Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 32 of 40

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Akwana atashi babu wuya gurun mai duka, komai yana tafiya yanda akeso, Sopy tana samun farin ciki awajen mijinta, takanji babu yashi a rayuwarta.
To shima a b'anfarensa yakanji babu tankar Safiyyar, kullum burubsu su farantawa juba, takan tsara masa abinci mai gam sarwa dasaka nishad'i, kullum tana cikin kwalliya ta d'aukar hankali, ta bad'e gidanta da jikinta da k'amshi, kullum burunta tayaya zata farantawa mijinta.
Bata wasa da samo hanyoyin rik'e miji, dan haka bily ta sakata a groups masu dama, takan tsinci abubuwan k'aruwa acikin HAUSA NOVELs masu yawa, dan kowa da irin baiwar rubutun da ALLAH yabashi, idan dare yayi su kashe junansu da soyayya itada HUBBIN ta.
Uncle G! yana matuk'ar alfahari da ita.
Matsala d'aya take fuskanta, itace fareeda, dan yanzu fareedar tafito dawasu salo2 na rainin hankali, sai lokacin data fuskanci sun kusa dawowa saita ci kwalliya ta zauna a tsakar gida, da sun dawo itace zata bud'e musu get tana kwar kwasa, suna shigowa falo zatayi saurin kawoma uncle G! ruwa ko lemo, da daddare kuwa tana nane dasu a falo, har saitaga sun shiga sannan take tashi, takan k'ir k'iri dafa wani abu takawoma uncle G! wai yaci, idan suna hira, taringa wata kwar kwasa da kwantar da murya kamar tana kusada mijinta,ko sopy ta gwaleta tofa bata nuna jin haushinta, wani rainin hankali kuma data d'auka shine datayi isha'i saitayi shiri cikin kayan barci tazo ta zauna falo suna hira.
Wannan lamari yana k'ona zuciyar Safiyya.

Yauma suna falo suna hira, uncle G! yana kwance saman doguwar kujera, yayinda sopy take zaune a k'asa saitin kansa tana cin tuffa (Apple), fareeda kuma tana saman kujera tana satar kallon uncle G!, wandashi bama ta isheshi kalloba, sopy tana kula da ita.
Zuwa can sopy ta ce, "wayyo ALLAH hubbina??, uncle G! ya juyo da sauri yana kallonta, ya ce, "ya akayi Sopyna?, cikin shagwab'a ta ce, "jinayi kaina ya sara.
Ya tashi zaune yana fad'in zona yimiki kamu, dan bana son kisha magani, saboda gudun ganganci, bansaniba ko nayi ajiyar baby.
Sopy ta mike da nufin zama kusa dashi, amma saiya jawota saman cinyarsa, ta ce, "ngd hubbina.
Yayi murmushi yana fad'in wannan aikinane, addu'a yafara yi yana tofa mata, bayan ya gama tawani kanne masa ido d'aya tareda d'aga masa gira.
Aii sai jikin mutumin naku yasaki, kwata2 ya manta da wata fareeda afalon, saiya had'e bakinsa da nata, yashiga sumba tarta cikin nuna kwarewa, Sopy saita bada kai bori yahau, sunkai tsawon lokaci suna abu d'aya, zuwa can yashiga shafata.
Wani kududun bak'in ciki yatokare zuciya fareeda, ta had"iye wani mugun yawu wanda yasakata sark'ewa tafara tari.
Sai a sanna uncle G! yatuna akwai wata halitta fareeda a falon, suduka suka d'ago suna kallonta, sopy tayi wani murmushi mugunta, tad'aga yatsun hannunta biyu tama fareeda sorry, cikin wani murmushin rainin hankali ta ce, "sorry fareedana, munata soyayya agabanki, kinsan hubbina ya iya mantar dani duniyar dana ke ciki, wlhy nama manta kinanan, ta sumbaci hannun uncle G! sukaima juna murmushi.
Jin kalamun sopy na rainin wayo sai suka saka zuciyar fareeda kumburo wa, jita ke mar zata fashe, har fuskarta saida ta nuna alamun b'acinrai.
Sopy ta ce, "hubbina?
Uncle G' ya ce, "na'am sopyna.
Ta ce, "yakamata kasiyoma fareeda tv sai asaka mata a d'akina, dan bai kamata tana zama damu a falo muna tayar mata da hankaliba, kasan gwauro bai iya shiga matsalaba, gashi kuma babu mai taimaka mataπŸ˜†πŸ˜œ.
Uncle G! ya sumbaci bakin sopy ya ce, "gsky ne sopyna, insha ALLAHU zanyi k'ok'arin hakan, dan nima nakula tana shiga damuwa da takura.
Fareeda tak'ara kumewa dajin kalamun sopy da uncle G!, ta kulama sun raina mata hankali, da sauri tatashi tana hawaye ta shige d'akin sopy.
Sopy ta bita da kallo tana 'yar dariya, ta mik'e tana fad'in hubbina bari najiyo miye damuwar "AMINIYATA!!!!!;".
Uncle G yabita da kallo yana murmushi, yasani sarai bak'ak'en magan ganu sopyn tagawa fareeda.
A can kuwa sopy tana isa tabud'e d'akin ta shiga, agado ta tarar da fareeda tana kuka, sopy tad'an tab'e baki sannan ta k'arasa gaban gadon tana tafa hannuwa, ta ce, "fareeda kenan nakula ke har yanzu d'aukata kike amatsayin safiyya sakarai, fareeda!! Tabas abaya kinyi nasarar kwace Abdul daga hannuna, to ki d'auka awanna lokacin kece kikayi winning d'in game d'in, nikuma nasamu game over.
Amma saidaifa awannan karon ta canja zani, domin nima da shirina nazo fagen famar, kisa azuciyarki uncle G! nawane nikad'ai, babu wata kucakar mace data isa naraba son youseef da ita, karki d'auka wani ban k'aro k'irjinki da saka kayan barci kizauna agabansa zai ja hankalinsa a kanki, 'yammatan dasuka fiki ilimi da wayewa ma sunyi abinda yafi haka amma basuci nasaraba.
To kema inaso ki d'auka aranki bazaki tab'a yin nasaraba, tuni nasan kece kike zubamin gshiri, yaji, sukari acikin abinci, fareeda son gsky babu abinda yake rusashi, nida uncle G! son gsky mukema juna bana sha'awa ba, dan haka ki daina wahalar da kanki wajen hangen zaki iya rusa wannan soyayyar, bare harki samu damar mallakar mijina.
Sopy tayi wata 'yar dariyar k'eta, ta ce, "lallai yau nayarda da batun aunty zainab, datace ke kaskace rab'u mai jini, kuma ke bom ce, tofa saidai ki d'auka awannan karon remote d'in bom d'inki yana hannuna, idan nagadama saina danna ki tarwatse, dan haka ki dawo da han kalinki jikinki, tun kafin kiyi asararsa, ki daina biyema shed'aniyar zuciyarki datake d'ora miki karatun da babu fassara, inko ba hakaba kina gab dashiga makarantar dana sani.
Tana kaiwa nan tafice abinta.

