Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 30 of 40
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 19~November~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ4โฃ8โฃ๐ธ๐ถ
...........Akwana atashi babu wuya gurin ALLAH, yau satin Sopy d'aya da komawa makaranata, kullum takan tashi kamar yanda ta saba ta had'a musu break, idan tana da lectures d'in safe sai su tafi tareda uncle, idan kuma batada shi sai yatafi, daga baya ta bishi.
A b'angaren fareeda kuwa tana nan tana shirya abubuwa masu yawa akan uncle G! Dan kullum tana yaudarar zuciyarta akana wataran zata iya mallakarsa amatsayin miji, na ce, "lallai kina da aiki 'yammata.
Yauma sopy ita kad'ai ta girka abincin rana, dan fareeda ta tsiri barcin rana, Sopy bata damu da hakanba, dan dama bataso fareeda tana tayata akan aikin gidanta, tagama tsaf tagyara gidan, yau kam a d'akin uncle G! tayi wanka, tadawo d'akinta ta shirya.
Babu dad'ewa uncle G! yadawo, dan yad'an fita, ta taroshi kamar yanda tasaba, takawo masa ruwa yasha sannan tarakashi bayi yay wanka.
Falo suka fito domin cin abincin rana, ya ce, "wai ina fareeda ne?.
Sopy ta ce, "tana d'aki tana barci.
Ya jin jina kai, badai tun barcin dana fita nabarta tanayiba?.
Sopy ta ce, "wlhy tunshine.
Baice komaiba yaja kujera ya zauna, sopy tafara zuba masa abinci, fareeda ta fito kamar an jehota, tana wani murza idanu wai ita ta tashi daga barci.
Uncle G! ya ce, "lallai yau kinsha barci, ALLAH yasa dai lafiya??.
Fareeda tayi wani walay da idanu sannan ta ce, lafiya lau yaa youseef.
Yanda tayi maganar sai ya k'ona ma sopy rai, wani abu yazo ya tokare mak'oshinta, da sauri ta d'auki ruwa tasha, uncle G! ya bita da kallon mamaki ya ce, "sopy yadai??.
Ta girgiza kai alamar bakomai, ta tura masa filet d'in abinci gabansa.
Fareeda tayi wani d'an murmushin samun nasa, taja kula tana zuba abincin.
Laumar farko uncle G! ya had'e rai, yad'auki ruwa da sauri ya kora, ita dai sopy kallonsa kawai takeyi, ya ajiye cokalin ya dafe kai.
sopy ta daure ta ce, "uncle lafiya??, yad'ago idanu cikin matuk'ar b'acin rai, ya ce, "kici abincin kiji mana.
Jiki asanyaye sopy takai lomar abinci bakinta, wani irin aza babben yaji taji na fitar hankali, ko yarabawa dasuke shan yaji bazasu iya cin abincinba.
Sopy ta dafe kai danjin ya sara mata, cikin masifa uncle G! ya ce, "to yau kuma miye sanadi?, ranar mun d'auka a matsayin kus kure, yau kuma amatsayin mi kikeso mu d'auka, duk maitarmu bazamu iya cin wannan yajin ba, wannan wace irin rayuwace, aii da ba haka kike girkinba ko.
Sopy ta d'ago fuska shab'e2 da hawaye ta ce, "kayi hak'uri uncle G!, nidai nasan lafiya lau nayi girkina, wlhy bansan yanda akayi yajinnan yay yawa hakaba.
Uncle G! yaja tsaki, ya ce, "to mikike nufi?, ko kina nufin wanine yazuba miki yajin?, naga dai gidannan mu ukune kawai, a cikinmu waye zai zuba miki yaji a abinci? .
Gaban fareeda ya fad'i rass.
Sopy ta share hawaye, ta ce, "inma wani yake zubamin dan yahad'ani dakai tofa na barshi da ALLAH, tana kaiwa nan tatashi ta shige d'aki.
Suduka binta sukai da kallo, shima saiya tashi ya shige d'akinsa cikin b'acin rai.
Fareeda tayi 'yar dariya, tana fad'in 'yan rainin hankali kwadaiji dashi, tashi tayi tanufi d'akin sopy itama.
Sopy tana kwance kan gado tanata rusar kuka, fareeda tashigo ta zauna gefenta, cikin sanyin murya ta ce, "sopy kiyi hak'uri, haka rayuwar aure ta ke, wani lokacin ayi farinciki, wani lokacin kuma kuka, sopy ta d'ago idanunta dasukayi jajur tana kallon fareeda, fareeda ta jin jina mata kai tana fad'in sopy gsky nake gaya miki, kuma nasan kema zaki fahim ceni.
Batareda sopy tace komaiba ta maida kanta ta kwanta.
Fareeda ta watsa mata harara harda gwalo๐.
Har dare gidan babu dad'i, sopy kuma tak'i dafa komai, tak'i shiga d'akin uncle G!, shima dai tunda ya shiga bai fitoba, fareeda ce kawai take cikin walwala.
Sallar magribace ta fitarda uncle G! waje, saida akayi isha'i ya dawo, hannunsa rik'e da ledoji, fareeda ce kawai a falon, ya bata leda d'aya ya wuce da sauran d'akinsa, fareeda ta bud'e ledan tana wani murmun mugunta, namane ciki da kayan ciye2, tako bud'e tahau cin kayanta.
