Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 40

Tafiyarsu tafara samun gar gada ne alokacin da Abdul yashigo rayuwar safiyya,, shima d'an anguwarsu ne,, amma abayan layinsu yake,,babanshi yanada rufin asiri dan gsky yafi iyayensu safiyya kud'i.
"Gidan su Abdul gidane na mata uku, da tarin yara dasuka kai adadin ashirin zuwa sama, Abdul shine na 6 a gidansu,, yayi karatu har zuwa (N,C,E)Sai dai Abdul irin samarinnan ne 'yan k'arya dason nuna burga.
Sun had'u da safiyya awani yammacin ranar talata, lokacin sun dawo daga islamiyya itada fareeda,, tun aranar farko da fareeda taga Abdul takamu da sonsa,, sai dai kash daga baya sai ya nuna k'awarta yakeso safiyya,, dan danan kuma soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Abdul da safiyya, wannan yasa fareeda ta danne son Abdul azuciyarta, sai dai kuma yau da gobe sirrin nata yana nema fitowa fili.
"""" dan duk ranar da fareeda taga Abdul yazo wajen safiyya takanji wani bak'in ciki da kishi,, har yakansa ta nuna fushinta afili,, duk da tasan k'awarta tata tana tsananin son Abdul,, wanda a yanzun haka ankai kud'in auren Abdul gidansu safiyya, harda saka rana,, za ayi bikinsu bayan ta kammala secondry.
"Toko wannan aure zai yiwwu??ko fareeda zata hak'ura da k'udirinta kafin k'awar tata ta fargane??? kubiyoni dan tabba tarwa.........................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 3~October ~2016

🔷🔹NI DA K'AWATA🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💕

🔶🔸3⃣🔸🔶

............yau takama weekend babu school su sopy suna gida, sopy ce zaune tana wanke wanken kwanuka inna na gefenta tana tsintar shinkafa 'yar hausa.
"Safiyya! Wai bazakiyi sauri ki tashi awajennan ba ko?? Nafad'a mikifa yau kece zaki mana abinci, amma kin zauna wanke2 bawani mai yawaba sai lank'andi kikeyi, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Sopy ta turo baki gaba ALLAH inna ni bana son yin girkin nan mutum yayta fama da iccen nan, ga azabar hayak'i idonka yayta hawaye kamar kana kuka.
Inna ta girgiza kai tana murmushi, nima d'in danake dafa miki kullum kizo kici haka nake fama, dan haka yau har girkin dare kezakiyi shi.
Sopy tazaro ido 😳kai inna da gsk kikeyi??
Na tab'ayimiki k'aryane?? Inna tabad'a tana mik'ewa tsaye,, Sopy tace"A'a.
inna tace" to yimaza ki gama ki tashi rana tanayi kinsan babanki kuma yakusa dawowa.

Sopy tai shiru tana wanke2n ta can kuma saitace inna!! Inna ta amsa da na'am.
Inna mizai hana ahad'e abincin harna dare?? A'a baza a had'eba kinsan dai babanku bason cin shinkarnan yakeba koda yaushe balle wannan fara da mai d'in, yana cine kawai dan bashida yanda zaiyi,, ayi shinkafar yanzu da daddare sai ayi tuwo.
Tuwo kuma inna!!!! Jiyafa shi mukaci nikam nagaji da cin tuwonnan wlhy.
Inna ta d'auki wani murfin roba dake gefenta ta jefi safiyya dashi,, dan k'aniyarki in bakici tuwonba mizakici?? Ko kin ajiye mana wani abincinne bayan tuwon?? Kudai yaran yanzu bakusan ku godema ALLAH ba yayin dayay muku ni'ima, da basai ki wuni ki kwana bamuci abinci agidannan ba, amma yanzu ALLAH yarufa mana asiri shine zakiyima mutane iyayi,, kul nasake jin wannan furicin abakinki.
"" Sopy tai kwal2 da idanu tana shirin yin kuka dan ganin ran innarta ya b'aci, tace" dan ALLAH inna kiyi hak'uri bazan sakeba ki gafarceni???
Inna tai murmushi to shikenan ya wuce share hawayenki kinji,, barma girkin nizanyi.
A'a inna kibari zanyi tafad'a tana nufar kichin d'in da hayakin wuta ya maida bangon bak'ik'k'irin, tafara k'ok'arin had'a wutar icce.

Sopy tana aiki suna hira da inna, inna tace waini lfy yau banga fareeda ba agidannan kuma kema banga kinje gidansuba????
Sopy tace"wlhy babu komai inna, tacemin ne zataje gidan k'anuwar mama a hotoro, nikuma kinsan ba shiri muke da'itaba shiyyasa nace bazanjeba,, to inaga tana can bata dawoba.
Hummm kudai kaiwai shirmenku ne ya motsa amma in banda haka miye nawani rashin shiri kema aii sadiya innar kice.
"Taf inna ALLAH yakiyaye sadiya tazama inna ta,, dan tunda nalura batasan abotarmu da fareeda nai alk'awarin na daina zuwa gidanta,, idan tazo nan anguwar ma gaisa, shima idan mun had'u kenan.
Inna ta shige d'aki tana fad'in kudai kuka sani.

