Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 40

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸2⃣6⃣🔸🔶

...........Tunda tabar office d'in tazama wata shiru shiru, gaba d'aya abin mamaki yake bata jitake tamkar amafarki, wai itace zata zama matar uncle G!, kai wannan lamari tamkar ba gsk bane, lallai ko bata son uncle G! tofa dolene ta aureshi, kodan ta k'ara nisanta kanta da Abdul, da fareeda, wasu hawaye suka zubo akan kumatunta, wlhy tana son fareeda, amma gashi fareeda tajawo abinda yanisantasu da juna, tana matuk'ar kewarta da son ganinta, takifa kanta saman tebir tana kuka.
Zaliha ta tab'ata, sopy lfy dai ko? Sopy tad'ago tana kallon zaliha, fuska share share da hawaye, ta ce, "babu komai wlhy zazzab'i nakeji".
Ayya sannu to kitashi na kaiki hostel mana.
Sopy ta girgiza kai ki bari mu gama lecture tunda saura d'aya.
Zaliha ta ce, "to shikenan", amma fa wata magana najiyo yanzu akanki!!.
Sopy ta ce, "akaina kuma zaliha??, wace irin magana kenan?.
Zaliha sarkin gulma ta gyara zama, wlhy wasu samari naji suna fad'in way soyayya kukeyi keda uncle G! Wai shiyyasa kikema samari girman kai, dan anga wai yabiki library d'azu.
Sopy ta k'urama zaliha idanu, kamar zata cinyeta, saida zaliha ta tatab'ata, sannan taja ajiyar zuciya, zaliha ta ce, "mi kuma kike tunani?
Sopy ta girgiza kai babu komai, amma ni k'arya suke min, dan kawai sunga yashiga library sai suce wajena yaje.
To aii wai bayan fitowarsa ke kuma kinje office d'insa!.
Sopy taja tsaki, ta ce, "kai magulmaci madai yaji haushi wlhy, to uncle G! Abokin uncle d'inanane tare sukai karatu a wannan makarantar, wannan itace dangan takar dake tsakaninmu, sai a daina gulmarmu aii, ta maida kanta ta kwanta.
Zaliha uwar gulma aka jinjina kai, kinsan ba kowane yasan hakaba, dan nima dabaki fad'aba ban saniba, dan wlhy nima nazata soyayya kukeyi, to ammafa kallon dayake miki irin na masoyane, idan fa yana lecture to gaba d'aya hankalinsa yana kanki, to kinga aii masu fad'a basuda laifi.
Banza sopy tayi mata, dan tasan zaliha magul maciyace tafad'a aji, ita ba k'ok'ariba sai iyayi da gwalli.
Ganin sopy ta shareta sai tatashi ta fita, wajen samarin ta nufa tazauna, suka shiga tambayarta zaliha tagaya miki, zaliha ta rik'e baki tana fad'in kukam magulmatane wlhy, idan ance maxa sun iya gulma ku musa mana, to ta ce, "wai abokin uncle d'intane.
Wani acikin samarin ya ce, "kai wlhy ban yardaba, k'arya ta fad'a miki, amma kicigaba da saka mata ido zaki hano gskyr maganar, zaliha tamik'e tana fad'in aiko saina gano bari naje dan za'ayi mana lecture yanzu.
Samarin suka shek'e da dariya, suna fad'i zaliha dama ke kina fahimtar karatune.
Zaliha ta hararesu tai gaba, dan tasan magana suka gaya mata.

