Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 21 of 35

Tana zaune a inda take bata da alamar motsawa bare ta tashi daga wurin."

Prefet d'in ta kuma harzuk'a cike da takaici ta d'aga balala zata kuma kai mata a karo na uku, tana wani huci."

Dijama tayi saurin mik'ewa tsaye cikin zafin nama ta rik'e bulalar,
ta duk'a ta d'auki prefet d'in saida ta d'agata sama snn tabugata a k'asa, ta karb'e bulalar hannunta tashiga zuga mata ita."

Ganin duka da bulala b'ata lokacine tayi jifa da bulalar ta haye ruwan cikinta tashiga nusarta."

Ihunda prefet d'in keyi shi yaja hankalin sauran d'alibai da malamai suka firfito. Cikin hanzari suna kallon ikon Allah,
D'alibai sun zagayesu suna kallo,
Duk a tunaninsu Aljanun dijama ne suka tashi, dibo da yanda suka dijama ta haye kanta, nesa ba kusaba prefet tafi dijama girma tsawo da k'iba da komai, duk cikin makarantar bbu wanda d'alibai ke tsoro sai ita saboda girman jikinta gashi kuma muguwa ce bata ragawa nak'asa da ita, malamai su kansu sunsan da hakan,

Amma yanzun abun mmki
gata a k'asa k'aramar yarinya 'yar shekara 14
'yar jss1 ta d'agata Sama ta kayar k'asa ta danne tana duka sai ihu takeyi."

Wnn yarinyar Aljanune suka hau kanta bayin kanta bane, inji malaman dake tsaitsaye sunkasa isa wurin su taimaki prefet. D'in."

Dijama tanajin malamai na fad'in Aljanune ai kuwa ta kuma birkicewa taci gaba da jifgarta, ta mak'e murya kamar ba muryar taba tana fad'in "Dan kinga mun kyaleki, kina dukanta,
bakisan ko mu suwaye bane?"

Can wata malama tayi k'arfin halin tunkararsu da kyar tasamu ta fincike dijama a kan prefet d'in."

Dijama na huci tana harararta tana fad'in "idan kika kuskura kika kuma kulamu sai munyi maki illah a makarantar nan."

Ai kuwa malamai sukayo kan dijama aka shiga bata hak'uri had'ida yi mata Addu'oi."

Shugaban makaranta yana office yana aiki labari ya sameshi, cikin hanzari a ka had'a Assambully kowa ya hallara, A ka d'ora dijama a kan Assambully, sai zarar ido takeyi tana turo bki."

shugaban makaranta yashiga bayani a kanta, yashiga nunata yana fad'in "kuyi taka tsantsan da ita kadda Wanda ya kuma kulata a cikinku, idan tayiwa wani daga cikinku wani abun ya hanzarta zuwa wurina ya kawo mun k'ararta ninasan yanda zanyi mata."

Idan kuka lura da abunda tayiwa 'yar uwarku, ya nuna prefet d'in dake rakub'e wuri d'aya sai zare ido takeyi tana sauke numfashi da sauri, alamar ta daku."

Ya isa kubawa kanku amsar cewa Nana khadija Hassan ba ita kad'ai takeba tana tare da Aljanu,
ko Aljanun manyan Aljanu."

Dan haka abunda nkeso daku shine ku kiyaye abunda na fad'a maku a kanta,

Suka amsa da "to malam."

Snn ya umurci kowa ya watse ya koma aji,
Dijama na shiga aji kowa ya kama kanshi da ita,
Hakan malamin English yashigo suka fara karatu gadan gadan."

Bayan antashi daga makaranta kowa yanufi d'akin barci domin cin abinci suyi wanka ayi sallah, snn akoma karatun marece wasu kuma sutafi islamiya."
Dijama taja tayi tsaye a wuri d'aya domin batasan inda zatajeba."
Anan idonta ya fara cika da hawaye."

Prefet d'in da tafara gani farkon zuwanta Senior Rukayyah ita tagani a gabanta tana mata murmushi ta rik'a hannunta suka nufi d'akinsu inda ta ajiye mata kayanta."

Senior Rukayyah tun lokacinda taga dijama taji tashiga ranta,
Hakan kuma a nan take taji ta kamu da son Mahmud lokaci d'aya, wnn dalilin yasa tad'auki d'amarar taimakawa dijama. A kan karatunta domin ta fahimci burin yayanta kenan tayi karatu."

*****************

Mahmud ya sauka Abuja lfy, Inda yaga karramawa wurin Alhaji Atiku.

Yana zaune cikin katafaren palon gidan Alhaji Atiku commondent anzagayeshi da kayan ciye ciye da abinci kala kala."

