Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 22 of 40
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 2~November~ 2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸3⃣5⃣🔸🔶
.........WASHE GARI suka tashi da shirin tfy, uncle G! Yana kula da sopy bata son a tafi.
Nasiha sosai baba da gwaggo sukai musu, dan sunce sopyma tazama d'aya daga cikin 'ya'yansu.
" Haka yakamata surukai su rink'a d'aukar matan 'ya'yansu, bawai ki zauna kina kishi da matar d'ankiba, wannan ba dai dai bane, idan kika d'auketa d'iyarkima wlhy saitafi girmamaki da baki daraja, amma daga lokacin dakika fara kishi da ita, tofa rainine zai shiga tsakaninku, shima d'an naki yazo yana jin haushinki a baza awofi, ALLAH yasa mugane".
Sai bayan sallar azahar suka tafi sopy harda kuka, shi dariya ma take bashi, har sukazo tsanyawa tana kuka, daya kula idan ya k'yaleta ba bari zatayiba, sai ya fara janta da hira, tun tana amsawa ciki ciki harta ware tana kallon hanya da garuruwa, ya tsaya a bichi suka sha mai, sannan suka cigaba da tfy, ta ce, "to nan wane garine?, ya ce, "bichi kenan indai kinji ana fad'in bichi to itace wannan, A'a ni yauma natab'a jin sunan garin, yay murmushi kawai batareda ya ce komaiba.
Gab da la'asar suka shiga cikin kano, ya ce, "yanzu ina kikeso mu fara zuwa? Kona kaiki ki gaida su inna?.
Da sauri ta ce, "e, muje gidan su inna.
Yad'an murmusa batare da ya ce komaiba.
Ganin sun wuce titin layinsu ta ce, "munfa wuce uncle koka manta ne?, yad'an kalleta sannan ya maida kallonsa bida titi, na canja shawara ne aii.
Saboda mi? Sopy ta tanbaya.
Ya dafe sitiyari da hannu biyu saboda naga kamar bai daceba ne, sun kaiki gidan miji kuma kin zo musu yanda suka kaiki, yakamata a samu canji.
ALLAH sarki Sopy ita kam bata fahimci inda ya dosaba, amma ta lura kamar da wata fassara yay maganar, daga nan tayi shiru bata sake maganaba, shima dai bai kuma cewa komaiba, har suka isa anguwarsu.
Gidan ma daidaicine, ginin talaka mai wadatar zuci, da kansa yafita ya bud'e get d'in sannan suka shiga, inda motar ta tsaya nanne kawai fili, daga ita kuwa babu abinda zai k'ara shiga koda mashin ne, suka fito ya ce, "Safiyya ga gidanki to.
Sopy tayi 'yar dariya ta ce, "naganshi kuma yayi k'yau.
Shima ma dariyar yayi yana bud'e but d'in motar ya sauke kayan duka, ya d'auki wasu yana fad'in namanta kefa makauniyace sai nayi miki jagora a gidan naki, itama d'auka tayi tabishi, yasa mukulli ya bud'e k'ofar falon, wani k'amshi ya daki hancinsu, suka ajiye kayan, ya ce, "zauna na k'arasa d'akkowa.
Sopy tabi falon da kallo tana jinjina kai, lallai iyayenta sunyi k'ok'ari, falon yayi k'yau, komai acikinsa jaa da farine, kujerune set guda sai santa rok (center rug) atsakkiya kujerun shima jaa anmasa kwalliya da fararen fula woyi, sai tebir a tsakkiyarsa shima dai tare suke da kujerun, falon zagaye yake da labulaye suma jaa da fari, sai tv sitan shima irin kujerun an d'ora filasma k'arama akai ta dai dai talaka.
Takai dubanta a dani (dinning) shima ank'awatashi da kujeru da firij, idan bata mantaba ta dad'e da ganin kujerun dani d'innan a gidan aunty Nafisa an lillib'esu da wani k'yalle ashe natane, hawaye suka gangaro a kumatunta na dad'i, bata san da bakin da zata godema iyayentaba da yayyenta musamman ma uncle kabeer dan yafi kowa taka rawar gani acikin rayuwarta, dama yayyenta sunsha gaya mata saboda aurenta suke sana'a tabbas yau ta shaida haka.
Uncle G! ya kamata ya zaunar saman kujera, dan tun d'azu yana kallonta, yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta, ya ce, "Safiyya ba kuka zakiyi ba addu'a yakamata kiyima 'yan uwanki domin sun taka rawar gani a kanki, ko mak'iyi yaga kayannan saiya jin jina musa, hannunta yakama yanufi kichin da'ita aii sai sukaga abin kallo yana kichin, lallai kicin d'innan ya tsaru nanama komai jaa aka tsara, ya ce, "ga sito d'inki ya nuna mata wata 'yar k'ofa, koda yake zomuje ki gani, suna bud'ewa kayan abinci suka bayyana uncle G! yasaki baki yana kallon ikon ALLAH harda su drinks yasan wannan tabas aikin uncle kabeer ne, uncle G ya rungume sopy cikin farinciki, ya ce sopy narasa bakin maga wlhy saidai muyita yima su baba addu'ar gamawa lfy, zomuje ki ida ganin ko ina.
