Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 34 of 40

💞Bily💞
💞💞Mrs Abd[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 24~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸5⃣3⃣🔸🔶

..........Su aunty hafsat suna jin dad'in zama da sopy, to itamadai sopyn gareta hakane, tanajin a zuciyarta idan da haka dukkan dangin miji suke gsky da an zauna lfy a akasar hausa.
"" dan kiyayyar dangin miji tana tasiri wajan ruguza tubalin ginin rayuwar aure, tana haddasa gaba da kiyayya nazumincin family guda biyu, yanasa 'ya'ya da tsanar dangin mahaifinsu, adalilin k'iyaya dasuke nunawa mahaifiyarsu, to ALLAH yasa mu gyara amin.""
Uncle G! ya umarcesu da su shirya yakaisu suyi barka suduka, amma sai fareeda ta ce, "ita bazata jeba, zata zauna agida.
Uncle G! ya ce, "yaza'a abarki agida ke kad'ai ai zaki takura, karki damu babu abinda zai faru sai alakairi, tunda suka fad'a da bakisu sun yafe miki.
Fareeda dai tatsaya tsayin daka akan bazata jeba, haka suka hakura suka barta.
Uncle G! yanaso yayi barci agidan, amma saboda gudin abinda zaije yadawo saiya hakura yafita.
Su sopy suka shirya suka tafi, bayan ummy tazo tayi musu jagora.
Da gudu sopy tashiga gidan tana kiran aunty Asiya, taje ta mamik'e katon jaririn da aunty Asiya ta haifa, wata sabuwar kaunarsa tana ratsata, jitake kamar itama tasamu k'ani ciki d'aya.
Ummy tak'araso da su aunty hafsat cikin d'akin, aunty asiya ta ce, "ALLAH ya shiryaki sopy, shine kikayo gaba kika bar baki abaya.
Libabatu ta ce, "ai bakomai tana murnane, anan suka wuni, akasha fira, su aunty hauwa'u ma sunzo, da zainab da Nafisa, aiko akasha hira kamar sun saba dasu aunty hafsat.
Muna nan zune saiga gayyar 'yan professional writer suma sun iso, sopy tayi matuk'ar farin cikin zuwansu, tashige cikinsu anata shan hira da tambayar ina fareeda ta ce," musu tana gida suka barota.
Sai wajen karfe biyar muka bar gidannan, bayan munci munsha daga mai k'yau, can na hango marakisiyya da madina sunata k'atuwar lauma, nayita harararsu dan karsu bamu kunya, amma ina saida sukaji sunyi nak, harda tambayar sopy wai kozasu sami wanda zasu kaima saratu ta fatima pii, dan karsu basu labari suji haushi akan su basu ciba.
Da haushi ya isheni saina yo waje batareda najira amsar da sopy tabasuba😜😜.

Agajiye suka shigo gida, sun tarar da fareefa a falo tana kallo, tayi musu sannu da zuwa, suka amsa suna zama, sopy ta ce, "fareeda uncle fa??.
Saida ta yatsine baki sannan ta ce, "bai dawoba.
Ko babu komai sopy taji matuk'ar dad'i da faruwar haka, dan dama bataso tabar fareeda da uncle G! agida d'aya su kad'ai, dukda tayi matuk'ar yarda da uncke G! d'in, amma tana tsoron sharrin shaid'an uban had'in tuggu, dakuma fareeda uwar gidansa, uwar cin amana.
Agurguje sopy tayi wanka, tazo ta d'ora abinci, saboda kar uncle yadawo babu abinci agidan, kan kace mi gida ya kaureda kamshi mai dad'i, Libabatu taje kichin d'in tana tsokanar sopy, wai mitake dafa misu su manyan masu gida, sopy tayi dariya tana fad'in ai kune na robar, yanzu ina had'awa na k'arfenne, suka tuntsure da dariya harda tafawa kamar k'awaye, kai jama'a wannan zama yana burgeni, dangin miji kamar danginka.
Sai gab da magriba uncle G! yashigo, agurguje yay wanka yanufi masallaci, sai bayan isha'i yashigo, sannan suma sunyi sallah, yashigo musu da kayan marmari, sukaci abinci suka k'oshi sannan aka shiga hira mai dad'i, saida sha d'aya tayi uncle G! ya ce, "bari suje su kwanta dan gobe sunada makaranta, badan angaji da hirarba kowa yaje ya kwanta.

