Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 12 of 40
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, karatu yana tafiya yanda sopy ke buk'ata, domin tana fahimtar komai dallah dallah, daga ranar kuma bata k'ara yarda tamakara lecture d'in uncle G! Ba, da duk wani malami,, dan ta zauna ta tsarama kanta lokaci tayanda zai amfaneta harma ya amfani waninta,, matsala d'aya tafara fuskanta shine yanda samarin makarantar suke matsa mata, itakam ayanzu ta tsani halin maza dan tundaga abinda Abdul yay mata tayima maza k'ud'in Goro, tana matuk'ar bak'in cikin namiji ya ce, "yana sonta, amma tana iya bakin k'ok'arinta domin kaucewa dukkan wani namiji, ta maida hankalinta akan karatunta gaba d'aya,, tana kuma k'ok'arin mancewa da abinda ya faru a baya, dukda har yanzu zuciyarta tana k'aunar fareeda, idan tatunata takanji matuk'ar kewarta da begen ganinta, haka son Abdul yana nan azuciyarta amma tana addu'ar ALLAH ya yaye mata sonsa, yakuma mantar da ita shi.
Su fareeda amare, ana gidan Abdul ana shan amarci, sai dai tana fuskantar matsalar yanayin zaman takewar gidan, gidane mai matuk'ar yawa, wanda yatara iyaye da 'ya'ya da jikoki, ga matan yayyensa suna shiga rayuwarta,, tagayawa Abdul amma yak'i d'aukar wani mataki, ga yaran gidan basuda wata cikakkiyar tarbiyya, dan kwata kwata yaran basa respert d'in na gaba dasu, sun raina yayyensu da matan yayyen.
Fareeda tafito daga kichin hannunta d'auke da kula, Abdul yashigo ransa ab'ace, tad'anja baya dan ganin yanda yafad'o babu ko sallama, ya wuceta batareda ya ko kalletaba, asanyaye tabishi zuwa d'aki, yana kwance akan gado yarufe fuskarsa da filo, tasa hannu tacire filon tana fad'in my love! bakada lafiya ne???
Cikin matuk'ar masifa ya ce, "asibiti ne ni.
Tad'anja baya tana fad'in ALLAH yabaka hak'uri.
Ya maida kansa yana fad'in kayane nad'e gammo na d'ora miki, yaja tsaki.
Fareeda ta zauna jagwab saman kujerar madubi, ta rintse idanu tana fad'in na shiga uku kardai ace Abdul zai fara juya min baya, lallai dolene na nemi zuwa gidan aunty sadiya.............âœðŸ»
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 19~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣9⃣🔸🔶
..............zaliha tak'araso dad'an gudunta, tana fad'in kai sopy shine kika taho kika barni?? Sopy tajuyo tana kallonta, ato naga ke kwalliyace damuwarki , bayan kinsan wannan d'an hayak'in shine zai farayi mana lecture yau.
Zaliha ta ce, "to muje aii akwaima sauran lokaci.
Jikin wata bishiya suka zauna kafin lokaci yayi.
Zaliha ta zunguri sopy, sopy! Sopy!! Ga mutuminki!!.
Sopy ta juyo, waye kuma mutumina? Karaf idanunsu suka had'u a karkashin inuwa d'aya,, tai saurin janye nata dan ganin wajensu ya nufo.
Wad'anda suke wajen suka shiga gaisheshi, yak'araso cikin tak'ama yana sanye da bak'in wando da jar riga, sai zabga k'amshi yakeyi, sajen nan ya kwanta luf luf akan k'yak'yk'yawar fuskarsa, azuciyar Sopy ta ce, "yaukuma k'ananun kaya aka saka".
Jin zaliha tana gaidashi sai itama tadawo hayyacinta, ta gaidashi itama ya amsa da lfy, kowa yazuba musu ido, shima ganin haka sai kawai ya wayance da tambayarsu wacece sakina musa?? Zaliha ta ce, "uncle G! Muma bamu santaba, sopy ko bama ta tankaba, yajuya yana tambayar sauran d'aliban dake gurun, suma sukace basu santaba, yajuya yatafi, yana maijin haushin kansa, way sai yaushe yarinyar nan zata fahimci inda nadosa ne?? Ko sotake saina furta mata da bakina ne?? Yad'anja k'aramin tsaki, yarinyar nan miskilancin tafa yayi yawa, gashi sonta yay masa shigar sauri, batareda ya shiryaba, ya lumshe manyan idanunsa masu suffar ganyeðŸƒ, ya salam! Yafad'a tareda fitarda huci daga bakinsa.
Office yakoma yazauna, yajingina bayansa da kujera, idanunsa a lumshe tamkar mai barci.
K'ofar aka kwankwasa, ko motsawa baiyiba, saida aka buga sau uku sannan ya ce, "waye"?.
Wata zazzak'ar murya ta ce, "nice!!
Ya d'anja tsaki, ya ce, "kowaye ya shigo, ahankali aka turo k'ofar wata k'yak'yk'yawar yarinya fara tas tashigo.
