Trending Hausa Novels

Yar Gidan Tsohuwa Littafi Na Daya

Reading file: YAR GIDAN TSOHOWA.txt

Chapter 27 of 35

Bak'uwar number yagani karon farko dariya yaga anfara sanyawa kamar haka."

_Hhhhhhhh sweetyna kenan na fad'a maka duk abunda nakeso sai na sameshi, kashirya zuwa garin Abuja ynzun nan domin tayani murnar zagayowar ranar haihuwata wanda na shiryashi domin kai, domin inyi tozali da kyakkyawar fuskarka mai cike da Annuri, byee sai kazo_

Cikin bak'in ciki da takaici ya gama karanta massage d'in d'aga kansa da zaiyi yyi ido biyu da ogansu,

Yace "mahmud Hassan sak'o daga _commondent General_ ya mik'a mashi key d'in mota yace ynzun nan yana nemanka garin Abuja."

Idon mahmud suka rikid'e zuwa launin ja, ya d'aga kai ya dubi ogannasu sai da yayi kamar ba xai karb'i key d'in ba,
Tunawa yayi da hud'ubar da Abba yayi mashi, "kayiwa Alhaji Atiku biyya tamkar shi ya haifeka, KA kuma d'auke shi tamkar ni mahaifinka, karka sab'a mashi ko kuma KA b'ata mashi."

Sai da ya runtse idonshi sann ya bud'esu, yasanya hannu ya karb'i key d'in motar a hnnun ogan nasu, snn
Oga yyi tafiyarshi."
Mahmud ya mik'e tsaye had'ida kallon sulaiman wanda shima shi yake kallo,"

Sulaiman yace "aboki mai yake faruwa ne?"
Mahmud yayi murmushin yak'e wanda yafi kuka ciwo yace "Abokina ba lokacin da zanyi maka bayani, kayimun Addu'a sauka lafiya, amma kuma yau zandawo komai dare,
Yana kaiwa nan ya wuce ya shiga mota ya tayar ya d'auki hanyar Abuja."

A yau Yusra cike take da murna da farin ciki, duk Wanda yasan Yusra ya kalli fuskarta a yau yasan farin cikinta na yau daban ne."

Hotel ta sanya aka kama mata naji da gani wanda ake Alfahari da ita a cikin garin Abuja."

Gaba d'aya friends d'inta saida ta gayyatosu da abokanen holewarta maza da mata, tana shaida masu masoyinta wanda zata aura, yana kan hanyar tahowa."

Gaba d'aya holl d'in anzagaye shi da babban kalanda mai d'auke da pix d'inta Dana mahmud wanda tasanya aka had'a mata shi,
Sunyi masifar yin kyau dama Yusra kyakkyawa CE, to bare kuma mahmud."

K'arfe biyar da rabi kowa ya halarci wurin daga ciki kuwa harda ita,

kid'e kid'e kawai kakeji yana tashi ko wacce budurwa rungume da saurayinta ana holewa wasu kuma suna manne da juna suna shan shisha."

A can sama take zaune tana kallon kowa d'aya bayan d'aya tana d'an kurb'a lemo a hannunta,
tanayi tana kallon agogon dake d'aure a hannunta, lokaci na tafiya har ynxun sweety bai k'arasoba to ko lfy?"

Tashiga tmbyar kanta."

Mahmud da gudu yakeyi ba kakkautawa Allah dai ya tsareshi ya shigo garin Abuja lafiya."

Kai tsaye gidan Alhaji Atiku ya nufa, ya tarbeshi cike da murna da farin ciki, anan yke shaida mashi dalilin kiran nashi, da yyi
shalele ce takeyin birthday,
Ta d'aga hnkalinta sai kazo ka tayata murna."

Murmushi yak'e kawai yyi baice komaiba,
Amma cikin zuciyarshi jinta yakeyi kamar ta fashe saboda bak'in ciki."

Alhaji Atiku baidamu da yanayin da mahmud yake cikin saba,
Illah ma sai dariya yakeyi domin yasan yau shalele zatayi barcin farin ciki, taga abin sonta

Batare da b'ata lokaciba ya shiga yimashi kwatancen inda take,
Yace " Idan kuma bazaka ganeba bari na had'aka da sojoji suyi maka rakiya."

Yayi saurin girgiza kai yace "nasan wurin ranka ya dad'e."

Alhaji Atiku yasaki dariya yace yau kuma fannin aiki KA mayar dani, KA ajiye daddyn a gefe kenan."

Bai tanka mashiba illah ya mik'e tsaye ya fito, had'ida ce masa daga can zan wuce."

