Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 28 of 40

Assalamu alaikum, ina godiya ga d'umbin masoya, dasuka turo min sak'on addu'a ga sister na datake asibiti, harma wad'anda basu samu damaba, ngd sosai da addu'arku ALLAH yabar zuminci.πŸ™πŸ»

πŸ’žBilyπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žMrs Abdus'salamπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žI LOVE YOU MY FAN'sπŸ’žπŸ’ž
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 17~November~2016

πŸ”·πŸ”ΉNI DA AMINIYATA!!!πŸ”ΉπŸ”·

NA BILKISA IBRAHIMπŸ’ž

πŸ”ΆπŸ”Έ4⃣6βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά

.........yau har sopy tagama aikin gyaran gidan fareeda bata fitoba, da kuwa kullum tare sukeyi, sopy tagama aikinta tsaf batareda tayi wani tunaniba, ko neman fareedar, bayan ta kammala komai tanufi d'akinta, fareeda na kwance abinta saman gado ta k'udundune da bargo, kallo d'aya sopy tayi mata tashige bayi abinta, dan ita azatonta fareedar barci takeyi.
Tana shiga fareeda ta mik'e, ahankali tafito tanufi dani d'in da'aka cika da kayan break, saida tabi kowanne ta bud'e taga abinda ke ciki, sannan tanufi kicin tana yatsine fuska.
Ta fito hannunta d'auke da robar gishiri, da sauri na lab'e dan kar ta ganni, ta bud'e ta barbad'e soyayyen dan kalin dashi, ta kuma bud'e sauran ta zuba har cikin ruwan zafi, da sauri ta maida ta koma d'akin ta kwanta kamar yanda take da.
Sopy tafito tana 'yar wak'arta ta, ta zauna tayi kwalliya mai tsari, wando da riga tasaka na fakistan, rigar tatsaya mata iya cinya, tayi k'yau sosai.
Tana shirin fita fareeda ta tashi tana wani mik'a alamar yanzu ta tashi a barci, sopy ta kalleta tana fad'in fareeda ince dai lafiya ko??.
Fareeda tad'an yatsina fuska ta ce, "mikika ganine sopy??.
Sopy ta girgiza kai, babu abinda nagani, naga yau kin dad'e baki tashiba ne kawai.
Fareeda ta zuro k'afafubta k'asa tana fad'in wlhy jiya nadad'ene ina nafikar dare shiyyasa yau namakara, na lurama har kin gama aiki ko??.
Sopy ta jin jina kai tana murmushi, aii babu damuwa, garama da kika huta, tai waje tana fad'in ki shirya muna jiranki a falo.
Fareeda ta rakata da harara, tana fad'in 'yar rainin wayo, aii na daina tayaki bautar gidannan, nafiso nima nashigo amatsayin matar gidan, dan bazanta wahalar banzaba.

