Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 40

Abdul yace" gsky baba saidai kuyi hak'uri wlhy bazan iya rabuwa da matataba ina sonta,, ina kuma burin kasancewa da ita har abada.
Fareeda ta karb'e wlhy nima baba inason mijina dan ALLAH karku rabamu,,,, aii kafin tarife baki yaya lawan yabata duka jikake taffff,, ta kwalla k'ara tana fad'in wlhy sai ALLAH yasaka min tunda ban yimimaka komai ba mugu azzalumi.......yako tashi yashiga dukanta tako ina,, Abdul yamik'e yashak'i wuyan yaya lawan yana fad'in kai bagidaje mahaukaci wlhy idan hannunka yak'ara sauka akan matata saina kasheka.
Uncle kabeer yadaka ma Abdul tsawa yace" sakeshi,, jikin Abdul yana rawa yasaki yaya lawan yakama hannun fareeda yana fad'in muje gida,,, baban fareeda yamik'e murya a sark'e yace" fareeda inhar kika koma gidan Abdullahi to babuni babuke, nacireki daga cikin 'ya'yana kije nabar masa ke.
" fareeda tace" baba nasan rankane ab'ace amma wataran zaka gane hikimata ta auren Abdul, harma kayi alfahari da hakan,, mama tace lallai fareeda wuyanki ya isa yanka yanzunan mahaifinki kike fad'ama haka saboda d'a namiji,, fareeda ta tab'e baki mama kema nasan bazaki tab'a ganewaba sainan gaba,, kamar yanda kuka buk'ata zanyi nesa da ku da 'ya'yanku har zuwa lokacin da zaku huce,, aunty zainab dake kusada ita ta wanka mata mari taka'ara mata nabiyu, Abdul yarik'e hannun cikin masiba zainab tace" kaid'an akuya sake min hannu ke kuma wlhy nan bada dad'ewaba zakiyi nadamar abinda kika aikata,, kuma saikinyi mamakin mijin da safiyya zata aura maci amana kawai.
Fareeda ta tab'e baki wannan kuma bai dameniba,, idan safiyya zata auri mazan duniya bai dameniba tunda nidai nasamu muradina,, taja hannun Abdul suka tafi,, mahaifin fareeda ya yanke jiki yafad'i agurin......................โœ๐Ÿป

๐Ÿ’•Bily๐Ÿ’•
๐Ÿ’•๐Ÿ’•Mrs Abdus'salam๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•
๐Ÿ’•I LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’•๐Ÿ’•
๐Ÿ’•
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 13~October ~2016

๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA๐Ÿ”น๐Ÿ”ท

NA BILKISA IBRAHIM ๐Ÿ’•

๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ1โƒฃ3โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.............gaba d'aya suka nufo kan baba,, uncle kabeer ne yay k'ok'arin yayyafa masa ruwa ya kawo numfashi,, yad'ago yana kallonsu dagaske fareeda tatafi ta zab'i yaron nan sama dani??
Aunty zainab tace" baba ta tafi kabarta kawai aii "DUNIYA MAKARANTA CE"" yace" shikenan ku shaida nacire fareeda acikin 'ya'yana kuma duk wanda yay mu'amulla da ita acikin ku ban yafe masaba,, kamar yanda ta buk'ata nabarta da Abdullahi.
Baban safiyya yace" dan ALLAH malam d'ahiru kabar wannan furicin da fareeda da safiyya duk d'ayane agurinmu,, in akayi hak'uri itama safiyyan ALLAH zaibata wani, dama can ALLAH ya rubuta ABDULLAHI mijin fareedane ba safiyyaba......baban fareeda ya k'atseshi malam ibrahim kabarni kawai wlhy nariga na yanke hukunci dan haka kabarni ina ganin mutuncinka.
Dole kowa yay shiru,, dan sunsan ransa ab'ace yake,, daga nanma kowa yakama gabansa.

Agidan su sopy uncle kabeer yace" wlhy ni abunma ganinsa nake tamkar a mafarki,, dama akwai iyaye irinna Abdul??
Baban fareeda yay murmushi abba akwaima wad'anda suka fisu,, ni tun ranar da aka kawo kud'in auren fareeda na fahimci ko mai,, dan haka daga baya na yi bincike,, nagano Abdullahi fareeda zata aura.
aunty Nafisa tace" amma baba kayi shiru baka fad'awa kowaba??
Baba yace" hakane Nafisa fad'ar fashida wani amfani, tunda fareedar yakeson aure, dan haka ina mai gargad'inku kada kowa yad'auki wannan abin da zafi,, mutaya safiyya addu'ar samun lfy kawai, dakuma fatan ALLAH yabata miji nagari wanda yafi Abdullahi bawai dukiya nake nufiba,, A'a wanda yafishi k'yawawan halaye.

Kowa ya amsa da to,, yace" kukuma yakamata kushirya kutafi gida jenku,, tunda sunce yau zasu sallamo safiyyar daga asibiti.
"Suka amsa da to baba"

Da daddare aka sallamo safiyya, koda sukazo gida wanka kawai tayi tasha shayi da magani ta kwanta, dan akwai maganin barci aciki,, baba yace mai sunan baba!! miye likita yace gameda ciwon nata?? Uncle kabeer yaja numfashi,, yaya!! likita yace sopy tasamu matsala a zuciyarta,, dan tadad'e acikin damuwa da yawan fad'uwar gaba,, saikuma fad'uwar datayi shekaran jiya tayitane sakamakon jin abinda bata zataba,, amma yace" idan aka cigaba da lallashinta da yimata abinda zai sakata farinciki to zata dawo kamar yanda take,, inkuma bahakaba zuciyarta zata kamu sosai.
" inna tafashe da kuka,, ALLAH sarki safiyya kekuma taki jarabawar kenan?? Baba yace" hajara ba kuka zamuyiba addu'a safiyya kawai take buk'ata daga garemu.
Uncle kabeer yace"gsky ne wannan, nan dai suka cigaba da tattauna matsalar.