Koda sopy ta koma d"aki takasa aywatar da komai, tunani ya bai baye kwakwalwarta, ji tai yau son Abdul ya dawo mata sabo azuciya, jitai a yau zata iya auren Abdul suyi kishi da fareeda, ta rintse ido ta bud'e tana fad'in, ya ALLAH idan shaid'an ne yake k'awata mini hakan ALLAH ka dawo dani cikin hayyacina!, ta fashe da kuka tana girgiza kai, wlhy bazan iya zaman kishi NI DA AMINIYATA ba har abada, fareeda na hak'ura na bar miki Abdul har abada wlhy, nabar miki! Na bar miki!!! Ta k'arasa fad'a cikin kuka mai ban tausayi, masu karatu nimadai saida na matse hawaye dan sopy tabani tausayi.
Ta dad'e tana kuka daga k'arshe ta dangana, tayi shiru, sai shashsheka da takeyi, dahaka wani waha lallen barci ya d'auketa.
Da safe da ciwon kai mai tsanani ta tashi, dan haka bayan gama sallar asuba saita koma barci.
Wringing d'in wayartane ya tasheta, sunan uncle kabeer tagani akan wayar, ta tashi da sauri, tana amsa wayar, bansan miya fad'a mataba ta tashi da sauri tahau shirin fita.
Kai tsaye office d'in uncle G! Tanufa dan tasan uncle kabeer yanacan, ta kwankwasa aka bata izinin shiga, da sallama tashiga, suka amsa mata, ta rissina tana gaishesu.
Uncle kabeer ya d'ora da fad'in my daughter ya dai? Naganki kamar kina cikin damuwa?,
Sopy ta girgiza kai, ta ce, "uncle lafiyata k'alaw kainane kawai keyin ciwo.
Ayya sorry my daughter, yanuna mata kujera ta zauna, uncle G! Ya ce, "kinsha magani ko?.
Ta ce, "e nasha shine ma yasakani barci.
Okey ALLAH yabaki lfy.
"suka amsa da amin."
Uncle G! Yamik'e yana fad'in bari naje nagabatar da lecture.
Okey lecturer!! Uncle kabeer yafad'a cikin tsokana.
Uncle G! Yafita yana fad'in kana nan baka canjaba kabeer.

Bayan fitar uncle G!, uncle kabeer yadawo da hankalinsa ga safiyya da kanta yake kasa tana wasa da zoben hannunta yay gyaran murya, sopy ta d'ago tana kallon sa, yay mata murmushi d'iyata yaya dai??.
Itama ta murmusa ta ce, "bakomai uncle.
Ya ce, "okey to shikenan, dama wata magana ce takawoni, duk da youseef yasanar dani kun fara maganar jiya ko??.
"E, uncle! Hakane".
Uncle kabeer ya ce, "to ke yakika gani?? Kin amince??.
Sopy tay kasa da kai saboda kunya.
Karki damu d'iyata, karki bari kunya tahanaki fad'ar gskyar ki, inhar baki sonsa ki sanar dani.
Sopy ta rufe fuska da hannuta ta ce, "ina sonsa uncle!!.
Uncle kabeer yay dariya, "ALHAMDULILLAH", yafad'a yana gyara zama, lallai ina tayaki murna d'iyata!!, da samun miji nagari mai addini da tarin ilimi, nasan watarana zakiyi alfaharin kasancewar youseef a matsayin mijinki, zakiji dad'in zama dashi domin kuwa mutumin kirkine shi, ALLAH ya kaimu lokacin musha biki.
Sopy taja hijjab ta rufe fuska.
Uncle kabeer yayi dariya, bazakice amin ba sopy.
Ta ce, "kai uncle wlhy kana bani kunya.
To bani kunyata uncle kabeer yafad'a.
Haka sukaita hirarsu, har uncle G! Yadawo, tunda ya shigo bakin sopy ya mutu, ta daina magana takuma sunkuyar da kai k'asa.
Uncle G! Ya nunawa uncle kabeer sopy da baki, uncle kabeer yay dariya ya ce, babu ruwana nidai, kunfi kusa.
Sopy ta d'ago karaf ta kama uncle G! Yana mata gwalo.
Batasan sanda ta harareshiba, ya ce, niko!!.
Saida taje bakin k'ofa sannan ta ce, "e, ta fita da gudu.
Dariya sosai sukeyi, uncle G! Ya ce, "kabeer dama haka safiyya take??.
Uncle G! Yay dariya ya ce, bazakaji mutuwar sarki abakinaba.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, sopy tana karatu yanda yakamata, takanje gida weekend lokaci2 idan tasamu dama, shak'uwa kuma tana k'ara shiga tsakaninta da uncle G!................✍🏻

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 27~October~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💞