Ya ce, "kowaye yafad'i abinda yakawoshi!, cikin rawar murya ta ce, "dama dadynane ya ce, "kazo ku gana idan kasamu lokaci.
Yabud'e fararen idanunsa wad'anda sukai d'anja ahanlin yanzu, sai dai har yanzu yana kwance a kujerar, yabita da kallon rainin hankali, miya faru yake nemana?
Ta gyara tsayuwa yanaso kuyi maganane.
Ya jinjina kai, toki sanar dashi yazo shi yasameni dan bana zuwa gidan kowa, kumama inada ayyukan yi masu yawan gaske.
Kuma indai akan maganar damukayi dakene, karma yafara zuwa wajena, ke kuma ina mai k'ara gargad'inki akan kifita hanyata, inko bahakaba zan cigaba da b'ata miki rai fiyeda yanda kike tsammani.
Yanuna mata hanyar fita, zaki iya tafiya dan inada aikin yi.
Ta marairaice fuska tamkar zatayi ihu, ta ce, "plz uncle G! ka daure muyi magana dan mu fahimci juna, wlhy ina tsananin k'aunarka, ka daure kasoni, nayimaka alk'awarin zan kasance yanda kake buk'ata, wlhy nayi maka alk'awari.
Uncle G! Yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad'an tsura mata idanuwa bahijja!! kamar yanda nafad'a miki tun farko, ba soyayya takawoni makarantar nan ba, bake kad'ai kika tab'a cewa kina sonaba, kuma suma amsar dana baki ita nake basu, ina mai baki shawara daki hak'ura kema kamar yanda suma sauran suka hak'ura,, kuduka bakwa cikin irin matar danake son aura, dan haka ina mai baki shawarar ki sama ranki hak'uri, daga yau kuma karki sake zuwa office d'ina, danni ba'a shigo min office saida dalili, kuma dalilin ma wanda yashafi karatu,musamman ma mata, ya nuna mata hanya zaki iya tafiya.
Taja numfashi idansu, har sun iya hakura da kai toni tabbas bazan iya rabuwa dakaiba, kaine mutum nafarko dana fara so kuma kaine na k'arshe, zan sanar da mahaifina yazo kamar yanda ka buk'ata, tunda kai kace bazakajeba, tana gama fad'a tafice abinta.
Shima tsaki yaja, yamik'e yana fad'ar ashe zaki mutu da son nawa kenan, dan har abada bazan sokiba, littatafai ya d'iba yafice shima, dan ya gudanar da lecture.
Ajinsu sopy yanufa, kamar yanda yasaba haka ya aikata, yahana makararru shiga, babu b'ata lokaci yashiga gudanar da lecture.
Sopy agaba take zaune, duk d'agowar datayi sai sun had'a ido da uncle G!, dan haka ma saita daina kallon inda yake, amma tanaji ajikinta har yanzu yana kallonta, kamar yanda yasaba yauma ya ce, "zaiyyi test.
bayan sun gama test yabisu yana karb'a, yazo karb'an na sopy, saida yafaki idon sauran d'aliban sannan ya ajiye mata wata takarda, ya karb'i ta hannunta, da ido ya nuna mata takardar daya ajiyemata, batace komaiba tad'auka kawai.
Bayan fitarsa kowa yafito, kafin ashiga wata lecture d'in.
Sopy batabi takan takardar uncle G! ba, dan bata d'auketa dawani muhimman ciba...............âœðŸ»
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 20~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸2⃣0⃣🔸🔶
............fareeda al'amura sun fara canja mata, dan yanzu Abdul yafara canja yanayin zaman nasu, ga masifar datake fuskanta wajan ummarsa, dan ummar Abdul masifafface, dukkan matan gidan tsoronta takeji, saboda masifarta.
Ta kula tunda likita ya ce, "tanada shigar ciki, tafara fuskantar matsala wajen Abdul, yafara nisantarta, Baya yin fira da ita yanzu, bakuma yadamuwa dasu kwana gado d'aya.
Lamarin yana damunta, gashi yahanata zuwa gidan aunty sadiya, ya karb'e wayarta tuni, yauma tana zaune ta yi tagumi, babu abinda take buk'ata sai nama,, tasan kuma Abdul bazai saya mataba, ga cikin nata mai shegen tsurfa da kwad'ayi, ta cije leb'e hawaye suka zubo mata akumatu, lallai idan har rayuwa tajuya mata baya to kuwa taga ta kanta, dan yanzu batada wanda zata tunkara tasamu sauk'i, aminiyarta tayi mata nisa, nisa kuma mai tarin yawa, tasan yanzu babu wadda sopy ta tsana kamar ita, garashin 'yan uwa, ga rashin iyaye, tafashe da kuka, kuka take tamkar ranta zai fita, nikam na tab'e baki dan wlhy ko kad'an banji tausayin taba, na ce, "ni!, barima natafi wajen k'awata sopy, nagano muku takardar da uncle G! Yabata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.