Bai jira amsar Alhaji Atiku ba ya Juya ya fita a fusace, yana jinjina son zuciya irin ta wnn mutumin."

Alhaji Atiku yana ganin fitar mahmud cike da b'acin rai
ya mere baki yace "indai shalele tasamu abunda takeso duk wnda ranshi zai b'aci matsalarshi."

****************

A guje yaja motar yanufi hotel d'in, ynda yashiga wurin a guje mutane sai k'ok'arin kauce masa sukeyi."

" *YUSRA*."!!!
Yashiga filin da ake tsakiyar taron,
Ransa a b'ace daga jin yadda amon muryar sa take fita zaka San yana cikin mummunan b'acin rai."

Yusra yaci gaba da kiranta har sai da ya isa inda take yayin da kowa hankalinsa ya koma kansa ana kallonshi, wurin yayi tsit."

Sai mmki akeyi wnn ai shine mijin da tace zata aure wanda aka manna photunansu."

Kallonshi takeyi cikin wata siga ta so da k'auna, ganinshi da tayi taji sanyi a ranta, dama tasan za'ayi hakan saboda ta fahimci mahmud yanada zafi idan ranshi ya b'aci."

Murmushi takeyi tana shan ( _Juice_) d'inta tana kallonshi dama ta zaci hakan daga gareshi Dan hka bata damuba, bare ta amsa kiran da yake Mata."

Wnn ya k'ara k'ular dashi yaje har gabanta suna kallon juna, abinda takeso kenan ta kashe masa ido d'aya tana masa murmushi, tana shan juice d'inta."

Tuni zuciya ta kuma k'uleshi tsakanin tsanarta da haushinta da kuma k'inta suka k'ara d'arsuwa a zuciyarsa bai San lokacin da ya d'aga hannu ya kwad'a mata mariba, y kuma d'auki wani cup a wurin dake cike da juice ya watsa mata a fuska da k'arfi."

Saida ta razana tayi saurin mik'ewa tsaye a firgice, duk kunya ta isheta gashi jama'a kewaye dasu,

Ranta ya b'aci ta harareshi,
Meye haka mahmud?" Wnn wani irin wulak'ancine hakan a gaban bainar jama'a."

Nafad'a maki har abada bazaki tab'a samunaba,
Saboda bana sonki bana k'aunarki, bakya cikin tsarin Matan da nkeso na aura, dakeda banzar rayuwarki Baku tab'a ban sha'awaba, karki sake yin kuskure da gaggaci a kuma kirana, domin zanyi mki abunda yafi wnn."

Ya d'aga kai ya kalli kalandar pix d'insu da aka zagaye wurin dasu,
ya nufi wurin ya shuga yagawa yana zubarwa k'asa."

Ya kuma yimata kallon bnxa ya watsar,
Gaba d'aya jikinta a waje yake tamkar tsirara take,

yace "banida abinda zanyi da macce irinki bakya cikin irin matan da zan zab'awa 'ya'yana a matsayin uwa,
Na tsaneki yusra na tsaneki,
Yana gama fad'in hakan ya juya yatafi had'ida yin wurgi da table d'in dake gabanta wanda aka jera mata kek da lemunmuka,

Tana ganin yayi tafiyarshi tabishi cike da bacin rai idonta yana zubar da hawaye, tana fad'in "kayi kad'an Mahmud aurena ya zame maka dole idan kaga ka auri wata a duniya to nice,

'Ya'ya kuwa in har zaka haifi su to ka tabbatar da nice uwarsu,
Idan bana cikin matan da kakeso, ni Kai kana cikin tsarin irin mazan da nkeso."

Kuma ni yusra ina samun abunda nkeso kota halin k'ak'a don Haka ka sanyawa rywrka nice matarka."

Snn wnn cin mutumcin da kayimun a bainar jama'a a ranar da nake liyafar murnar zagayowar haihuta bazan mnta dashi ka d'au bashi."

Wnn shi zaisa na nanuna maka isata, in kuma maka dole ka shirya rywar aure dani kota girma kota arziki."

Bai sauratetaba ya shiga motar sa ya bule ta da hayak'i da k'ura yayi tafiyarsa yabarta cikin bak'in ciki da b'acin rai ga Wani rad'ad'in sonshi da ke mata zafi a zuciyarta idonta ya kad'a yayi jawur,

Ta kasa kukanma kunya kamar zata kasheta tayi da nasanin Zuwan da yayi,
Dakyar ta iya tanufi motar ta, tashiga sauran k'awayenta da jama'a da ke gurin suka taru suna bata hak'uri,
Amma bata saurare suba da k'arfi ta taja motarta tanufi gida Allah dai ya kiyaye ta isa gida lfya🤔
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅

Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.