Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 40

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕
16~October ~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💕

🔶🔸1⃣6⃣🔸🔶

.............Sopy ana makaranta, komai yana tafiya yanda takeso, sai dai tak'i sakin jiki da kowacce k'awa, duk da ana nuna mata anabuk'atar yin k'awance da'ita, bakamar wata zaliha, itadai sopy tana burgeta, sai dai sopyn tak'i bata fuskar dazata kusanceta, itakam sopy tana tsoron makirci irin nad'an adam ne, dan wadda ta yarda da ita, ta amincewa ita tafara saka mata shakku game da halayen d'an adam, wannan yasa take nisantar 'yammatan makarantar, sai dai tadage tana fahemtar abinda ake koya musu, kuma yanayin tasiri arayuwarta da kuma alk'awarin data d'aukarwa kanta da uncle kabeer.
Yau tanada lectures d'in safe, dan haka ta tashi tayi shirinta, cikin siket da riga na atanfa jaa da kore, tad'akko fareen hijjabi har k'asa tasaka, tad'an fesa turare mai sauk'in k'amshi, dukda bawata kwaliya tayiba tayi k'yau, dan sopy tanada k'yau irin wanda in kacika kallonta zai k'ara k'ayatar dakai, dukda bak'ace bak'inta yanada k'yawun kallo, gata da jiki maik'yau, irin wanda mutane sukan kirashi karuwan jiki, dolene idan kaga surar sopy komin ustazan cinka ka k'yasa, dan haka koda yaushe takan sance cikin hijjab, saboda idan har tasaka gyale tafita sai tasamu samari samada goma sunce suna sonta, wasukuma kwarjinin ta yake hanasu furtawa.
Tafito kafad'arta rataye da jar jakka, tafiya take cikin nutsuwa kanta ak'asa, tad'an kalli agogon hannunta mai sauk'in kud'i, tad'an tab'e bakinta, kai barima nazauna anan tunda munada sauran lokaci.
Tana nan zaune, saitaga d'alibai nata saurin shiga aji,wasuma harda d'an gudu, ita dai kallonsu takeyi, amma batayi wani yink'urin tashiba, zaliha tak'araso tana fad'in "lallai safiyya kina ganin kowa yana k'ok'arin shiga aji, amma ke kina zaune, yau munada lectures da "uncle G" kuma idan har yariga ki shiga aji tofa "k" bazai barki kishigaba......tak'arasa fad'a tana k'ok'arin tafiya, kafin sopy tace,"wani abu tuni zaliha takai k'ofar class.
Sopy tamik'e itama tanufi class d'in sai dai kash tana kaiwa ga k'ofar ajin shikuma malamin da zaliha takira uncle G yashiga.
Sopy ta tsaya cak abakin k'ofa, ta daure ta ce, "malam good morning!
Saida yay mata wani kallo na rainin hankali, sannan ya ce, "morning! da ganan yaja bakinsa yay shiru.
Sopy tai tsaye abakin k'ofa domin bai bata izinin shigaba, tana nan tsaye wasu 'yammata suka k'araso suma, d'aya acikinsu ta ce, "A'isha yaukam munzo arashin sa'a uncle G!! yarigamu shiga, wadda aka kira A'isha ta tab'e baki, ki ce, "sarkin 'yan girman kai yashiga, nikam wannan malami bansan miya d'auki kansaba???
Sopy dai tana tsaye tana jinsu, sai dai zuciyarta cike da tambayoyi, akan toshi wannan malamin wayeshi??? Ita dai yau kwananta hud'u a school d'innan, amma bai tab'a shiga a jinsu ba sai yau, to shikuma waye????
Ta maida kallonta gareshi, yana sanye da wani farin yadi mai laushi, rigar da kad'an ta wuce d'uwawunsa,k'afarsa sanye da bak'in takalmi,hakama hannunsa yana d'aure da bak'in agogo,, idanunsa cikin farin gilas siriri,, dukda dukannin kayan dake jikinsa bawasu masu tsada bane, amma shikam sun zauna dai dai da tsarin halittarsa.
Dogone amma ba canba, amma tabbas baza'a kirashi gajereba,bak'ine amma mai haske, yanada manyan idanu farare tas, wad'anda saboda haskensu har akan iya ganinsu tacikin kwalbar dake idonsa👓, dan har wani k'yalli sukeyi, kumatunsa zagaye yake da bak'in gashi sid'ik wanda ake kira saje, hakama bakinsa zuwa gemunsa shima zagaye yake da bak'in gashin, kansa babu suma mai yawa dan da'alama yanayin aski saidai ba irin tal tal d'innanba, domin akwai gashi kwance akansa bak'i sid'ik yasha mai sai k'yalli yakeyi, yanada d'an jiki dankuwa baza'a kirashi siririba,amma jikinsa yay masa k'yau.
Yad'an juyo yana kallon su sopy dake waje, yaji ajikinsa tabbas ana kallonsa, sopy tayi saurin d'auke idonta daga kallonsa, shima saiya d'an tab'e baki yacigaba da bawa d'alibai darasi akan English domin shi malamin turancine.
Yagama lecture d'insa, harda yin test, yazo fita sopy tamatsa gefe tabashi hanya, ko kallon inda suke baiyiba ya wuce abinsa, d'aya acikin 'yammatan nan uku taja tsaki, kai wannan gay d'in akwai rainin hankali saikace d'an wani da wata.