Bedroom d'inta ya kai ta, sannan sukaje nasa nanma ya had'u saidai nasa komai ruwan ganyene (green) kenan, ya zaunar da ita a bakin gadoyana fad'in Safiyya kinga gidanki sai dai k'aramine dan na talakane, a hakama nakai tsawon shekara hud'u ina ginashi, dan cikin albashi ake cire wani abu ad'anyi aikin, amma mun godema ALLAH da baiwar da yayamana ta rai da lfy, ahakama munfi wasu, ina fata zakizo mu had'a kai mu zauna kfy, mukuma yarda da k'addara aduk lokacin data riskemu, muyi hak'uri a lokacin da babu ta waywayemu, muzama masu wadatar zuci akan abinda ALLAH ya azurtamu dashi, mukuma gode masa.
Arzik'i bashine rayuwa ba dan da wani arzik'in gara dawwama a talauci, nayi alk'awarin zan rik'eki amana, sannan ina rok'onki damuyi hak'uri da juna a yayin da muka samu sab'ani, mukuma fahimci juna alokacin da wani abu yashige mana duhu, na tabbata wannan zai taimaka mana wajen zaman aure.
Sopy ta ce, "insha ALLAHU zaka sameni mai biyayya a gareka.
Ya ce, "ALHAMDULILLAH.
yanzu tashi muje na rakaki d'akinki kid'an watsa ruwa ko?.
Ta ce, "to......................âœðŸ»
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 3~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣6⃣🔸🔶
.........Har d'akinta yarakata, bayan fitarsa takuma k'arewa d'akin kallo, sannan tashiga wanka, tai murmushi dan ganin jininta yazo, lallai tayi farinci da faruwar hakan, tayi wanka tafito sai dai matsalarta d'aya batada always to yaya kenan zatayi?, tasan daga nan zuwa dare dole ta nemi mafita, inko ba hakaba zai rink'a b'ata mata jikine, tana nan zaune tana sak'a wasik'ar jakai saitaji sallama, ta fito da sauri tana amsawa, saitaga wata 'yar matsakaiciyar budurwace hannunta rik'e da kwando.
"Yarinyar ta gaidata."
"Ta amsa cikin sakin fuska".
Yarinyar ta mik'o mata kwandon dake d'auke da kuloli ta ce, "gashi inji aunty Asiya.
Sopy ta ce, "aunty Asiya kuma?, wace aunty Asiya nasani anan anguwar?.
Uncle G yafito sanye da jallabiya fara, yarinyar ta gaidashi, saida ya amsa sannan ya ce, "Asiya matar kabeer fa, aii bamuda nisa gidansu na nan k'asanmu.
"Lah aii ban saniba".
Ya ce, "na mantane nagaya miki, ni bari naje masallaci lokaci yana k'ara k'urewa, ta ce, "adawo lfy, yafita yana fad'in ALLAH yasa.
Yana fita Sopy ta Cema yarinyar ya sunanki?.
Ta ce, "sunana fatima amma anace mini ummy, nice name sopy tafad'a.
To ummy dan ALLAH ina zaki sayo mini always ?, ummy ta ce, "aii akwai shago nan bayanku kawo na siyo miki.
Yauwa ngd ummy 'yar albarka, taje ta d'akko mata d'ari biyar tabata ta fad'a mata irin wanda takeso.
Babu dad'ewa uncle G yadawo, sannan sopy tana kicin tana d'auraye inda zasuci abinci.
A falo yazauna ya kunna tv dan anhad'a komai, wannan duk aikin uncle kabeer ne, ummy tayi sallama ta shigo, ya ce, "O, baki tafiba?, ta ce, "e, aunty ce ta aikeni.
Okey to kawo, ta mik'a masa ledar da canji ta ce, "bari natafi zanje islamiyyane, ya ce, "to ki gaishesu kice mun gode sosai ya mik'a mata naira d'ari, ta ce, "A'a, ngd, ya ce, "karb'i aii ni nabaki, ta amsa tana godiya ta tafi.
Ya bud'e ledar dan son ganin minene aciki, ya ce, "tofa, abinda kuma yafaru kenan, ya ajiye yana fad'in an rusa mini show d'ina kenan.
Sopy tafito da kayan filet, ta dire a saman tebirin dake tsakkiyar falon ta ce, "ga abinci ko akai dinning?, ya sakko k'asa yana fad'in aii ak'asama zanci, dan nagaji dayawa, saida tafara zuba masa abinci ya ce, "af, nama manta yarinyar ta ce, "tawuce gama sak'onki".
Sopy ta ce, "to, ngd".
Tagama zuba masa farar shinkafar da miya da lemon kwakwa, sai salat.
ya ce, "kefa?, ta ce, "sai anjima, harararta yayi, ya ce, "sa hannu muci kikuma cire wannan hijjab d'in kisha iska.
Ganin ya d'an d'aure fuska, yasata bin umarninsa, ta cire hijjabin tazauna sunacin abincin, dukda tsakura takeyi kuma a kunyace takeci, bai kuma ce mata komaiba yacigaba da kallonsa yana cin abinci.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.