Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 36 of 40

Suka tafi gidan shiru, dan uncle G! yana masallaci, tazuba abinci taci batareda tajirashiba, ta sha magani tashige d'akinta ta kwanta.
Uncle G! ya dawo yaga bata falo saiya lek'a d'akinta, tana kwance akan gado amma da alama idanunta biyu, dan yaga tana karkad'a k'afafuwa, alamar har yanzu asama take, dazata samu wani dasaita ruburbud'a😜, kamar yanda ta suburbud'i fareedaπŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ‘ˆπŸ».
Uncle G! yashigo jiki asanyaye, yak'araso kusa da gadon ya tsura mata idanu, kallo d'aya tayi masa ta kauda kai gefe, yad'an murmusa, ya zauna kusada ita, yakamo hannunta dake saman ruwan cikinta, yad'an matsasu, tayi burus dashi, ya matso ya juyo da fuskarta gefen dayake, saita runtse idanu.
Ahankali ya furta wai laifin mi nayi sopyna, idan nayi laifine sai asanar dani, wasu zafafan hawaye suka shiga zubowa daga kumatun sopy.
Uncle G! ya jin jina kai, lallai ya yarda da batun uncle kabeer dayace fushin sopy bala'ine, shikam ya shaida yau, yasa hannu yana share mata hawaye, ya dawo da kanta saman cin yarsa yana cigaba da lallashi, amma tak'i saurarensa.
Dole yahakura yaje yaci abinci yay wanka, yayo shirin barci yazo yakwanta kusada ita, yay musu addua dan ita harma tayi barci.
Shiko saiya kasa barcin dan abubuwan dasuka faru d'azune suka shiga dawo masa, gani yake kamar alabarin littafi ko film, ya dad'e bai barciba, saidaga baya ya saceshi shima. .............✍🏻

πŸ’žBilyπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žMrs Abdus'salamπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žI LOVE YOU MY FAN's
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 25~November~2016

πŸ”·πŸ”ΉNI DA AMINIYATA!!! πŸ”ΉπŸ”·

NA BILKISA IBRAHIMπŸ’ž

πŸ”ΆπŸ”Έ5⃣5βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά

...............Tsawon kwana uku kenan amma Sopy tak'i sakin jikinta, kwatata ta daina fara'a, bata shiga d'akin uncle G!, dan idan ta tuno da yanda tasamesu ad'akin shida fareeda sai taji hawaye na kwaranya a idaniyarta, lallai tana ji aranta da uncle G! da fareeda sunyi tarayya tofa da har abada ta barmata uncle G!😳.
Gaba d'aya uncle G! yarasa kanta, tun yana lallashi har yabari dan yafara jin haushinta shima, yayi fushinsa na kwana d'aya ya sakko dan dole yakoma lallashinta.
Yauma tana zaune afalo ita kad'ai ta kurama tv ido,saidai azahiri ba kallon takeyiba tana duniyar tunanine, uncle G! yashigo hannunsa nik'i2 da kaya, kwata2 sopy batasan ya shigoba, dan tunaninta baya tareda duniyarta.
Ya dire kayan a tsakkiyar falon, ya nufo gareta, ahankali ya zauna kusada ita, yajawota zuwa jikinsa, tai figigit alamar dawowa, cikin d'an rikicewa ta ce, "sannu dazuwa, ALLAH bansan ka dawoba.
Uncle G! yay d'an murmushi tareda shafa gashinta ya ce, "yaza'ayi kisan nashigo bayan kina duniyar tunani, ya kuma mayseta ajikinsa yana fad'in sopyna plz yakamata komai ya wuce, ki d'ebi abinda yafaru ki watsashi baya, muci haba da gina sabuwar rayuwa, ki d'auki hakan a matsayin k'addararki ta rayuwa.
Sopy ta zubo da hawaye tak'ara kwanciya luf ajinkin uncle G!, shikuma yana shafata kamar mage, ta ce, "nakan dad'e ban damu da abuba koda yafaru a garenine, amma daga lokacin da'aka kaini mak'ura nakan shiga rud'ani da gushewar farin ciki, tad'ago tana kallon fuskar sa, ta ce, "uncle!! plz ka kaini wajen dazanyi kamar sati biyu, wannan ce kad'ai mafitar dazata mantar dani, rud'anin danake ciki a yanzu.
Uncle G! yay murmushi ya ce, "indai hakan zai sakaki farin ciki tofa zan miki, dama na shirya mana tafiya Gurum tunda makarantarmu mun shiga yajin aiki, tad'ago da sauri tana kallonsa tai saurin fad'in dgsk??.
Ya jin jina kai alamar eh.
Ta ce, "amma baka fad'a mini ba.
Yashafa kanta ya ce, "naga kina cikin rud'anine", yad'ora da fad'in idan kuma bak'ya son Gurum toki fad'i inda kike so sai muje, domin samun farincikin ki.
ta murmusa tareda murza tafin hannunsa, tad'ago tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa ta ce, "aii nafison Gurum fiye da ko ina.
Shima murmusawa yayi ya ce, "ngd da k'aunar dakikema garina.
Tad'an harareshi oh, garinka mane kai kad'ai?.
Yay 'yar dariya ya ce, "sorry garinmu.
Yaudai babu laifi sund'anyi hira, har aka ci soyayya a wajen barci.
Na girgiza kai ina fad'in mata da miji sai ALLAH.

