su dijama Hutu atafi a d'aukota."
" Abba ya kalli momy suka saki murmushi,Abba yace "yi hak'uri Mahmud ynxun shirin da nkeyi kenan da kaina zanje na d'auko maka dijamarka."
Gaban mahmud ya yanke ya fad'i yace "Abba dijamata fa kace?" Tab Allah ya tsaran INA zan iya da fitinar dijama."
Abba yana murmushi yace "kuma fa hakan ne, bari kawai natafi na d'aukota sukayi sallama Mahmud ya kashe wayar,"
Khalil da shigowarsa kenan yaji Abba na waya yasan da Mahmud yakeyi irin ynda yaga yana sakin fuska yana dariya, maganar da taja hankalinsa gareshi itace "bari naje na d'auko maka dijamarka."
Gabansa yaji ya fad'i ransa ya b'aci "wato dijamarsa harma ta zama tasa?"
Yayi k'ok'arin saita Kansa, ya durk'usa k'asa ya gaidasu harda wani sunkuyar da Kansa k'asa,
Suka amsa mashi cike da kulawa."
Yace "Abba kabar shi natafi na d'aukota, Abba yasaki murnushi yace "ai na d'auka makaranta zaka tafi?"
Yace "bama da karatu ynxun sai zuwa 3pm Abba yace "OK to katafi ka d'aukota Allah ya tsare."
Fateema ta fito cikin kwanliyarta ta atamfa Wanda tayi mata kyau sai wani k'amshi humra take fitarwa mai d'aga hankalin lafiyayyan d'a namiji,"
Humra momy ce Wanda itama bata shafata sai idan zata kasance tare da Abba, saboda da zarar ya shak'i k'amshinta hankalinshi zai d'aga yajishi yana son ya kasance da ita."
tashiga d'akinta ta d'auka ta sanya momy bata saniba."
Tana k'arasowa wurin k'amshin humra ya kuma k'ara game pallon."
K'amshin yana dukan hancin khalil gaba d'aya hankalinshi ya yatashi cikin minti biyu idonshi ya rikid'e zuwa launin ja wata irin wutar sha'awa yaji ta taso masa."
A kasalance ya juya ya kalli fateema yace "ubnwaye yabaki wnn turaren da kika sanya?"
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.