::::::::::::::::::::::::::::::::::::☆
Fareeda tana gidan innarta sadiya, k'anwar mamace mahaifiyar fareeda, itamadai bawata babba bace dan kusan sa'ar hauwa'u ce yayar safiyya.
Suna zaune afalon sadiyar gabansu tiren taliyane da yaji damai,, kunsan dai mu 'yan kano mun iya k'wad'ayin mai da yaji, sadiya takalli fareeda 'yar uwa ina jinki jamuje labari.
Fareeda ta harareta oh dama matsalar tawa labarice?? Sadiya tace yi hak'uri ina tsokanarkine. """Fareeda taja ajiyar zuciya sannan takuma gyara zama tana fad'in wlhy anty da nayi niyyar bar mata Abdul amma yanzu bazan iyaba, idan nagansu tare jinake tamkar na had'iyi zuciya na mutu.
Dan ALLAH ki bani shawara miya kamata nayi???? Dan na mallaki Abdul.
"""Sadiya tayi murmushi aii wlhy koni ban goyi bayan ki bar mata shiba, Abdul k'yak'yk'awane dama dake yadace bawannan bak'ar yarin yarba,k'ilama asiri tai muku dan na lura tun farko ke yake so. Fareeda ta gir giza kai,, bana tunanin haka aunty sadiya nasan halin sopy nakuma san abinda zata iya,, inama tasan inda wasu malamai suke?? bare taje, kedai kawai bani shawara.

Sadiya ta tab'e baki dan ta lura fareeda bazata gane inda ta dosaba,, tace kawo kunnanki kiji!!!;!!
Fareeda ta mik'a kunnenta ga sadiya, can kuma sai suka tuntsire da dariya harda tafawa, fareeda tace"wlhy shawararki tayi auntyna ALLAH ya biyaki,, inada tabbacin samun ABDUL yanzu.
Tofa masu karatu wace irin shawar sadiya tabama fareeda ne??? dahar take murna haka, harma da tabbatar wa kanta samun ABDUL,, to kudai biyoni dan jin wannan bada k'ala.......... ..✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕

4~October ~2016

🔷🔹NI DA K'AWATA 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💕

🔶🔸4⃣🔸🔶

..............koda yamma da fareeda tadawo bata shiga gidan su Sopy ba, Sopy tagama shirin islamiyya ta fito, inna bari nagani ko fareeda tadawo saimu wuce islamiyya idan kuma bata dawoba nisai na wuce.
"" to autar inna adawo lfy""
Tafita tana fad'in ALLAH yasa innata.
Da sallamarta tashiga gidan, mama dake zaune a k'ofar d'akinta tana linke kayan wanki, ta amsa da fara'arta,, Sopy ta tsugunna ta gaida mama.
"Mama tace" waini yau ina kika shiga safiyya?? Duk yau ban gankiba, ince dai lfy???
Sopy tayi murmushi wlhy lafiya lao mama ina gidane kawai.
Aii d'azu danaga fareeda ta shirya canake tare kuka tafi hotoron??
A'a mama batare mukajeba saboda zanyi wanki.
ALLAH sarki kishiga tana nan tun d'azu tadawo inagama barci takeyi;

Sopy tamik'e tana fad'in fareeda kasace aii,, amma barcin yamma.
Tad'aga labilen d'akin fareeda kwance d'ai d'ai akatifa tana kwasar barci, Sopy tak'arasa cikin d'akin tasa hannu ta daki bayan fareeda, ke uwar barci tashi.
"Fareeda ta taahi a firgice tana fad'in wayyo mama.......saitaga safiyya tsaye akanta,, Sopy tace sarkin tsoro kawai kin wani tashi afirgice kamar wadda aka firgita.
Fareeda ta harareta wlhy sopy ke 'yar iskace miye na tashina ina barci??
To badole natashekiba tunda ke bak'ya duba agogo, kullum kece kikeja mu makara a islamiyya.
Fareeda ta yatsine fuska aini inagama yau bazani islamiyyar nanaba.
" saboda me??? Sopy ta tanbaya.
Babu komai kainane kawai keyimin ciwo.
Sopy tace" kinsha maganine?? A'a ban shaba amma yanzu zani nasiyo tunda kin tasheni,, tamik'e barima mufita tare.

Tare suka fito fareeda ta amshi kud'in magani awajen mama suka tafi,, dai2 zasu fita kwanar layinsu suka gamu da ABDUL dawani abokinsa Adam,, adam yace" 'yan halak kunk'i ambato yanzu muke hirarku ashe kuna hanya.
"CIkin zolaya Sopy tace" kodai kuna gulmarmu???
Abdul yace" kajiko abokina shiyyasa nace kayi shiru karka fad'a,, wad'an nan baka iya musu.
Adam yay dariya gsky ne abokina,, wannan abotar mai k'arfice nadad'e banga k'awaye masu irin shak'uwarkuba, gaku nan tamkar 'yan biyu.
"" fareeda tace" lah bakada labarin mu 'yan biyune rana d'aya aka haifemu kaje ka tambaya.""
Adam ya jinjina kai aii bama saina tambayaba nayarda, dan abokina yatab'a fad'amin.
"Abdul yamatsa kusada sopy gimbiyata yayadai??
Tai murmushi lfy lao habibina saidai my sister ce kanta yake ciwo.
Ayya ALLAH yak'ara sauk'i shiyyasa naga d'aya da uniform d'aya babu???
Sopy tayi murmushi eh kusan hakane danni zanje islamiyya itakuma zata sayo magani ne.
"Ayya sorry fareeda ALLAH yak'ara sauk'i."
Amin fareeda tafad'a tana fari da idanu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.