Fareeda tana kwance kamar gunki, zuciyarta cike da mamakin kalam safiyya, wai yaushe sopyn ta waye?, ya akayima tagano sirrikan zuciyarta haka?, lallai yau sopy tagaya mata magan ganu masu ciwon gsk, irin wanda babu wani mahaluki daya tab'a gaya mata kwatan kwacinsu, ta dun k'ule hannu ta naushi iska, da sauri nafito ina tuntsura dariyaπŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†, dan karta maujeni nima, tabar mijina da jinya.
D'akin uncle G! na nufa, amma saina tarar sun rufe k'ofa, dan haka na nufi hanyar fita, dan bazan koma wajen fareeda 'yar mahakaciya ba ta bibbigeni abanza, gobe nakasa kawo muku rahoto😜😜......................✍🏻

Assalamu alaikum, ina mik'o d'umbin gaisuwa ga dandazon makaranta littafin ""NI DA AMINIYATA!!!,"" ina muku fatan alkairi a duk inda kuke, ina kuma gdy da k'aunar da kuke nuna mini,, ALLAH yabarmu tare, ya had'amu a ALJANNARSA baki d'aya.

πŸ‘ŒπŸ»acigaba da gashiπŸ˜‚!!!!!!!!!!!!!!!!...πŸ‘ŒπŸ»

πŸ’žBilyπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žMrs Abdus'salamπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žI LOVE YOU MY FAN'sπŸ’žπŸ’ž
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 21~November~2016

πŸ”·πŸ”ΉNI DA AMINIYATA!!!πŸ”ΉπŸ”·

NA BILKISA IBRAHIMπŸ’ž

πŸ”ΆπŸ”Έ5⃣1βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά

...........WASHE GARI. Fareeda kasa fitowa tayi, har sukayi break bata fitoba, Uncle G! ya ce, "Sopy yau kuwa lafiya naga fareeda bata fitoba??.
Sopy tad'an murmusa tareda fad'in lafiyarta k'alau, k'ila ta k'oshine.
Uncle G! yad'an tsura mata idanuwa, domin son gano wani abu, amma sai Sopy ta kauda kai tana dariya, shima saiyayi dariyar ya ce, "miya baki dariya sopyna?.
Sopy ta ce, "kaine kabani dariya, dan naga ka kafeni da kallo kamar a kotu.
Ya ce, "Sopyna baki da dama kema, nakula randa natashi k'ara aure zamusha fama, dan kinada kishi, ya k'arasa maganar cikin tsokana.
Sopy ta d'aure fuska tamau.
Uncle G! ya tuntsure da dariya, harda buga kai, yadawo kusada ita, yadafa kafad'ar ta kinga sopyna dawasa nake miki, ke kad'aice matar youseef daga ke babu k'ari.
Sopy tad'an turo baki tana fad'in nidai ban yardaba.
Ya jawota zuwa jikinsa ya ce, "mikike so nayi miki dan ki yarda??, ta d'ago tana kallonsa, ta ce, "kayimini alk'awari.
Yad'an kafa mata idanu na tsawon minti biyu, saikuma ya lumshe idanunsa ya bud'e, ya jinjina kai yana fad'in ni youseef nayi alk'awarin kasancewa da safiyya har k'arshen rayuwata, kuma ita kad'ai amatsayin matata, saidai idan wata k'addara ko jarabawa takawo sab'anin haka a rayuwarmu.
Sopy ta rungumeshi tana murmushi, ta ce, "nima hakan take a gareni hubbina, ALLAH kuma yabamu ikon ruk'e junanamu da hak'uri da juriya.
Uncle G! ya rungumeta yana fad'in amin ya Rabbi sopyna.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.