Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 31 of 40

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 20~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸4⃣9⃣🔸🔶

..........Aunty zainab ta wankama fareeda mari, Wanda yasata zubewa awajan dafe da kumatu, cigaba tayi da dukanta tamkar uwarta, dak'yar su aunty Nafisa suka rik'eta, cikin matuk'ar b'acin rai aunty zainab ta ce, "kubarni naci uban wannan mara mutuncin, ita hartanada k'afafun zuwa gidan safiyya, saboda batada mutunci.
Sopy tafito da sauri dan jin hayaniya, yayunta tagani tsai tsaye da alama babu lafiya.
Aunty zainab ta tako har zuwa inda sopy take, tana fad'in wato sopy har kin farka daga magagin cin amana da yaudara irin na fareeda ko, tanuna fareeda da jini yake zuba ta hanci saboda dukan hancinta da aunty zainab d'in tayi, ta ce, "waccan dakike gani bom ce data tarwatsa rayuwarki abaya, kuma inada tabbacin yanzuma zata tarwatsa sabuwar rayuwar dakika kasance aciki, dan ita kaskace rab'u mai jini, data tsotse jinin jikinki saita barki da zallar ruwa, takama kafad'ar sopy ta girgiza tana kuka tana fad'in haba safiyya miyasa kika amince da wadda taci amanarki, miyasa kika amince da wadda tarabu da iyayenta akan d'ana miji, itace sanadin kamuwar mahaifinmu da ciyo mai muni, itace ta haddasa bak'in ciki a family namu wanda bazamu tab'a mantawa dashiba, itace tasa mutane sukema gidanmu kallon masu k'arancin tarbiya, miyasa kika yarda mak'iyyarki wadda bata sonki dan ALLAH, Aunty zainab ta durkushe awajen tana wani irin kuka mai ban tausayi, itama sopyn saita take mata baya, suka rungume juna suna kuka.
Suma sauran sai matsar hawaye sukeyi, fareeda kam tana gefe tana jiyyar kanta, ahaka uncle G! yashigo yasamesu, ya tsaya turus yana kallonsu da mamaki.
Dak'yar ya iya furta tambayar waye ya mutu????.
Gaba d'ayansu suka d'ago kai suna kallonsa, sopy tazo da gudu ta shige jikinsa, ya rungemeta tsam yana lallashinta, bayan kamar minti biyar ya cirota daga jikinsa, ya ce, "Sopy miya farune wai??, ko wanine ya rasu??.
Sopy ta girgiza kai tana hawaye, yasa hannu yana share mata hawayen yana fad'in kukan ya isa haka, fad'amin miyake faruwa??.
Sopy ta nuna masa fareeda da hannu, fuska duk jini da alamun duka, kunsandai farin mutim, koyaya aka tab'ashi sai yanuna.
Uncle G! yadawo da kallonsa wajen su aunty zainab, har yanzu kuka takeyi, aunty Nafisa taje ta d'agota ta rungume, tana bata hak'uri.

Tsawon minti shabiyar, kowa ya nutsu, suna zazzaune a falo, harma Sopy tayi k'arfin halin kawo musu ruwa, fareeda kuma ta wanko fuskarta.
Uncle G! yay musu sallama suka amsa, sannan yad'ora da tambayar abinda yafaru.
Aunty Nafisa ce tasanar masa da komai, ta d'ora dafad'in, mukammu abin yabamu mamaki, dan bamuyi tunanin ganin fareeda ananba, dukda dai agida ana nemanta, saka makon mijinta yaje har gida yafad'ama iyayenmu cewa yasaketa har saki uku.
Uncle G! yaja numfashi sanna ya d'ora da fad'a musu yanda ya samo fareeda har zuwanta gidan da zamanta, dakuma hukuncin dasuka yanke na maidata gida, amma sopy ta ce, "tana jin tsoron hakan, dan bataso akasa fahimtarta, yaci gaba da fad"in amma ina mai baku hak'uri akan kubar fareeda domin tayi nadamar abinda ta aikata, Sopy ta ce, "azuciyarta zadai tayi nan gaba, dan mai hali baya canja halinsa uncle.
Uncle G! ya ce, "kutan bayi Safiyya tunda fareeda tazo gidannan bata tab'a aikata mana wani abu wanda bai daceba, dan haka ina rok'onku kuma ku yafe mata, kamar yanda Safiyya ta yafe mata, inada tabbacin hakan zai taimaka mata wajen k'ara samun gyaruwar halayenta, ku kuma zamo mana 'yan jagora wajen nema mata gafara gasu baba da mama.
Aunty zainab ta ce, "ban katsekaba yaya youseef, amma nasan har yanzu fareeda batayi nadama ba, wlhy nasan tana nan tana k'ulla wasu sababbin makirce2n nata, nasan fareeda sosai, tun muna k'anana nake fuskantar mugun halinta, nasan fareeda tafi shak'uwa da Sopy fiye da kowa acikinmu, amma nafi Sopy sanin halin fareeda, dan Sopy ta yarda da fareeda, kuma batada yawan saka idanu akan d'abi'un fareedar.
Aunty Nafisa ta ce, "A'a, zainab tunda ya ce, "tayi nadama bakuma ta tab'a aikata wani abu dazai shiga tsakaninsuba to yakamata muyafe mata, mukuma yimata addu'ar k'ara samun shiriya.
Nandai sukaita rok'on aunty zainab har ta sakko, ta yafema fareeda, dan saida fareedar ta gurfana agabansu tana neman afuwa, Na ce, "shegiya kamar har zuciyarta.

