Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 40
Zaune yake a offece yana duba takardun jiya, dasu sopy sukayi teat, har yazo kan wata takarda danaga ya kurama ido, yajuyata yak'ara juyawa, sai kuma yak'ara maimaita sunan SAFIYYA IBRAHIM KABEER, tabbas yarinyar ce yafad'a afili, domin lokacin dayake zagaye sunan daya gani akan takardar gaban ta kenan, ya cire gilas d'in idonsa, yakuma murza idon dan tabbatar da abinda yagani shin gskne kokuwa idanunsane suke masa gizo??
Amma yasan ba gizo bane, domin sopy ita kad'ai tazauna, bare ya ce, "wajen wani ta kwafa".
Yacigaba da juya takardar yana kallo,, aka kwan kwasa kofar domin neman izinin shigowa.
Ya ce, " who is that?
Daga can akace nine.
Yay dariya come in, my gay!.
Abokinsane malam faruk, shima lecturer ne a makarantar, yabashi hannu suka gaisa, ya kalli takardar hannunsa, my man! lfy naga kanata juya takarda??, ko watace ta ce, "tana sonka??, dan na sanka akwai farin jini."
Uncle G! Ya kalleshi aii idan wannan nema da sauk'i.
Malam faruk ya gyara zama to minene yafaru??
Kasan wani abu?? "A'a saika fad'a,, wato wata yarinya ce tabani mamaki wlhy, jiya namusu lecture, to sai takasance acikin makararru, yauma haka, amma abinda yabani mamaki nayi musu test , saikuma ta amsa mini komai dai dai, yamik'a masa takardar, karb'a kagani.
Malam faruk yakarb'a yana dubawa, ya jin jina kai , lallai wannan yakai ayi mamaki, dukda akwai mutane masu kwazo da kwakwalwa aduniya,, kai kankama abin misaline, dan haka karkai shakku.
Uncle G! Yad'an tab'e baki yana fad'in hakane abokina.
Sopy suna zaune itada zaliha a kofar wani class, saiga uncle G ! Yafito daga ajin, hannusa d'auke da littatafai, suka gaidashi sau d'aya ya amsa musu, har yad'an gotasu saikuma ya dawo, litta taffan hannunsa ya mik'awa sopy, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, " ki kaimin offece d'ina.
Cikin rawar murya sopy ta ce, "aii ni bansan offece d'inkaba, yad'an juyo ya kalleta, dan har ya fara tafiya, ki tambaya mana, taji yafad'a ya wuce abunsa.
Sopy takalli zaliha ta ce, "zaliha plz idan kin sani ki rakani mana? Zaliha ta rik'e hab'a rufani ki sayani sopy, sai dai na nuna miki, dan wlhy bakowa yake shiga wannan offece d'inba.
Kamar ya bakowaba ? To dan me??
Saboda maishi baya bari, kinga kina k'ara b'ata lokaci muje na nuna miki.
Sopy tabita tana mamakin yanda yawancin students a d'in makarantar suke shakkarsa,, dukda school d'in ta kasance university gidan 'yanci.
Da wannan tunanin tak'arasa offece d'in da zaliha ta nuna mata,, a tunaninta baya nan dan haka ta dannakai kawai abinta batareda neman izinin shigaba,, tai sauri jada baya dan ga nin sa zaune akujerarsa ya d'ora k'afarsa saman tebir d'in gabansa, yana latsa waya.
Ya d'ago yana kallonta idanunsa sanye cikin glas, cikin rawar murya ta ce, "sorry ser bansan kana cikiba.
Baice mata komaiba , sai dai ya nuna mata tebir d'in dake gabansa, alamar ta ajiye.
Ta ajiye ta juya zata tafi,, sai taji ya ce, "waya baki izinin tafiya?? Ta juyo da sauri tana kallonsa, dan batai zaton da ita yakeba, amma saitaga shima ita yake kallo, tadawo ta tsaya, ya sauke k'afafunsa kasa, ya ce, "bismilla zauna".
Jikin sopy a sanye ta zauna zuciyarta cike da mamakin wannan irin karfin hali haka.
Yakai tsawon minti biyar bai sake bi ta kanta ba yanata latsa wayarsa, saida ya mula Dan kansa, sannan yad'ago yana kallonta ya ce, "SAFIYYA IBRAHIM KABEER ko?
Dukda ba yau aka fara kiran cikakken sunantaba kamar haka , amma saitaji yau sunan yay mata daban tamkar banata ba, domin kuwa ya iya fad'ar sunan,, kamarma yafi kowa iyawa ..................âœðŸ»
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 18~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣8⃣🔸🔶
...............ya ce, "koba "k"!, baceba???
"Tai saurin fad'in nice ser."
Ya jinjina kai tare da janyo wata takarda yamik'a mata, waye ya rubuta miki wannan????