🔶🔸2⃣7⃣🔸🔶

..........BARI MU WAYWAYI FAREEDA....
Fareeda kam rayuwa ta canja mata, kwance take tana fidda numfashi da k'ar sakamakon zazzab'in dake jikinta, babu abinda ya haddasa mata zazzab'in sai uban aiki da umman Abdul tasakata, dak'yar tagama aikin tajawo jiki tazo ta kwanta.
Abdul yashigo ko sallama babu, ko kallo bata isheshiba ya wuce yana canja kaya, fareeda tabishi da kallo tana zubar da hawaye.
Ya gama yanufi hanyar k'ofa domin fita, ta daure ta ce, "Abdul!!.
Ya juyo yana kallonta awulak'ance batareda yayi maganaba,
Cikin kuka ta ce, "dan ALLAH Abdul inaso muyi magana, ka taimaka kazauna.
Ya gyara tsayuwa kinga malama idan zaki fad'a ki fad'a dan babu wani zama dazanyi, inada gurin zuwa.
Fareeda ta cije baki, cikin k'arfin hali ta tashi zaune.
Ta ce, "Abdul dan ALLAH miyasa ka juya mini baya, yakamata ka fahimceni, yanzu ka daina kula dani, kana ganin wahalhalu dana ke ciki agidannan ga gallazawar mahai fiyarka amma baka tab'a nuna rashin jin dad'in kaba, dan ALLAH karka barni Abdul, yanzune nafi buk'atar zama dakai Abdul, karka manta saboda kai nabar iyayena, nabar 'yan uwana, nabar aminiyata mai sona dason ganin farincikina, amma danmi zaka barni bayan yanzu kai kad'ai gareni, saikuma wannan cikin dakake gani bai dace yazoba ayanzun.
Abdul yaja tsaki, yanuna ta da d'anyatsa yana fad'in, wlhy idan kina tare da wannan shegen cikin bazaki tab'a samunaba, zaki cigaba da rasa abubuwa arayuwarki kuwa, kamar yanda wad'ancan mutanan suka barki to nima haka zan barki, amma har yanzu kinada sauran dama, inhar kika yarda aka zubar da wannan cikin tofa zan dawo miki a matsayin Abdul d'inki nada, inko har kika cigaba da bijirewa buk'ata ta tofa zaki shiga k'angin rayuwa wanda yafi na yanzu, kuma bazaki raini d'an dake cikinkiba agidannan, dan nafad'a miki ban shirya haihuwaba yanzu, ban shirya zama uba ba yanzu, amma kikayi sakakin d'aukar ciki saikace wata akuya, acikin wata biyu da zuwanki, ke wlhy yanzuma dan abbana ya hanani sakinkine, amma kicigaba da zama akan taurin kanki kigani, idan ban yi waje dakeba, nabaki nanda sati biyu ki yanke wadda zata fisheki, ko ki yarda azubar da ciki, kicigaba da zama dani, ko kik'i yarda nayi waje dake.
Fareeda ta fasheda kuka ta ce, "haba Abdul kayimin adalci mana cikinnan fa d'an kane, ta hanyar aure muka sameshi, kuma namiji shike bada kwan haihuwa, miyasa bazaka gane ba laifina bane? Kuma wlhy ana mutuwa wajen zubar da ciki ko mutum yarasa mahaifarsa, baka gudun d'aya acikin wad'annan yafaru dani ne??.
Abdul yaja tsaki, yafice yana fad'in matsalarkice kuma wannan, nidai nafad'a miki buk'a tata, idan kin kiyaye kin tsira, idan kin cigaba da bijirewa zaki koma gidan tsohone.
Kuka sosai fareeda takeyi dan duk taji kalaman Abdul na k'arshe, ta tura kanta cikin filo tana gunjin kuka, yaune rana ta farko data tab'ajin wani abu mai kama da nadama ya ziyarci zuciyarta, saidai har yanzu tana son Abdul d'inta, tanaji kuma a zuciyarta tafi safiyya sonsa walhy, lallai dolene tabi hanyoyin dazata magance matsalar dake tsakanin ta da Abdul, koda kuwa zubar da cinne, tunda shine tushen faruwar matsalarsu,😳😳 lallai fareeda bakida hankali.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.