Alhaji Atiku a gefenshi nesa dashi yana mashi bayanin yanda zasu fara trening d'in gobe."

Sai jiyaniya sukeji tana tashi a harabar gidan, mahmud baiyi mmkiba dibon da yayi tundaga farkon layin gidan har zuwa cikin gidan
sojojine birjik aka Zuba a wurin."

Yashiga tunanin wata k'ila bak'ine Alhaji Atiku, yayi

Bai gama tunaninsaba aka bud'o k'ofa aka shigo batareda anyi sallama ba."

Ganin murmushi yayi d'auke a kan fuskar Alhaji Atiku, waigawa yayi domin ganin mai yake kallo yake yiwa murmushi."

Wata tsaleliyar budurwa yagani fara fes da ita wanda bazata wuce shekara 23 ba a duniya.

tana da kyaunta ba laifi, ta sanya riga da wando wad'anda suka bayyanar mata da duk ilahirin surar jikinta, ta d'ora wani figigin gyale a kanta Wanda dashi da babu duk d'aya. Fuksarta sanye da bak'in glass hannunta d'aya d'auke da katuwar waya. D'ayan kuma d'auke da jaka.
Gefen hannunta dama da hagu, sojojine ke take mata baya."

Hannu ta d'aga masu tare da ya tsine fuska a kan suyi tafiyarsu,
Saida suka Sare mata snn suka juya suka tafi."

ganinta yayi taje cikin shagwab'a ta haye a kan cinyar Alhaji Atiku."

Mutuwar tsaye Mahmud yayi ya tsura masu ido yana kallon ikon Allah."

Cikin shagwab'a take cewa daddy na gaji dayawa."

Hannu ya sa yana shafa bayanta yana "fad'in Ayyah sannu shalele kitashi kitafi kiyi wanka ki huta momynki na ciki, tayi maki tausa."

Turo bki tayi tace "ni kai nakeso kayimun."

Dariya yasaki mai sauti yace "nida kaina shalele?" To tashi kitafi gani nan zuwa yanzun nan

Yace baki gaida yayankiba gashi nan zaune, ya Nuna mata Mahmud da yasaki baki yana kallonsu."

Taya tsine fuska ta kai dubanta ga mahmud, dan bata lura da akwai wata halitta a wurinba,

Ido biyu sukayi da Mahmud ta tsayar da idonta gareshi ta kasa d'auke idonta a kanshi gaba d'aya kyanshi da haibarshi ya tafi da imaninta."

Mahmud kuma lokaci d'aya yaji ya tsaneta, saboda daga ganinta bata da tarbiya da kamun kai a tare da ita."

Wow ta furta had'ida mik'ewa tsaye tanufi wurin mahmud tasanya hannu zata shafi gefen fuskarshi yayi saurin rik'e mata hannu had'ida had'e fuska yayi jifa da hannunta gefe d'aya saura kad'an ta fad'i k'asa"

Bata damu da abunda yyi mataba, illah tazo gabanshi daf da shi ta zauna yanda suna iya jin saukar numfashin junansu tace "kana da kyau wanda baya misaltuwa, ina sonka."

Ta juya ta dubi Alhaji Atiku tace "daddy wnn yana da kyau ina son shi zan aureshi."

Alhaji Atiku yasaki dariya, yace shalele ai yayankine Abu yazo gida kenan, ki sanyawa rayuwarki kinsameshi, harma kin aureshi."

Mahmud yayi saurin d'aga kai sama ya dube Alhaji Atiku cike da mmki."

Shalele tasaki dariyar jin dad'i, tace "nagode daddy na dan haka nake sonka fiye da momy, tana kaiwa nan tafita cike da jin ddi

Tana fita Alhaji Atiku ya maida kallonshi a kan mahmud da murmushi a kan fuskarshi yakira sunanshi.

"Mahmud wnn itace 'yata kwaya d'aya tilo a duniya sunanta *YUSRA*
A duniya babu abunda yusra ta nema ta rasa."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅

Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)

*20*

Tafe take d'auke da robar abnci, a hannunta,
tuwon masara da miyar karkashi, tafito daga danie tafe take tana 'yar wak'arta wadda taji d'alibai nayi."
.
A gefen wasu manyan 'yan mata ta wuce da alama prefet ne
Taji suna fad'in "sai munyi mgnin wann shigiyar yarinyar badai ance Aljanu garetaba,

Idan dare yayi musameta a. D'akin da take,
ai a d'akin senior Rukayyah take, musameta a can idan tayi barci muci ubnta."
Suka sanya dariya harda tab'awa."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.