Sopy takarb'a tana kallon takardar, test d'in ranarce aii, tad'an gyara zamanta, bawanda yarubuta min nice nayi da kaina.
Yad'an tsura mata idanu wannda yasa dole tayi k'asa da kanta domin kunya, shikuma ya murmusa, Karo na farko dana tab'a ganin murmushin sa, yacigaba da kallon takardar Kenan yanzu idan nace ki sake rubuta min zakiyi kamar haka??.
Sopy ta jin jina kai, ta ce, "insha ALLAHU ser".
Ya ce, "good", takarda da biro yabata, nabaki minti goma sha biyar.
Tad'an kalleshi saikuma ta kauda kai, azuciyarta ta ce, "idan kasaba rainawa d'alibanka hankali, to nikam bazan amince ba, taja takardar tana rubuta amsoshin tanbayoyinsa, tagama acikin minti goma.
Yad'an kalleta cike da mamaki, itama kallonsa take, ya danne mamkinsa dan karta kawo masa raini, ahankali ya furta zaki iya tafiya.
Sopy ta mik'e batare da ta tanka masaba, ta fice abinta.
Yabita da kallo afili yafurta miskilanci!!, humm kunji masu karatu shiya manta da nasa miskilancin, ahankali ya kwanta da bayansa ajikin kujerar, hannunsa rik'e da takardar data rubuta yanzu, yaja ajiyar zuciya, ya sumbaci takardar ya lumshe fararen ida nunsa masu suffar ganye.ðŸƒ
Narik'e hab'a dan mamaki, marak'isiyya ta zungureni aunty bily mikenan??? Naja numfashi wlhy nima bansaniba marak'isiyya, saidai musa ido akansa dan gano miye sirrin zuciyarsa,, amma wannan irin subba da yayma takardan nan aii abin tanbayane?? Marakisiyya ta ce, "lallaikam aunty bily.
Sopy na fitowa zaliha ta tareta, sopy miya faru?? naga kin dad'e, Sopy ta harareta to uwar 'yan son gulma babu komai.
Plz dan ALLAH ki fad'a min nasan hakanan banza bazaki dad'e a offece d'in uncle G! ba, sopy tai d'an tsaki to bawani abubane test d'in jiya yasani na sake.
Ban ganeba??
Sopy tai gaba aii dama ke baki ganewa.
Zaliha tabiyota tana naci, dole sopy tagaya mata yanda sukayi,, zaliha ta ce, "lallai abin mamaki uncle G! kenan, kya k'ara gani indai shine.
:::::::::::::::::::::::::::::::♡ yau takasance alhamis sopy tana Zaune da 'yar kazaginta zaliha suna duba wani book, gurin akwai yawaytar d'alibai suna shan iska, k'alilanne suke karatu, domin yawancinsu duk tare suke da samari suna hira, wani gay yak'araso inda suke, yay musu sallama zalihace kawai ta amsa amma sopy ko kallo bai ishetaba kanta yana ga littafai.
Saurayin ya zauna kusada zaliha, yayinda sopy ta mik'e ta canja gurin zama,, saurayin yabita da kallo, zaliha way yaushe k'awarki zata wayene??
Zaliha ta tab'e baki babu rana jamilu! dan ita ra'ayinta daban dana mutane.
Ya jinjina kai yana fad'in tofa, jami'a gidan bankashi.
Zaliha ta kalleshi ta k'yalk'yace da dariya suka tafa da gayen.
Sopy dake kallonsu taja tsak'i irin wannan abubuwanne yasa bata sakarma zaliha fuska dan ta kula 'yar komai da ruwanka ce, tamai da kanta ga karatunta.
D'alibai sunata shan hirar soyayya agurin, sai sopy tazama saniyar ware, dan bata bama kowane saurayi fuskar kusantar taba,, batada abokin hira sai littafi ko waya, saikuma idan sun had'u da zaliha, ko kuma tayi tayin chatting abinta.
Uncle G! Yabi dukkan d'aliban da kallo cikin bak'in ciki, shikam irin wannan halayyar bata burgeshi, domin aganinsa rashin tarbiyya da kamunkai ne yake kai d'aliban maida makaranta wani lambun masoya, yad'anja tsaki tareda k'ara jingina a jikin motarsa, karaf idanunsa akan sopy dake gefe tana karatu, Yay d'an murmushi gsky tana k'ara burgeshi, dan yanason mace mai kamunkai, da rik'e mutuncin kai, ya lura yarinyar tanada tarbiyya dan baitab'a ganinta da wani saurayiba, ya dad'e yana saka mata ido amma haryanzu baiga wani abun aibu a tareda itaba,, saidai yakula muskilace tafad'a aji.
Yazo zai wuce duk yawancin d'aliban suka shiga gaidashi,, amma ita hankalinta nakan littatafai, ko kuma tanajinsu tadai sharesune oho.
Shima ya wuce batareda ya kuma kallontaba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.