Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 18 of 40
Agidansu sopy kuwa anata shirin bikin uncle kabeer, sopy duk tazama busy sakamakon duk abinda uncle kabeer zaiyi saida ita, ga makaranta damma cikin weekend za ayi bikin, batada wani lokacin kanta, yauma suna gama lecture uncle kabeer yakirata akan tashirya gashinan zuwa zai d'auketa suje wani waje, gudu2 tayi wanka bata tsaya yin wata kwlliyaba ta zura doguwar riga ta shadda tasaka hijjab sai dai yau iyakarsa guywa tad'ansaka turare ta fito.
Bata dad'e da fitowaba shikuma ya shigo cikin makarantar, bayan sun gaisa ta ce, "to uncle mutafi ko?.
Ya ce, "sai mun jira youseef dan hardashi zamuje.
Sopy tai saurin kallon uncle kabeer, uncle dammi sai da shi zamu?.
Uncle kabeer ya ce, "dan yanada muhimmanci atafiyar.
Sopy tayi shiru dan ita kam gsky bata son tafiya tare da shi, inhar yana guri bata sakewa, saboda tsananin kunyarsa datakeji......, muryarsa ce ta katse mata tunaninta, yak'araso yana fad'in sorry na b'ata muku lokaci ko?.
Uncle kabeer ya ce, "A'a, itama aii yanzu tazo.
Sopy ta daure ta ce, "ina yini sir! ?.
Ya ce, "lafya lau maa!.
Uncle kabeer ya tuntsure da dariya ya ce, "one one, kenan.
Suka shiga mota suna dariya banda sopy datad'an murmusa kawai, tunda suka shiga mota sopy tayi tsit, sai dai duk d'agowar dazatayi saitaga uncle G! Ita yake kallo ta madubin gaba, ganin yasaka mata ido saita daina d'agowa ma gaba d'aya.
Kasuwa sukaje, suka lodo kaya, na duk amfanin dazasuyi awajen biki, tundaga kayan abinci da drinks, da duk wani abunda zasu iya bukata, sun siyo dai dai k'arfinsu, suka zubo amota suka kai inda zasu ajiye.
Uncle kabeer ya ce, "auta saura d'inkinki ko?.
Sopy ta ce, "uncle aii telan ya ce, "sai gobe idan ALLAH yakaimu.
Okey to ALLAH yakaimu goben, yanzu bari mu kaiki makaranta ko?.
Ta ce, "dan ALLAH uncle ka kaini gida gobe sai nadawo.
Uncke G! ya harareta, saboda son yawo ko?? To makaranta zamu maida ke, dan goben da safe nine zan fara yi muku lecture, kuma harda test mai zafi, kinsan kuwa idan bak'ya nan hukuncin ki yafi nakowa.
Uncle kabeer ya juyo yana kallonta, to kinji fa, kinyarda na kaiki gidan??.
Sopy ta d'ago ta kalli uncle G!, daya tsura mata fararen ida nunsa masu haske, tai saurin maida kanta k'asa kamar xatai kuka.
Uncle kabeer ya ce, "sopy shagwab'arki tayi yawafa, ko kin manta kin girma, nafa kusa aurar dake.
Aii kamar jira take saita rushe da kuka.
Sukuma sai dariya ta kufce musu, suka fita daga motar suna dariya, uncle G! ya ce, "gsky kabeer bakada kirki, ya bud'e baya yashiga inda sopy take zaune, yakai hannu zai kama hannunta saita k'ank'ame jikinta, shima saiya fasa,.
Cikin taushin murya ya ce, "to kukan ya isa haka, ke dai abu kad'an sai kuka, kabeer ya shagwab'aki dayawa.
Ta turo baki gaba, ya ce, "hummm, ashe idan baki maida bakin nanba zan tsotseshi yanzunnan.
da sauri ta rufe fuskarta, ta kama k'ofa zata gudu, amma sai tajita gam arufe.
Ya murmusa da ina zakije??
Ta ce nidai kutafi na fasa zuwa gidan.
Uncke G! Ya ce, "aii dama dole ki fasa, tunda na hana, ya mik'a mata wata leda ga wanna kiyi kwalliyar biki ko,.
Ta ce, "uncle kabeer da babafa duk sunyimini d'inki.
Ya ce, "to aii nasu daban, nawa daban, su iyayene, nikuma mijine.
Tai k'asa dakai tana fad'in nagode ALLAH yak'ara bud'i.
Ya murmusa dan jin dad'in addu'arta gareshi, yad'ora da fad'in, kamar yanda nayi miki alk'awari gobe zan aika a d'akko miki Aysha.
Da sauri ta ce, "dan ALLAH dagaske sir!.
Uncle G! Ya harareta oh, bazaki daina cemin sir! D'innan ba ko?.
Ta ce, "to aii dai sunankane ko.
Ya ce, "humyim, zanyi maganin bakinki, nan bada dad'ewaba.
"Shiru tayi masa."
Yayinda uncle kabeer yashigo motar yana fad'in kunga kumuje nifa inada aikin yi, dannaga ku soyayyace agabanku.
Sopy ta ce, "kai uncle nidai dan ALLAH kabari.
Uncle G! Ya koma gaba yana fad'in kaidai anyi uban banza, nikam ban more sirikiba.
Uncle kabeer yay dariya yace, "habawa kaidai kabini ahankali idan ba hakaba na hanaka d'iyar.