Bayan kwana biyu suka shirya, zuwa Gurum, babu yanda baiyi da'itaba akan suje su gaida su inna ba, amma ta ce, "bazata jeba, har k'ararta yakai wajen uncle kabeer.
Uncle kabeer ya ce, "ya k'yaleta, yasan saboda fareeda ta ce, "baza tajeba", kuma hakan yayi, inko taje tofa sabon fad'a zai tashine.
Uncle G ya ce, "haba aii ta hak'ura, uncle Kabeer yay dariya ya ce, "lallai nakula har yanzu bakasan halin sopy ba, ta hakura ne dan bata ganinta, amma sopy tafi kurma naci awajen fad'a.
Uncle G! yay dariya yana f'ad'in ga k'arfin tsiya, dariya sukayi suduka suka kashe wayar uncle kabeer yana fad'in nidai babu ruwana, kunfi kusa, .

Yaukam tunda safe Gurum tai d'iba, shabiyu a Gurum tayi musu, su gwaggo sunyi farin cikin ganinsu, anmusu tarba mai k'yau, abinci har sopy ta rasa wanda zata ci.
Aysha ta gyara musu b'an garensu.
Da yamma baba yadawo daga gona shima yayi matuk'ar farin cikin ganinsu, yay musu godiyar hidimar dasuka sha da su Libabatu, yasa musu albarka sosai, itadai sopy saijin kunya takeyi.
To haka rayuwa tacigaba da tafiya mai tarin farinciki, dan Gurum tayi musu dad'i, gashi kullum sai aysha ta raka sopy gidajen 'yan uwa da abokan arzik'i, tun uncle G! yana nuna baya so har ya hak'ura.
Yau kwanansu hud'u da zuwa, sopy ta yashi da matsanancin zazzab'i, tun dare take zuba amai, har zuwa safiya, duk jikinta yasaki, saida safe uncle G! ya sanar da su gwaggo.
Cikin hanzari gwaggo tazo b'an garensu, ta iske sopy tanata shek'a amai, ta kalli uncle G! ta ce, "yusufa yakamata kakira mas'ud abokinka yazo ya dubata ko?.
Uncle G! ya ce, "to gwaggo, bari naje naga idan yana nan, gwaggo ta ce, "to ALLAH yasa adace.
Ya fice yana fad'in amin, babu dad'ewa suka dawo tareda mas'ud shima d'an Gurum ne, tare sukai piramary da secondary, ya duba sopy sosai, saiya saka mata k'arin ruwa yatafi dan ya bincika abinda ke damunta.
Karin ruwan da aka saka mata yasatayi barci, gwaggo da uncle G! zaune sun saka sopy Gaba sun zabga tagumi, baba kuma yana daga k'ofar d'aki zaune akan dankari, shimadai yayi shirun, aysha kuwa ta garzaya domin sanar da su aunty hafsat halin da'ake ciki.
Sai wajen karfe d'aya mas'ud yadawo, sannan su gwaggo sun fito, ya mik'ama uncle G! hannu yana murmushi.
Jiki a sanyaye uncle G! yabashi sukayi musabaha, mas'ud ya ce, "my Brother congratulation on your success!".
Cikin rashin fahimta uncle G! yake kallonsa, ya daure ya ce, "d'an uwa ni wane arzik'i nasamu da har zaka tayani murna.
Mas'ud yay murmushi ya ce, "kasamu babban arzik'i wanda wasu da yawa suke nema, harma dani aciki,kasamu k'yauta wadda ALLAH kad'aine yake badawa,kasamu arzik'i mai tarin ni'ima, na samun d'a daga matarka Safiyya!.
Cikin matuk'ar farin ciki ya rungume mas'ud, yana fad'in "Alhmdllhi ALA kulli halin", lallai nayi maraba da samun wannan d'ingimemiyar k'yauta, ina kuma godiya ga sarkin sarakuna, mai so dak'aunar bayinsa.
Uncle G! Yadawo da kallonsa ga sopy yana murmushi, lallai ALLAH yasoshi daba'a zubarmasa da d'a ba wajen dambe.
Sun dad'e suna murna kafin gwaggo ta shigo, itama mas'ud ya fad'a mata, dan uncle G! yakasa saboda kunya.
Dan danan gida ya kaure da murna, harsu aunty hafsat ma sunzo tun d'azu, kowa farin ciki yake zasuga d'an uncle G! Aduniya, gwaggo da baba jisuke kamar yau suka fara samun jika, bare kuma uban ginsami uncle G!, aii jiyake yafi kowa sa'a a wannan rana.
""wannan na sopy ne da uncle G!!!!πŸ‘πŸ»πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ‘ŒπŸ»"".......................✍🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.