Bayan fitarsa suka shiga, class suka cigaba da karb'ar sauran darasi.
Sopy zaune ajikin wata bishiya, tana duba books nata, dan bitar abubuwan da'akai musu, zaliha tazauna a kusada sopy tana fad'in 'yar uwa dama kinanan?? Tun d'azu nake nemanki!!
Sopy tajuyo tana kallonta, e, ina nan, inad'an yin karatune.
Hakan yanada k'yau zaliha tafad'a tana murmushi.
Sopy ta maida kanta bisa karatunta, saikuma ta d'ago ta ce, "yauwa zaliha dan ALLAH bani labari gameda "uncle G" malamin d'azu da safe.
Zaliha ta gyara xama cikin zumud'i, dan ganin sopy yau takulata,, ta kaikaice tafara zabgo Zance tamkar 'yar jarida.
Nidai ayanda nasani sunansa malam yuseef Husain Ahmad, Gurum amma anfi kiransa da uncle G, malamin English ne, mutum ne mai aji, baya son wasa, bakuma ya wasa da kowace d'aliba, dan baya sakarwa kowa fuska, inhar kayi sake yashiga aji kafin kashiga, tofa ranar bakada rabo amasu samun darasinsa.
Yanada ilimi fiye da tunanin mai hankali, dan ayanda naji, nan makarantar yayi, yafita da face class na Resold dan haka suka d'auke shi aiki, zan iya ce miki iya abinda nasani kenan gameda tarihinsa.
Tad'anyi dariya k'awata kar dai kema kin kamu da son sa?? dan wlhy rabin 'yammatan makarantar nan duk son sa sukeyi,, harso suke yayi musu magana,, amma shi kam ko kallo basu isheshiba, shiyyasa suke cemasa mai girman kai.
Sopy ta harareta kekam na lura ke 'yar rainin hankalice,, daga tanbayarki tarihin mutum saiki min fassara, to kuwa idan kinason mu shirya dake kidaina min irin wannan.
Ganin ran sopy yab'aci, zaliha tashiga bata hak'uri.

Fareeda zaune ta zabga uban tagumi babu abinda yake damunta sai tunanin sopy, ba k'arya tayi missing d'inta, sai dai haryanzu bata tab'aji azuyarta ta cutar da sopynba, bare tayi nadamar Hakan, Abdul yay kissing d'in kuma tunta, tai saurin juyowa tana kallonsa, ya ce, "miye damuwarki?? Tad'an yatsina fuska ta ce, "sopy nake tunani wlhy nayi missing d'inta my love!
Abdul yad'an tab'e baki, yana mik'ewa kinga wannan matsalarki ce, ni yanzuma tashi ki kawo min abinci dan yunwa nakeji wlhy,, fareeda ta harareshi oh hakama zakace matsalata ce???
To inada matsala da damuwarki ne?? Cikin jin haushi fareeda ta ce, "A'a.
Ya ce, "to, kuma, zakiji haushina??
Fareeda dai taimasa banza tafice domin kawo masa abinci......................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕

[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 17~October~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💕

🔶🔸1⃣7⃣🔸🔶

................yauma duk k'ok'arin sopy nagujema tarkon uncle G!, amma saida ta fad'a, dan kuwa harya shiga aji, tad'an cije leb'enta, dan bak'in ciki, tabishi da kallo yana tsaye gaban allo, yauma cikin manyan kaya sai dai yau shaddace mai ruwan k'asa, d'inkin dai tamkar na ranar, dan rigar itama bata wuce d'uwawun saba, amma yau babu glas.
Sai da yagama lecture d'insa sannan ya ce, "kowa yashirya yin test, kuma yau har nawaje su shigo.
Wannan magana tasa tabawa mafi yawan d'aliban mamaki, domin duk yanda kuke dashi inhar yarigaka shiga aji tofa bazaka shigoba, bare idan zayyi test, amma yau dakansa yabuk'aci su shigo.
Bayan shigowar su sopy da ragowar makararru, ya gabar musu da tanbayoyin.
A hankali yake takawa cikin class d'in bakajin motsin komai sai takunsa, kowane d'alibi ya duk'ufa wajen aikinsa, k'amshin turarensa duk ya gauraye class d'in, yak'araso dai dai inda sopy take zaune, yazuba mata idanu dan ganin batayi wani yunk'urin rubuta wani abubama.
Jin antsaya akanta yasata d'agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, sopy tai saurin janye nata idon dan baxata juri kallon saba, jikinta asanyaye tamaida kanta ga takarda.
Shikam wani abu yaji yasoki kansa harzuwa babban d'anyatsan kafarsa, yarintse ido yabud'e, ya salam yafad'a tare da jan ajiyar zuciya, ya wuce abinsa yana cigaba da zagaye d'alibai dan kar suyi satar amsa.
Lokacin daya basu yana cika yakarb'e, yafita abinsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.