Har wajen k'arfe goma sopy tana d'aki tak'i fitowa, uncle G! dake kwance bisa gado yanata juye2, yad'anja tsaki, azuciyarsa ya ce, "wai dama haka matan suke kamar zuma, ga zak'i ga harbi, ya tashi zaune yana bin d'akin da kallo, yay d'an murmushi yayinda idanunsa suka kai akan hoton su shida sopy, sunyi matuk'ar k'yau, kowannensu yana murmushi, atake yaji zuciyarsa ta huce, ya mik'e tsam yanufi d'akin sopy, har yanzu fareeda tana falon tana kallo, kallo d'aya yay mata ya d'auke kai, ya tura k'ofar yashiga, sopy tana kwance tana jinsa.
Ya zauna kusada ita yana shafa fuskarta, itadai tana jinsa tayi shiru, ya duk'o da fuskarsa kusada tata har sunajin saukar numfashin juna, cikin taushin murya ya ce, "haba my sopy yau ba'ayi danine?.
Ta janye fuskarta daga kusada tasa, tana turo baki gaba๐ , ya kwanto ta bayanta, yana sassanyar dariya acikin kunnenta.
Jitai tsigar jikinta ta tashi yarrr, ya sumbaci gefen kuma tunta, ta d'ago da sauri tana kallonsa, saita murgud'a masa baki๐, yayi murmushi yana fad'in nikike murgud'awa baki?.
Tai masa shiru, sakkowa yayi daga gadon ya d'auketa cak, fareeda tayi saurin komawa saman kujera ta zauna, sopy kuwa sai watsal2 takeyi tana kukan shagwab'a wai ya sauketa bataso.
Ya ce, "aii saimunje d'aki kin fad'amin wanda kika murgud'awa baki.
Ta ce, "nifa bada kai nakeba, ya ce, "daga baya kenan.
Fareeda ta rakasu da harara tareda jan wani mugun tsaki, dan bahaka tasoba.๐๐
Uncle G! Ya jefa sopy saman gado, yay mata runfa da faffad'an k'irjinsa, bakinsa ya had'e da nata, yashiga nuna mata soyayya mai tsaftar gske, naja hannun hauwa'u, ina fad'in kinga zomuyi waje kafin uncle G ya koramu.
Ta ce, kai bilki ki tsaya mud'an k'ara gani mana, na zaro idanu waje ina fad'in ALLAH ya shiryaki hauwa'u, daga samun lafiyarki, ko kinaso uncle G! ya maidaki gadon asibitine?, kijama janu d'an kuka.
Sai da komai yalafa muka koma, tarar dasu mukai yana bata nama abaki suna ta hirarsu da dariya.
Hauwa'u ta ce, "lallai bilki mai shiga tsakanin miji da mata yana tareda kunya.
Na ce, "wlhy kuwa hauwa'u, hannunta naja muka nufi d'akin sopy dan mugano muku halin da fareeda take ciki.
Saman gado muka tarar da ita, tana faman jan tsaki, na jin jina kai ina fad'in lallai wannan bata gajiba, dan na kula wani abu take k'ara shiryawa.
Hauwa'u ta ce, " 'yar wahala, ni kinga mutafi muma wajan mazajenmu karmu lalace anan.
WASHE GARI
sopy ta had'a break tsaf, ta gara gidan, saidai yau na kula kamar akwai abinda take k'ullawa, dan sai murmushi takeyi, tana shiga wanka fareeda ta fito tanufi kichin d'in.
Sopy suka gama shirinsu tsaf da uncle G! suka fito sunata zabga k'amshi, fareeda dake zaune afalon tun d'azu ta gaida uncle G!, suka gaisa da sopy, sannan suka nufi dini domin cin abinci, farida kuma saita nufi d'aki waizata d'akko abu.
Sopy tagama had'ama uncle G! abinci ta tura gabansa, yako ja ya hauci, sopy tatattare kulolin datai amfani dasu tanufi kichin, nayi dariya, dan nakula sopy ta kwashe abincin sune itada uncle G! acikin wata kula daban, saita bar wani a d'ayar kular, tayi alamu kamar an d'iba.
Tana dawowa ta tarar fareeda tafito, sai dai, sai kallon uncle G! take dayake cin abincinsa cikin kwanciyar han kali harma yana lumshe idanu.
Taja kula itama tazu, ko kallon inda take sopy batayiba taja abincin ta ta hauci.
Fareeda dai saicin abinci take tana matse idanu, gashi babu damar magana, tunda masu gidan basuce komaiba, saima hirarsu sukeyi, sai dai zuciyarta sai tunani take akan ya akayi basuji d'anbanzan sukarin data zuba a aciki abincin ba.
Da haka suka gama, uncle G! yafita, sopy ma tatafi d'akinsa dan ta gyara, fareeda taja abincin da uncle G! yarage taci, saitaji lafiyarshi lau, tarike kugu๐ฏ tana fad'in wato matar nan boye musu abinci tayi kenan??.
Sopy dake lab'e tana kallonta tayi murmushi kawai.
Aka kwan kwasa k'ofa da sauri fareeda taje tabud'e azatonta uncle G! ne, amma saitaga su aunty Nafisa, da aunty hauwa'u, da aunty zainab yayarta, dakuma aunty Asiya matar uncle kabeer, cikin mamaki suke kallonta, itama dai cikin tsoro da fargaba take kallonsu.
Tofa masu karatu, koya zata kayane kuma, kukasance taredani danjin amsar tambayarku..........................โ๐ป
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.