Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 40
Ya k'arasa office d'insa amma saiyayi turus ak'ofa domin ganin kairat zaune, ya had'e rai ya ce, "lafiya dai??
Kairat tad'ago tana kallonsa, lafiyarce takawo hakan.
Yakuma tamke fuska ya ce, "miya kawoki office d'ina nace??.
Yanda yayi maganar cikin tsawa saita tsorata, dan tasan baya son wargi, cikin rawar murya ta ce, "dama nazo nasanar dakai dadyna zai maidani karatu AMERICA.
Uncle G! Ya tab'e baki, lallai yayi dabara, to ALLAH ya taimaka, zaki iya tafiya.
Kairat ta kalleshi cikin matuk'ar bak'in ciki, dan ganin yanda yake korarta, ta daure ta ce, "to ya maganarmu dan inaso nasan matsayina agurinka!!.
Saida yay mata kallon sama da k'asa sannan ya ce, "bakida wani matsayi agurina kamar yanda nasanar dake, sai dai ina miki fatan alkairi a rayuwarki", ya nuna mata k'ofa akaro na biyu, zaki iya tafiya dan inada abinyi.
Wani bak'in cikine ya tokare mak'oshin kairat, tai waje cikin bak'in ciki, dan idan tayi magana kuka zai iya zuwa mata.
Uncle G! Yaja tsaki, yana fad'in 'yar wahala, indai so nane kin d'akko abinda yafi k'arfinki, domin tuni wata ta karb'e zuciya ta, useless! Kawai.
Kairat d'iyar wani mai kud'ice, tunda aka kawota makarantar nana ta k'yalla ido akan uncle G! Taji takamu da sonsa mai tsanani, sai dai shid'in batai masaba, yafison ya auri d'iyar talakawa irinsa.....................âœðŸ»
💞bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 25~October~2016
🔷 🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸2⃣5⃣🔸🔶
............Safiyya! kam tunda uncle G! Yafita tashiga aji tazauna zuciyarta cike da tunani iri iri, koda zaliha! ta zauna kusada ita tana mata surutun data saba bata kulataba, saima ta d'akko wayarta tana catin da uncle kabeer.
Wani sak'o yashigo amma saitayi burus dashi, dan azatonta wanine ya d'auki nomber d'inta a group dan haka wasu keyi, musamman ma samari.
Shigowar wani malami yasa ta daina catin d'in, tanatsu domin d'aukar lecture.
Bayan fitarsa batada wata lecture sai k'arfe uku, dan haka tanufi library domin wani bincike.
Ta shak'i wani k'amshi wanda tabbas tasan mai shi, amma saita share tacigaba da karatunta, jin k'amshin ya yawaita agurin yasata juyowa domin tabbatar da zarginta.
Uncle G! Ne tsaye yana binciken wasu books saidai da alama bai gantaba, dan haka tak'ara k'asa da kai, bata buk'atar yaganta.
sai dai ta makaro, domin kuwa tunda ya shigo da ita yafara tozali, ya basar ne kawai yanuna bai gantaba.
Cikin takunsa na masu aji da gayu yanufo inda take zaune, hannu biyu yasa yadafe tebir d'in gabanta, tareda fad'in Assalamu alaiki?.
Da sauri tad'ago dan batai tsammanin zuwansa ba.
Ya ce, "bakijin sallama ??.
Cikin rawar murya ta amsa, ta d'ora da gaisheshi.
Yaja kujera ya zauna yana fad'in ya ykk?
Sopy taja numfashi tana fad'in lfy law.
Ya ce, "good".
Kafin yayi magana wayarsa ta hau k'ara alamun kira, ya cirota daga aljihun gaban rigarsa ya amsa.
Saida yagama wayarsa sannan yadawo da dubansa gareta, yayinda wasu d'alibai dake library d'in suke kallonsu.
Ya mik'e yana fad'in kisameni a office inaso muyi wata magana dake, domin inaso naje gida wannan week d'in akan maganar aurenmu!!.
Da sauri ta kalleshi, shima kallonta yakeyi, dan haka ta maida kanta k'asa, ya kwashi wasu takardunta data ajiye, ta daure ta ce, "uncle zanshiga lecture dasune fa.
Yatafi yana fad'in nasani idan kinzo saiki karb'a ina jiranki karki b'ata min lokaci.
Sopy ta dafe kai tana fad'in nashiga uku ni safiyya mutumin nan fa yafara shiga min hanci, yakamata na face shi, kanta ta maida ga karatu amma saita kasa karatun dole ta mik'e tafice, tadad'e tana tunanin zuwa office d'insa, dan gsky bataso azargeta akan yawan shiga office d'insa.
Wayarta ta hau wringing, tad'aga tana mita.
Muryar uncle G! Taji yana fad'in ina jiranki fa!!.
Kafin ta ce, "wani abu ya yanke wayar, ta dafe kai tana fad'in ya salam, dole ta daure ta nufi office d'in.
Ta kwankwasa, ya ce, "shigo mana, dan yasan ita ce!!.
Da sallama tashiga kanta ak'asa, yad'ago yana kallonta batareda ya ce komaiba.
Jin yayi shiru, ta ce, "gani!!."
Ya ce, "aii naganki, ya maida kansa kan abinda yakeyi.