Taf, dakasha matsa kuwa, kaga aii kabayar da wuriko?? uncle G! Yafad'a yana tada motar...................âœðŸ»
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 28~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸2⃣8⃣🔸🔶
...........biki dai ya kankama, komai yana tafiya yanda akeso, Aysha k'anwar uncle G! Tazo, sopy tayi farincikin ganinta, itamadai Ayshar! sopy! ta burgeta, tana ganin kuma ida yayansu ya aureta bazasu samu matsalaba, dan suma talakawa ne kamarsu, kuma gidan mutunci.
Duk inda sopy tashiga Aysha na biye da ita, wannan yasa tasamu sauk'in wasu ayyukan, uncle G! Kam bata ganinsa domin suma suna can suna hidimominsu.
Yau aka d'aura auren KABEER MUKTHAR da ASIYA ALIYU d'aurin auren yasamu halartar mutane masu yawa, musamman abokan aikinsa da kuma wad'anda sukayi karatu tare, ga mutanen baba suma, to saimuce ALLAH yasanya alkairi uncle kabeer ALLAH yabada zuri'a d'ayyiba, nanda wata tara mu dawo suna.
Da daddare aka kai amarya d'akin mijinta, su sopy sun isa gidan tun kafin zuwan amarya, amarya da danginta suka iso, anyi musu tarba ta mutunci, bayan an kammala abubuwan al'ada, motoci suka kwashi mutane domin maidasu gidajensu, amma sopy da Aysha sunanan, uncle kabeer ya ce, "su tsaya su gyarama amrya inda aka b'ata, dan k'awayenta sun tafi dan gudun karsu rasa motar dazata maidasu gida, bayan tafiyar kowa suka k'uk'e suka gyara gidan suka bajeshi da k'amshi, wajan k'arfe tara abokan ango suka rako angon k'amshi.
Sudai su safiyya k'ofar gida suka koma domin jiran su, basufi minti talatinba suka fito, motar uncle G! Suka shiga ya maidasu gida, a k'ofar gidansu sopy uncle G! ya ce, "Aysha tashiga gida, Sopy ta ce, "to nima aii gidan zanje.
Ya ce, "A'a zamuyi magana ne.
Dole tayi shiru.
Bayan fitar Aysha, uncle G! Ya kalli sopy, ita kuma tayi k'asa da kai, ya d'an murmusa yana fad'in Safiyya! sarkin kunya.
Yanda yakira sunan nata saida tsigar jikinta ya tashi, tabbas babu wanda ya iya fad'ar sunanta kamar uncle G!, yakan fad'i sunan dawani irin yanayi mai saka mamallakiyar sunan cikin wani irin yanayi.
Yay gyaran murya, tareda k'ara ambatar Safiyya!!
Itama cikin sanyin muryarta mai zak'i ta ce, "Na'am.
Yad'an gyara zamansa, ina ganin gobe idan ALLAH ya kaimu zan maida Aysha gida, daga nan kuma zan taho da magabatana domin kawo kud'in aurnmu!!.
Sopy tayi shiru tana tunani, yad'an buga yatsunsa biyu sukai k'ara, ta juyo tana kallonsa, yay murmushi tunanin mikikeyi ne?.
Ta ce, "bakomai, amma dan ALLAH kabar Aysha tad'an k'ara kwana biyu.
Ya ce, "bazai yuwuba Safiyya saboda Aysha tana makaranta kuma kinga gobe litinin, tamayi asarar karatun goben kenan.
Sopy ta ce, "hakane, amma dan ALLAH idan anyi musu hutu zaka kawota.
Karki damu, zatazo insha ALLAHU sannan ma kina gidanki!.
Tasa hannu tarufe fuska.
Humm sarkin kunya kenan, nikam kar kunyarnan ta cutar dani a abayan aure.
Bata ce, "komaiba tabud'e motar ta fita.
Yay murmushi to saida safe tunda babu sallama.
Washe gari uncle G! Yazo d'aukar Aysha, da kuka suka rabu da sopy, inna tanata lallashin Aysha, haba Aysha kukan ya isa haka mana, insha ALLAHU kwanannan ma zata dawo wajenku kinji, kiyi hak'uri kibar kuka ya isa haka.
Da haka dai sopy tarako Aysha wajen uncle G! Dake k'ofar gida, yabisu da kallon mamakin dan ganin idanunsu duk hawaye, ya jinjina kai yana fad'in sannunku da kuka, saikace wad'anda zasu mutu.
Sopy ta gaidashi ya amsa yana kumshe dariya.
Ahaka dai sukai sallama, uncle G! Yaja mota suka tafi, tunda suka tafi Aysha take kuka, saida uncle G! Yadaka mata tsawa sannan tayi shiru.
Cikin fad'a ya ce, "kinbi kin dameni da kuka, saikace har abada bazaku sake had'uwa ba? Inhar bakimin shiruba to wlhy zan tsaya na zaneki anan.
Tasan halinsa sarai dan haka tayi shiru, ta ce, "yaya dan ALLAH kayi hak'uri wlhy aunty safiyya tanada kirki, duk wanda ya zauna da'ita dole yayi bak'in cikin rabuwa da'ita, dan ALLAH yaya kuyi aure da wuri dan tadawo gidanmu gaba d'aya.
Uncle G! Yay murmushi oh Aysha kinda abin dariya wlhy, to wai mi auntyn nan taki tayi miki hakane kiketa yabonta??
ALLAH yaya sunada yawa, yanzu haka bakaga tsarabar datayo minba, ta gwaggo da ban ta baba daban hardasu aunty hafsat ma duk tayi musu suma.
Uncle G! Ya jinjina kai lalai aunty tana jidaku, kenan ni kad'aine batayima tsarabarba??. Aysha tayi dariya to yaya ai kai kuna tare kulum shiyyasa.
A'a bawani muna tare ita dai ta wareni kawai.
Haka sukaita hira har zuwa gida.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.