Yaudai anan suka wuni, Sopy tayi musu abinci mai dad'i da gamsarwa, sukasha hirarsu ta yaushe gamo, sopy ta ce, "aunty Asiya yaushe zaki haihu?, Aunty Asiya tayi murmushi ta ce, "sai watan gobe Safiyya.
Sopy ta marairaice fuska ta ce, "dan ALLAH ki lallab'i uncle kabeer yabar uncle yakaini naga su inna, dan ya ce, "wai saikin haihu zan fara fita.
Aunty hauwa'u ta ce, "A'a bakin koma makarantaba??, Sopy ta zumb'uro baki gaba tana fad'in, to makarantar da ga ita ina nake zuwa,?.
Dariya sosai tabasu, Aunty zainab ta ce, "aii ko autar inna saidai kiyi hak'uri, dan muma duk haka akaimana, ta ce, "tab nikam wlhy nagaji, aii zama guri d'aya tsautsayi inji kifi, suka tun tsure da dariya suna tsokanarta.
Fareeda kuwa tana d'aki ta kume kanta, dan taji zafin dukan, zuciyarta ta ce, "karki damu fareeda dama abu mai daraja ba'a samunshi abanza, sai ansha wahala, inda zaki bini daki2 dana fad'a miki hanyoyin dazakibi ki mallaki uncle G!.
Na ce, "hummm naga wannan 'yar akuyar har yanzu bata san inda duniya ta nufaba.
Gani nai tana zuba murmushi, alamun karatun da zuciyar tata takaranta mata yayi mata dad'i, kuma ta karb'eshi hannu bibiyu.
Lallai idan zaka gina ramin mugunta tofa ka ginashi gajere, dan idan aka samu kus kure tofa kaizaka fad'a ciki.

saida akayi la'asar sannan suka tafi, tareda alkairi mai yawa daga uncle G!.
Bayan tafiyarsu Sopy ta shiga d'akin uncle G! Yana zaune yana duba wasu books, ta zauna gefensa, ya d'ago manyan idanunsa farare tas yana kallonta, tayi masa sassanyan murmushi, ya kanne mata ido d'aya shima yana mayar mata da murtanin murmushin nata.
Ya rufe littafin yajuyo gareta, ta ce, "hubbina ka daina karatunne??, ya jawota jikinsa yana fad'in ai idan kina guri sopyna banida lokacin komai sai naki, kin zamomin magana d'isun da kan kama zuciyata da matuk'ar sauri idan kika kusantota, idan kuma bak'ya kusa tofa zuciyata tana tareda ke, dan gangar jikina kaiwai kike barmini, yakama yatsun hannunta yana wasa dasu, yak'ara kashe murya ya ce, "Sopyna yaushe zaki bani magajinane??.
Sopy tasaka hannu ta rufe fuska dan kunya🙈.................✍🏻

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞 I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 20~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸5⃣0⃣🔸🔶

...........Uncle G! Yay murmushi yana fad'in Sopy sarkin kunya, daga tambayar baby sai aji kunya..
Tayi k'ok'arin mik'ewa zata gudu uncle G! yakuma matseta, ta ce, hubbina aikifa zanje nayi, yaja hancinta yana fad'in ainanma aikin kikeyi, ta ce, "aikin mi nakeyi anan?, ya ce, "na bama youseef farin ciki mana.
Sopy tayi murmushi, ta ce, "uncle wai yaushe zamuje Gurum??.
ya ce, "kinaso mujene??.
ta ce, "emana inaso naje na gaida su gwaggona.
Yay murmushi to shikenan zamuje, amma kibari sainan gaba, dan su aunty hafsat sunce zasuzo ranar juma'a.
Cikin matuk'ar farin ciki ta k'an k'ameshi, ta ce, uncle dgsk kakeyi dan ALLAH?.
YA CE, dgsk Sopyna, sunce zasuzo suyimana kwana biyu, ta ce, harda Aysha?, ya ce, eh harda ita.
Kai wlhy naji dad'i sosai, tatashi tana fad'in bari kaga naje nafara shiri.
Ya bita da kallo yana murmushi, akullum tamkar k'ara masa son Sopy akeyi, yakanji kamar babu mata aduniya sai ita kad'ai, komai na yarinyar abin sone.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.