Sopy tabishi da kallo cikin takaici, takardunta yake dubawa, taja k'aramin tsaki amma baiji ba, a zuciyarta ta ce, "kaidai kana son sakani cikin matsala, banason wani yazargeni wlhy.
Ya d'ago yana fad'in wai bazaki zaunaba ne??.
Ta ce, "nanma ya isa.
Ya ce, "okey nima bari nataso tunda yau tsayuwar kike sha'awa.
Kafin ta ce wani abu yataso, ya k'araso inda take tsaye, jingina yayi ajikin bango ya hard'e hannayen sa a k'irji, ya dasa mata fararen idanunsa manya masu yalwar gashi.
Ta k'ara k'asa da kanta dan ganin irin kallon k'urullar dayake mata, ya murmusa dan ganin yanda taketa sinne kai kamar wadda tayi k'arya, ya gyara tsayuwarsa, sopy!! Wai sai yaushe zaki kalli cikin idanuna ne, kunyarki tayi yawa fa.
Hannu tasa ta rufe fuskarta.
Yay dariya tareda fad'in okey to shikenan, dama inason nasar dake jiya da daddare naje gidanku!!.
Ta zaro idanu, gidanmu kuma??
Ya jin jina kai, e, gidanku, aii dama na ce, "miki bada wasa nazoba, yacigaba da fad'in, munyi magana da baba, nasar dashi komai nida kabeer, yakuma karb'eni fiye da zatona, yanzu haka yabani izinin turo iyayena! Sai dai ya ce, "bikinmu zaikai nanda watanni dan yanzu suna shirin bikin kabeer, amma bayan bikin kabeer da wata uku zuwa hud'u sai ayi namu.
Sopy ta zame ta zauna a k'asa, bayanta jingine da k'ofa.
Ya bita da kallon mamaki, ya daure ya ce, "yaya dai? Ko hakan bai mikibane??.
Ta d'an kalleshi, ta girgiza kai.
Ya ce, "to miye matsalarki??.
Ta ce, "babu, ta cigaba da fad'in nasan iyayena bazasu cutar daniba, dan haka na amince da duk abinda suka yanke, kuma zan yimusu biyayya.
Uncle G! Yaja ajiyar zuciya yana fad'in ALHAMDULILLAH!!, ya tsugnna a gabanta, ya ce, "karki damu safiyya!, kabeer ya sanar dani abinda yafaru dake a baya, tsakaninki da AMINIYARKI da kuma SAURAYINKI, to inaso ki manta da abunda yafaru a baya, ki gogeshi a arayuwarki, kid'auka yanzu zaki sake sabuwar rayuwane, ki yarda ni ne!! Zab'in alkairin da ALLAH yay miki, zan baki mamaki insha ALLAHU, Zan rik'e amanar da baba yabani taki kinji.
Yaja numfashi, gobe idan ALLAH yakaimu kabeer zaizo, zai sanar dake sauran bayani, ni kuma jibi idan ALLAH ya kaimu zanje nasanar da iyayena, ya mik'a mata farin hankici daketa tashin k'amshi, karb'i ki goge hawayenki dan banason su zuba k'asa.
Sopy ta karb'a dan ita bama tasan tana kukaba, saidai batasan kukan na miyeba?? Farinciki ko bak'incikin rabuwa da Abdul, tasan tabbas uncle G! Yafi Abdul komai kyau, ilimi, aji, da sauran abubuwa masu yawan gske, kud'i kawai mahaifin Abdul zai nunawa uncle G!, itakam bata d'auki kud'i wani abu mai muhimmanciba arayuwarta, dan itama talakace tib'is, tanada tabbacin samun nutsuwa a gidan talaka d'an uwanta.
Jitai uncle G! Yana fad'in to kukan ya isa haka, inko bahakaba zan lashe hawayen dasuka sake zubowa.
Hannu tasa tasa tarufe fuska tana dariya.
Shima dariyar yayi, "wai yau miyasaki makara ne??
Cikin sanyin murya ta ce, "karatun tarihinka mana.
Ya ce, "nice, hakan yayi nasan yanzu kinsan ni kowaye, ni talakane tib'is, sai dai rufin asirin ALLAH kawai, ina fata wannan bazai shafi auren muba ko??, Dan kinji wayeni dakuma inda nafito, kinji su waye family nawa, zaki iya neman k'arin bayani a wajen kabeer, dan yasan komai a kaina.
Tai murmushi to aii nima talakace, nasan kuma kasani, tunda kana tareda uncle kabeer.
Yad'an murmusa yana fad'in to shikenan ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, amma daga yau idan kika k'ara makara a lecture d'ina tofa bayan horon hana shiga aji, akwai horo tsakanina dake, dan haka ki kiyaye, yafad'a yana mik'ewa.
Itama ta tashi tsaye, to bari na tafi.
Kai habadai tun yanzu, nifa ban gaji da ganinkiba!!.
Hannu tasa ta rufe fuska ta ce, "aii munkusa shiga lecture ne.
Yay dariya to sarkin kunya, ga kayanki can jeki d'auka.
Ahankali ta nufi tebir d'in sa, ta tattara takardunta ta kwaso zata juyo wayarsa ta hau wringing, ya ce, "taho min da phone d'ina!.
Saida ta d'an rissina sannan tabashi tay waje da sauri, dan batason yasake tsayar da ita.
Yay murmushi, yana binta da kallo...............[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 26~October~2016
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.