Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 40

Abdul yakalli agogon hannunsa gimbiyata yakamata ki wuce dan zaki makara karkisha bulalar makarafa.
Sopy tad'an murmusa gskyar ka habibina dan yasayyadi yananan abakin get, bari nawuce kasan idan ina tare dakai nakan manta kowa da komai.
" nima haka gimbiyata Abdul yafad"a yana kashe mata ido d'aya,,, Adam yace" kuna sha aninku masoyan zamani,, itakam fareeda tayi kicin kichin da rai kamar zata fasa ihu,, sopy ta tab'ata sister barina wuce saina dawo ALLAH yak'ara sauk'i.
"Amin tafad'a ranta a dagule"
Abdul yace" aii barima mu kaita k'yamis aduba miki ita.
Yawwa habibina nakwa gode maka,, bari nawuce sai da daddare mun had'u.
"To shikenan ALLAH ya kaimu my lovely wife.

Abdul yadawo da kallonsa kan fareeda bayan b'acewar sopy,, fareeda tad'anja k'aramin tsaki mara sauti,, Abdul yay saurin fad'in lfy?? Fareeda taid'an yak'e wlhy jinai kaina ya sara.
Okey sorry to muje ko??
Adam yace" aii ni inaga anan zamu rabu, dan wlhy abba ya aikeni amma sai yanzu natuna, kuje da daddare zamu had'u insha ALLAH fareeda ALLAH yak'ara sauk'i,, saida daddare idan munzo tad'i.
To Adam nagode ALLAH yakaimu daren.
""Amin adam yafad'a,, sukai sallama yatafi suma suka tafi.

Tafiya suke cikin nutsuwa kowa da irin tunanin dayakeyi azuciyarsa, har suka isa k'yamis d'in sadiq amma k'yamis d'in arufe.
Abdul yace" inaga saimunje k'amis d'in Rufa'i fa,, kozaki iya??
Tai murmushi babu damuwa muje nida nake neman lfy.
Shima murmushin yayi,, to shikenan muje.
" sun isa k'yamis d'in Rufa'i aka bama fareeda magun guna,, Abdul yabiya suka fito,, saida sukaje bakin titi fareeda tace" Abdul idan bazaka damuba inason muyi wata magana.
"Abdul ya kalleta to ina saurarenki,,fad'a min.
A'a maganar bata tsaye bace,, indai ban takuraka ba musami gurin zama.
Abdul yace" to inaga kibari saida daddare idan nazo saimu zauna muyi maganar mu uku harda Sopy, inaga hakan zaifi ko???
"Fareeda ta had'iye wani kududun bak'in ciki daya tsaya mata a mak'oshi,, jikake k'uuuuuttt!!!
Abdul yace hakan yayi ko?? Fareeda ta girgiza kai,, Alamar A'a,, tacigaba da fad'in mubiyu nakeson muyi maganar dan banaso Sopy tasani,, kasaka mana lokaci muhad'u nida kai kaiwai.
Abdul yay shiru yana tunani, saikuma yaja numfashi, to amma miyasa baki son Sopy tasani?? Fareeda tayi d'an murmushi, babu komai wlhy amma bana son tasani saimun kammala komai sannan, inason nabata mamakine.
Abdul yay dariya to shikenan babu damuwa,, saimu bari zuwa kamar weekend ko???
Babu damuwa indai hakan yayi maka ni agareni babu matsala.
"" to amma kina ganin tayaya zamu kasance tare dake batareda sopy tasaniba?? Kinsan koda yaushe kuna tare.
Indai wannan ne babu matsala nasan yanda zan kauce mata.
To shikenan Abdul yafad'a yana kallon fareeda,, har gida yarakota sannan yajuya,, amma zuciyarsa tana tunanin mi fareeda keson fad'a masa wanda batason safiyya tasani ??? Hakadai yayta tunani har yak'arasa majalissarsu inda suke zama da abokansa da yamma bayan kowa yadawo aiki ko kasuwa.
To masu karatu kubiyo danjin mi fareeda zata fad'awa Abdul ne??? Shin idan ta fad'a masa zaya amince????? Kubiyo ni danjin amsar tan bayoyinku. .................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕
5~October ~2016

🔷🔹NI DA K'AWATA 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💕

🔶🔸5⃣🔸🔶

...................fareeda tafito cikin sharin fita, mama tabita da kallo kekuma ina zakije da yamman nan???
Mama dan ALLAH kibarni naje gidan aunty sadiya gobe in ALLAH yakaimu da safe saina dawo tunda babu makaranta.
Mama ta harareta kinga fareeda kifita idanuna tunkafin na b'ata miki rai,, yaufa kwananki uku da zuwa gidan sadiyar shine yaukuma kice zaki koma,, to waima mizakije yine??
: : fareeda ta turo baki gaba nifa sak'o zan amso awajenta.
Sak'o kuma??? To sak'on mi?? Kuma waye yabada sak'o abaki??
Fareeda tayi shiru dan batasan abinda zata fad'awa mama tabarta zuwaba,, saikawai tacire gyalen ta ajiye saman igiyar shanya,, tana fad'in tunda dai kin hana shikenan.
Mama tai tsaki ke dai kika sani.

