Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 37 of 40
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 26~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸5⃣6⃣🔸🔶
.............Sopy bata farkaba sai la'asar bayan ruwan da'aka saka mata ya k'are, uncle G! ya taimaka mata tayi wanka dan taji k'arfin jikinta.
Su aunty hafsat suka shigo suna mata sannu, gwaggo takawo mata Abinci da Awara da fura wadda tasha nono mai k"yau.
Aunty hafsat ta ce, "k'anwata azuba miki abincin ko? kici.
Sopy tad'an yatsine fuska ta ce, "aunty nak'oshi, uncle G! ya harareta ya ce, "mikike nufi da kin k'oshi, haka kikeso ki zauna da yunwa?, tun jiyafa rabonki da cin abinci.
Gwaggo ta ce, "A'a yusufa abita ahankali, gwaggo ta matso kusada ita, ta ce, "d'iyata daure kici koda awararce, ko fura, fad'a min wanne kikeso, inkuma bak'ya sonsu a sake miki wasu.
Sopy ta ce, A'a Gwaggo zanci awarar, to shikenan gwaggo ta fad'a, Libabatu ta zuba mata awarar ta mik'a ma uncle G! dake kusada ita.
Ya d'auka yakai bakin sopy, sopy tayi k'asa da kai dan kunya, ahankali ta furta uncle kabarsa zan iya ci dakaina.
Ya ce, "karb'a kici kinga hannunki akwai datti gashi kuma jikinki babu k'arfi.
Gwaggo dake jinsu ta ce, "in bata son naka, bari ni nabata, da sauri sopy ta bud'e baki uncke G! ya saka mata awarar.
Abun yabasu dariya, dan haka suka tuntsure da dariya suduka d'akin, aunty hafsat ta ce, "k'anwata kunyarki tayi yawa.
Gwaggo ta ce, "aii haka akeson mace takasance mai kunya, Dan kunya adon mace .
Sopy tad'anci Awarar, dan tayi mata dad'i sosai, bayan tagama ta k'ara kwanciya, uncke G! ya ce, "tashi kid'an zauna ki huta, kar kwanciyar tayi yawa.
Gwaggo ta ce, "A'a kabarta ta kwanta, k'ila tafi jin dad'in kwan ciyar.
Ya ce, "to.
Sai dare su aunty hafsat suka tafi.
Baba ya sissiyoma sopy abubuwan kwad'ayi ya ce, "abata taci, bayan yai mata sannu suka tafi b'an garensu.
Uncle G! ya kalleta yana murmushi, ya ce, "lallai ke 'yar gata ce, kowa jiyake dake, tayi murmushi tana fad'in kokana kishine?.
Ya murmusa tareda d'ora hannunsa akan cikinta, ya ce, "bawani kishi, kema aii gamasu kwace miki fada nan sun kusa zuwa.
Cikin rashin fahimta sopy ta ke kallonsa, ta daure ta ce, "ban gane abinda kake nufiba??, ya kanne mata ido d'aya ya ce, "zaki gane, alokacin da yarona ko yarinya suka fara aikin 'yan kwallo acikinki.
Sopy ta zaro idanu waje ta ce, "kamar ya ya?, ya kwanto da kanta bisa cinyarsa, yad'ora hannunsa saman cikinta, d'ayan hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ce, "Inada babbar ajiya awannan cikin, ma'ana saka makon ciyonki na bayyanar yarona ne.
Sopy tasaka hannu ta rufe fuska dan tagane miyake nufi, yay 'yar dariya, lallai yarinya kardai kice yarona d'an farin k'auye za'a maidashi?, to wlhy ban yardaba, garama tun yanzu na fad'a miki, dan banyarda a b'oyema yarinyata ko yarona suna ba, banyarda atureshi saboda yazo a matsayin d'an fariba, yasa hannu ya cire hannunta data rufe fuska dashi.
Saita rintse idanuwa, yakai bakinsa kan nata, yafara al'amura.
Na ce, "hummmm shidai uncle G! baya gajiya dayin kiss, bare kwana biyu ba'a had'uba.
Haka al'amura suka cigaba da tafiya a gurum, sopy tana shan tarairaya, duk abinda ta ce, "tana so sai an nemamata, koda awajen gurum yake kuwa, gwaggo ta hanata aikin komai, d'akinsuma Aysha ce take gyarawa kullum, a b'an garen uncle G! kuwa abin ba'a magana, suma su lubabatu suna bada gudummawa, dahaka sati biyun dasuka d'ebo tacika.
Amma baba da gwaggo sun hana tafiya, sunce tunda ba'a koma makarantar ba to bazasu tafiba sai sopy ta k'ara samun sauk'i, badan uncle G! yasoba dole ya hak'ura.
Shikam yana so su tafine dan yana cikin takura, gashi kuma wata sa'inma sopy a d'akin gwaggo take kwana idan jikin yay tsanani, itama kanta sopyn ya lura yanzu gudunshi takeyi.
Itako sopy bataso uncle G! yazo mata da buk'ata ne, shiyyasa take baya2 dashi, dan bata so yacika takura mata.
Kunsan wani cikin yana faruwa haka.