Yau da gobe ahankali jikin safiyya yafara sauk'i dan tana samun kulawa wajen baba da inna dakuma uncle kabeer,, yayyen tama suna bata kulawa,, haka mamar fareeda kullum saita shigo dubata itada baban dasu yaya lawan,, jikinta yana yin k'yau saidai yanzu bata son yawan magana,, ko hayaniya, ko fira ake akusada ita saidai kallo,, koda yaushe tana kwance, sallah ce kawai ketashinta abincima bata son ci,, sai uncle kabeer ya lallab'ata.
" lokuta da dama idan ta tuna cin amanar da AMINIYARTA tayi mata da SAURAYINTA wanda take matuk'ar SO sai kaga hawaye nazuba akumatunta,, takanyi bak'in cikin kub'ucewar mutane biyu masu muhimmanci agareta alokaci d'aya,, sun barta alokacin datake buk'atarsu fiye da kowa,, sun tafi lokacin datake buk'atar abokin shawara,, sun barta lokacin datake buk'atar mai d'ebe mata kewa,, sunyi nisa da ita alokacin datake buk'atar mai share mata hawaye,, tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi๐Ÿ˜ญ, nima bansan lokacin danawa hawayen suka fara zaryaba, dan nasan zafin rabuwa da masoyi,, saidai nawa mutuwace tarabamu, bakamar na safiyyaba da yana raye yayi nisane da'ita saka makon makircin AMINIYARTA.
inna tashigo d'akin da sauri danjin kukan safiyya,, ta rungumeta ajikinta tana lallashinta,, haba safiyya kiyarda da k'addara mana alokacin data riskeki,, ki godema ALLAH mana alokacin daya jarabceki,, karki jahilci kanki kiyi hak'uri irin hak'urin manyan ANNABAWA mana ayayinda jarabawa ta riskesu,, inkikai hak'uri sai ALLAH yayi alfahari dake domin yana tare damasu hakuri,, indan kikayi hak'uri sai ALLAH ya musanya miki da mafi alkairi.
Sopy ta kuma rungume inna tana fad'in to inna zan daina,, kawai abinne yana bani mamaki,, wai fareeda da'ita aka had'a baki wajen cin amanata,, dama tuni tasan dukkan matsalata amma tarufeni,, duk halin k'unci da yawan damuwa dana shiga fareeda tanada masaniya akai,, shiyyasa kullum saitace zataje ta tanbayo miyasa Abdul yadaina zuwa wajena,, kullum da irin tsarin da zata yi min,,, ashe itace kecin dunduniyata ban saniba,, ashe fareedace tushen damuwata tafad'a tana rushewa da kuka,, haba AMINIYATA miyasa kika aikata?? Miyasa kika yimin haka?? Miyasa kika zama mai irin halin muna fukai??? Miyasa saida nayarda dake kikaci amanata??? Miyasa kika zab'i mu rabu akan saurayi????
Inna tace" kinga ya isa haka kiyi hak'uri. Sopy ta d'ago tana kallon inna, wlhy inna ba rabuwa da Abdul bane matsalata nafi jin ciwon rabuwa da fareeda,, domin zuciyata da ruhina suna matuk'ar k'aunar fareeda,, itace K'AWA tafarko da zuciyata ta yarda ta ita harta zama AMINIYA mafi soyuwa a zuciyata,, ashe zata rabuda ni akan saurayi,, zata raba tsantsar SO da k'auna da zumincin dake tsakaninmu,, ashe zata saka shakku da fargaba azukata guda biyu da tsantsar yarda ta cikasu?? Ashe duk so da k'aunar dana nunama Abdul da fareeda su babu abinda suka ajiye mini sai tari yaudara da cin amana??? Nikam nayi asarar AMINIYA da miji mafi soyuwa azuciyata,, inna banyi tunanin sake maye gurbin wad'annan mutanen biyuba arayuwata,, domin nayi asarsu alokacin danafi buk'atarsu.
Inna tace" kiyi hak'uri safiyya ki barma ALLAH shine mai kowa da komai,, inkinyi hak'uri zai musanya miki da wad'anda suka fisu,, kedai ki kasance mai gsky aduk inda kika tsinci kanki,, da ace kekika cutar gara ace ke aka cutar kinjiko???
Sopy tad'aga kai tana hawaye, insha ALLAHU inna karkiyi shakku akaina,, zan kasance kamar yanda kika buk'ata.
To shikenan yanzu dai ki kwantar da hankalinki kibar yawan damuwa kinga likita yahanki tunani saboda ciwonki,, muma bamu son mu rasaki.
" to inna zanyi k'ok'ari insha ALLAHU kodan hankalinku ya kwanta.
Inna tayi murmushi to shikenan auta ta.
Sopy tace" inna ina uncle yake??
Yaje siyo miki maganinki yanzu zai dawo,, wlhy inna bana son uncle yatafi yanzu dan ina jin dad'in zama dashi.
To aiko saidai hak'uri auta kinga dole ya koma wajen aikinsa,, dan kinga bikinsa shima yanata gaba towa.
Sopy tace" hakane kuma inna, ALLAH dai yakaimu lokacin.
Inna tamik'e tana fad'in amin autata.................โœ๐Ÿป

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.