Sopy kwance atsakar gida jikin wata 'yar bishiyar mangwaro dake tsakar gidansu,, hannunta rik'e da littafin English tana dubawa, dan exam tana gabatosu,, inna dake zirga zirga a tsakar gida dan k"ok'arin had'a abincin dare, ta kalli sopy safiyya ki tashi ki share tsakar gidannan kar magriba tayifa kina ganin rana tafara jaa.
To inna safiyya tafad'a tana mik'ewa, ta nannad'e tabarmar tafara sharar tsakar gidan,, tana cikin sharar malam ibrahim yay sallama da gudu sopy taje ta taryoshi,, baba sannu dazuwa.
Yauwa safiyan baba,, ya gidan?? Wlhy baba kafiya lao, to madalla.
Ta karb'i ledan hannunsa tana fad'in baba mika sayomin???
Yay dariya safiya way sai yaushe zakibar kwad'ayine kinfa girma,, inna tafito kichin tana masa sannu ya amsa cikin fara'a,, yaja kujera 'yar tsugunno yazauna,, inna takawo masa ruwansha.
Sopy tagama shara ta wanke hannunta, sannan tanufo babanta, baba tunda kaki fad'a min nibari naduba dakaina,, baba yay dariya to duba 'yar baba kankanace nasiyo miki saboda nasanki da son kankana,, ta d'auki ledar tana fad'in nagode babana mai sona.
Inna tace" malam ita kad'ai kasayoma kankarar Kenan? ?? Safiyya tace kai inna kina kishine???
Inna taimata 🖐🏻dak'uwa kinci gidanku nicema nake kishin dake ???
Malam ya mik'e yana musu dariya,, yad'au buta yayi alwala, ita kuma Sopy tazauna gyara kankana, dan tana fashin sallah.

Suna zaune atsakar gida suna cin abinci,, sopy tana gefe tana shan kankana,, inna tace" ni ina tawa kankanar?? Sopy tamik'e tana fad'in wlhy baba idan banbama inna kankanar nanba bazata barni nasha iskaba.
" inna tarik'e baki wayni yaushe safiyya ta rainani agidannan ne malam??? Malam ibrahim ya murmusa bawani raini,, aii ko kurama da 'ya'yanta take wasa a dawa,, itama tana tsokanarkine kaway.
Inna tace" kaidai kana goya mata baya ne kaway,, safiyya tai dariya baba kabarta ai kwanannan zan tafiyata gidan aunty Nafisa hutu saita dad'e bata ganniba,, damma uncle kabeer bashida mata da gidansa zan koma.........yaron dayay sallama yasa sopy yin shiru.
"" kai shamsu lfy ??sopy ta tanbaya,, shamsu yace wanine yace kizo awaje,, wani kuma?? Waye wani?? bashida suna ne??? Shamsu yace nibansan sunansaba amma agidan Alhaji Abubakar mai fata yake.
Baba yace"kaga yaro yitafiyar ka,, gata nan zuwa.
Sopy ta turo baki wlhy nikam baba banason fita tad'innan yau,, baba yace"" tobake kika zab'i mijinkiba da kanki maza tashi kije,, amma kar a zauna wannan doguwar hirar,, tun ana fad'ar gsky har akoma k'arya.
Sopy tace"to baba bari nak'are shan kankanata.
A'a tashikije idan kin dawo saikisha.
Dole tamik'e tatafi badan tasoba.

Inna ta kalli baba,, malam wlhy nidai dan kawai safiyya tanason yaron nan amma nikam bai kwanta min araiba,, banaso akai safiyya gidan nan mai tarin mata da 'ya'ya.
Baba yaja ajiyar zuciya,, hajara babu abinda zamu iyayi face addu'a,, dan neman zab'in ALLAH, ALLAH yazab'a mana abinda yafi alkairi.
"To amin malam"

Awaje kuwa sopy tana fita saita tararda Abdul tare da fareeda suna hira,, lamarin yayi matuk'ar bawa sopy mamaki,, amma saita danne tak'arada wajensu da sallama.
Atare suka amsa mata,, takalli fareeda,, ke sister amma ke 'yar rainin hankalice yanzu nan dama baki tafiba???? Fareeda tace" kibari kawai 'yar uwa wlhy mamace ta kwafsa min tahanani zuwa,, fushi nakeyi shiyyasa kikaga ban shigoba,, yanzuma nazo na ari wayan Abdul ne nakira aunty sadiya nafad'a mata abinda yahanani zuwa.

Sopy taja ajiyar zuciya mai k'arfi,, Abdul yay saurin kallonta gimbiyata miye matsalarki???? Babu komai habibina ykk?? Lfy lau nake gimbiyata.
Nan dai suka dasa hira harda fareeda,, dan tak'i tafiya.
Hakan baisa sopy ta zargi komai ba, dan zuciyarta a tsarkake take,, ta yarda da fareeda da Abdul, d'ari bisa d'ari.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.