Da safe da wuri sopy ta tashi tahad'a karin kumallo, suka shirya sukaci itada uncle G!, suka bar musu nasu, sukai musu sallama suka tafi, suma suka bisu da addu'ar dawowa lafiya.
A maranta sopy tana tareda Nadiya, dan yau bataga zalihaba rediyo mai jini.
Haka suka cigaba da karb'ar lectures har zuwa karfe shidda na yamma, uncle G! ya d'akkota suka dawo gida.
Lafiyayyen abinci suka tarar su aunty hafsat sunyi, dan haka suna yin wanka sukaci abinci bayan sunyi salloli.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kullum sopy sukan biya suga jariri kafin su tafi makaranta, takan had'a musu abincin safe ta gyara gidan kafin su tafi, sukuma suna yin na rana, saidai sopy ta lura fareeda bata aikin komai agidan sai su aunty hafsat, itadai saidai abata taci ta kwanta tayi barci, dan haka faridar tayi wani irin k'yau tak'ara farida kiba.
Sopy bata tab'a tanbayarta miyasa bata aikiba, dan bata bukatar hakan.
Da haka akasha sunan d'an gidan uncle kabeer, yaci sunan baban su sopy wato ibrahim, za'a rinka cemasa khalil, anrak'ashe an kwalle, ansha shagali, fareedama taje wajen sunan, saidai tanata rab'e2 saboda tsoron 'yan uwa saita saka nik'af, ba wanda ya ganeta saisu zainab, suma sai suka shareta sukayi kamar basu ganetaba.
Mukan baruwanmu, danta shagalinmu mukeyi, uncle G! ma sun had'ama abokansu walima dai2 karfinsu, anzo antayasu murnar samu d'a.
Sai wajen sha biyu suka koma gida, kowa yanemi makwanci ya kwanta saboda gajiya.
Da safe da wuri sopy takoma gidan uncle kabeer ta taya kannan aunty asiya aiki suka gyara ko'ina tsaf.

Satinsu libabu biyu sukai haramar komawa gida saboda yara dasuka baro, uncle G! ya had'a musu shatar ta arzik'i suka tafi suna kewar sopy itama tana kewarsu, har kuka tayi konace sukayi, dan har auty hafsat saida ta matse hawaye, shikansa uncle G! yaji babu dad'i, dan zuwan 'yan uwansa ya k'ara masa farin ciki, saboda k'yaunar dayake musu, fareeda kanta saida tad'an matse hawaye saboda sabo, dahaka dai suka tafi suka barmu da kewa😭.

Yau tsawon kwanan su aysha biyu da tafiya, gida yakoma yanda yake, yau babu aiki dan haka sopy taje ganin masu jego, tabar uncle G! yana barci ad'akinsa, fareeda kuma tana falo.
Fitar sopy babu dad'ewa zuciya tashiga zuga fareeda bisaga gurguwar shawara, har zuwa sha biyun rana bata gama aminta da shawarar zuciyartaba, saidai zuciyar tata taci gaba da karanta mata tafsir mai wuyar fassara, ta kalli agogo karfe sha biyu da kwata, tad'an murmusa tanada tabbacin ba yanzu sopy zata dawoba, tamik'e da suri tashiga wanka, tafito ta tsara kwalliya, mudai muna lab'e muna kallon ikon ALLAH, tagama tsaf tad'akko wata yololiyar rigar barci tasa ka, ta feshe jikinta da turare, d'akin uncle G! mukaga ta nufa, kunsan ALLAH nikaina 'yar rahotonku saida numfashina yaso ya d'auke, amma haka na lallab'a nabi bayanta.
Ta shige d'akin tana ran gwad'a, ta maida k'ofa ta datse da key, tabi uncle G! dake kwance saman lafiyayyen gadonsa da kallo, dagashi sai gajeren wando yan barcinsa hankali kwance, dan yasha maganin mura.
Fareeda ta k'awata fuskarta da murmushi tana wani sake gyara zaman rigarta, tabbas yau saita aiwatar da abunda tadad"e tana buru, koda sopy tayi nasarar hanata auren uncle G! tofa yau saitayi nasarar had'a makwanci da ita, dan babu makawa saita saka uncle G! ya bata ruwan dazai gusar mata da k'ishir warta.
Ta taka ahankali harzuwa jikin gadon nasa, ahankali takai hannu zata tab'ashi kamar an ce yafarka, saiya tshi afirgice, cikin tsoro da fargaba yake kallon fareeda babu abunda yake ambata sai ""inna lillahi wa'inna ilairraji'un, "" wallahu galibun ala amrihi, wad'an nan sune addu'oi in dasuke fita daga kan lab'b'ansa, fareeda kuwa tana gabansa tana wani jujjuya jiki da salo2 na yaudara, wanda shaid'aniyar zuciyarta take koyar da'ita.
Adai2 wannan lokacinne kuma sopy tadawo, ta tab'a k'ofar taji arufe, bataso ta tadashi dan haka taje d'akinta ta d'akko wani key d'in, bata damu da rashin ganin fareedar ba, dan atunaninta tana kichin tana girki.
Ji sukai ana bud'e k'ofa, cikin tsananin tsoro da firgici suka maida hankalinsu awajen, sopy ta bud'e k'ofar saidai tuni zuciyarta ta yi tsawa maikama da saukar aradu, ko kwaran kwatsa, binsu take kawai da idanu, dan kallo d'aya zakai musu kaga alamun rashin gsky atareda su............................✍🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.