In tak'aice mu dai saida sukayi wata d'aya dawasu kwanaki, dan saida aka sanar an koma yajin aiki sannan baba yabarsu suka dawo kano.
Sun dawo cike da kewar muta nen gurum, yayinda suma suka barosu da kewarsu.
Tsaf suka tarar da gidansu an gyara, wananan duk aikin aunty Asiyane, sunji dad'i sosai, suna zuwa sai wanka da cin abincin da aunty asiyar ta aiko musu.
Bayan sun gana suka kwanta dan su huta.
A b'an garen fareeda kuwa al'amira sai ahan kali, dan ba komai take nema ta samuba, sauk'in tama tana agidan su sopyne, amma tayi bak'i ta rame kamar ba'itaba, kullum sai inna ta ce, "taje ta gaidasu mama.
Badan tasoba take zuwa, dan idan taje gidan sai mama ta had'e mata rai, daga ita har baba basa sakar mata fuska, lamuran suna damunta, amma tasan laifintane.
Yau ma tana zaune ad'akin sopy nada, ta had'a kai da guywa, hawaye suna kwaranya a idanunta, tana tuna rayuwa irin ta gidan sopy, duk da uncle G! bamai kud'i bane, amma yana k'ok'ari akan iyalinsa, yana wadatasu da cima mai dad'i, amma nan daga tuwo sai shinkafa, tarik'e kai tana hawaye.
Araina ne ce, "su fareeda anji jiki, an shiryu badan ALLAH ba😜.....................âœðŸ»
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 27~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸5⃣7⃣🔸🔶
BAYAN WATA TAKWAS
...........Rayuwa mai gudu da sauri, daga safiya tayi sai gari ya waye, fareeda dai an shiryu da gsk, dan takoma makarantar islamiyya, gashi takoma wata shiru2, batada burin daya yuce tasamu miji tayi aure itama ta zauna agidanta, kullum kuma tana cikin yin istigifari, takan shiga gidansu ta taya mama aiki, dukda har yanzu mama bata sakar mata fuska, haka aikin inna duk ita takeyi, damuwar ta d'aya sopy, dan har yanzu sopy bata yafe mataba, ko gidan tazo bata kulata, gaisuwama sama2 sukeyi, kullum burinta ALLAH yakawo randa sopy zata yafe mata sukoma yanda suke da.
Inna tana k'ok'ari wajen yiwa sopy nasiha akan tayafema fareeda tunda ta shiyu, duk sanda tazo gidan saita yimata irin wannan nasihar.
To itama sopyn tayarda fareeda ta canja, amma tanaso tak'ara shiryuwane kafin ta ce, " ta yafe mata, dan tuni ta yafema fareedar batadai furta bane kawai.
GIDAN SOPY
Sopy anata fama da k'aton ciki, wanda da'alama ranar haihuwa kawai ake jira, dan tama daina zuwa makaranta.
Afalo na isketa itada uncle G!, tana zaune a saman kafet ta mimmik'e kafafuwa, tasaka filet d'in kankana a tsakkiya tana sha, uncle G! Yana gefenta kwance a doguwar kujera.
Ya kalleta ya tuntsure da dariya, sopy tajuyo tana kallonsa, ta ce, "miya baka dariya? hubbina!.
Cikin dariya uncle G! Ya ce, "wlhy ke kika bani dariya sopyna, jibi yanda kika mik'e kafafu kina shan kankana, ALLAH kirage ci, nakula aranafa saikici abinci sau biyar.
Sopy ta murgud'a baki😠tana fad'in to waye yaja mini?, aii dai kowa yasan da bahaka nake da ci kamar jakaba ko?.
Uncle G! Ya kwashe da dariya, ya ce, "aina kusa kad'a miki tanbarin acici kazar gona.
Sopy ta watsa masa harara, saikuma ta shagwab'e fuska tafara kukan shagwab'a, ya sakko yana gintse dariya, kusada ita ya zauna yana shafa bayanta ahankali, acikin kunnenta ya ce, "yakamata kibar shagwab'a, dan kinkusa zama momy.
Yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta.
Ta ce, "to ba kaibane kake tsokanata, ya sumbaci kuma tunta yana fad'in to yi hakuri na bari maman baby.
Yanzu mikikeso nayi miki danki huce, ta nuna masa k'afafunta da sukayi d'an fushi.
Yay murmushi dan yasan mitake nufi, ahankali yafara mammatsa mata kafafun, ita kuma tafara lumshe idanu, ya ce, "karfa kiyi mini barci 'yammata!!.
Sopy tad'an bud'e idanu tana murmushi, ta ce, "kasan kuwa harna fara jin barcin wlhy.
Ya ce, "aii ke yanzu kin zama kasa, dan ko fira bak'ya barinmu muyi, b'urun2 saikice aje akwanta, ta ce, "to yazanyi hubbina!, nima ba laifina bane, ya ce, "gsky ne laifin babynane, yafad'a yana kanne mata ido d'aya.
Ta ce, "yauwa hubbina wai yaushe kacema Aysha zata zo?, ya ce, "sai ranar juma'a, tunda ta ce, "Al'hamis za'ayi musu hutu.
Sopy ta ce, "ALLAH ya kaimu, yakuma kawo mana ita lfy.
"Amin uncle G! Yafad'a yana murmushi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.