Sopy kuwa d'akin uncle G! tanufa, tad'an zauna gefen gadon kusada shi tana shafa fuskarsa, ahankali ya bud'e idanu akanta, suka sakarwa juna murmushi, ya mik'o mata hannunsa wai ta tadashi, takama hannunsa tana fad'in ALLAH yasa na iya tada kai uncle d'ina!, dan kayi nauyi dayawa, yajawota tafad'o jikinsa, yasa hannu biyu yay mata zobe, cikin kunnenta ya ce, "nine mai nauyin ko??.
Ta d'ago tana kallon fuskarsa sukayi murmushi, ta sumbaci k'irjinsa, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda k'ara rungumeta.
Cikin sanyin murya ta ce, "my youseef tashi kayi wanka ko??, yad'an lumshe idanu, cikin shagwab'a ya ce, "saidai idan zakimin da kanki??, tad'an zaro idanu waje tana fad'in nifa nayi wanka aii saina b'ata jikina.
Ahankali yatashi da'ita zaune shima yatashi yana mata wani sihirtaccen kallo, cikin sanyin murya ya ce, "kinyi k'yau sopyna.
Tayi murmushi tareda fad'in nagode hubbina.
Ya ce, "woow nice name, daga yau haka za'a ringa kirana ko??, tai wani walay da idanu ta ce, "inhar kana buk'ata??.
Ya mik'e yana fad'in aii namafi kowa buk'ata.
Takama hannunsa suka nufi bayi, taimasa wanka fas sannan suka fito, ta shiryashi cikin k'ananun kaya, dan yau babu aiki.
Falo suka fito sunata zabga k'amshi mai dad'i, fareeda na zaune itama taci kwalliya cikin atamfa aiket da riga, sopy tabita da kallon dan ganin kwalliyar datayi.
Fareeda ta basar daga kallon da sopy take mata, ta d'an zamo daga kujerar ta ce, "yaya youseef ina kwana??.
Uncle G! ya amsa da lfy lao fareeda, kin kwana lfy??.
Ta ce, "Alhmdllih.
Ya ce, "masha ALLAH.
Dani suka nufa domin yin break, sopy tafara k'ok'arin had'ama uncle G break, saida ta zuba masa komai sannan ta turama fareeda kamar yanda ta saba.
Uncle G yaja filet gabansa yana fad'in yauwa 'yar albarka, laumar farko dayayi ya kume azaune kamar gunki, dan jin wani aza babben gishi har kwa kwalwarsa, yaja kofin shayun da sauri ya kurb'a domin neman sauk'i, amma saidai kash shima shayin haka yake.
Fareeda tana kallonsa, amma sopy bata lura da halin dayake cikiba, dan hankalinta yana kan zuba abincinta.
Uncle G! ya d'ago idonsa dayayi d'anja yana kallon asopy, sopy ta d'ago suka had'a ido saita sakar masa murmushi, amma ganin yanda fuskarsa ta canja sai jikinta yay sanyi ta ce, "hubbina yayadai???.
Ya daure ya ce, "ci abincin kiji.
Ta d'iba ta kai baki, dan ita azatonta yayi dad'ine sosai, jin gishiri zauzau yasata d'agowa da sauri tana gallonsa, shima ita yake kallo, fareeda da dad'i ya kashe ta, ta d'iba takai baki, da sauri ta zubo dashi a hannunta ta ce, "Sopy yaya haka??.
Sopy ta maido da kallonta gareta, zuciyarta sai bugawa take da sauri2, wasu hawaye masu zafi suka zubo afuskarta.
Amamakin fareeda saitaga uncle G! ya matsa da kujerarsa kusada sopy, ya kamo hannunta ya rumtse anasa, yasa d'ayan hannun yana share mata hawayen, cikin sanyin murya ya ce, "sorry safiyya!, karki damu, aii kowa yana kuskure a rayuwarsa, tunda haka bata tab'a faruwaba dole muyi miki uzuri.
Sopy ta kwanto da kanta saman cinyarsa tana shashshekar kuka, ta ce, "ngd uncle d'ina daka fahimceni.
Ahankali yake buga bayanta kamar wata jaririya, ya ce, "to ya isa haka nan, kinsan bana son kukanki.
Ta d'ago suna kallon juna, sukaima juna murmushi, yasa hannu ya kuma sharemata hawayen, ta ce, "uncle bari naje na sama mana wani abun mai sauk'i.
Ya jin jina kai yana murmushi.
Fareeda tabisu da kallo cikin matuk'ar bak'in ciki da haushin rashin samun nasara, mik'ewa tayi tabi bayan sopyn zuwa kichin.
Abu mai sauk'i sukayi, dukda sopy ce rabin girkin, dan fareeda bak'in ciki ya hanata yin wani aikin kirki.
Yana zaune afalo yana kallo suka fito, ya tashi yana fad'in yauwa sannunku, dani suka zauna suna break d'in, uncle G! sai kod'a abincin yake dan sopy ta saki jikinta, dan har yanzu bata cikin walwala, wai abincin yayi dad'i, harma yafi na kullum.
Sopy tayi murmushin k'arfin hali, ta ce, "uncle kana dai fad'ane kawai.
Ya ce, "da gsk nakeyi sopyna, ki kuma tambayi fareeda ma, yafad'a yana kallon fareeda datakeji kamar ta tashi tabar wajen, tai saurin k'irk'iro murmushi, cikin daburcewa ta ce, "ALLAH sopy da dad'i.
Sopy tayi murmushi ta ce, "to shikenan ngd.

Bayan sun gama, uncle G yafita, sopy kuma tanufi d'akinsa dan ta gyara.
Fareeda tana zaune abin duniya duk ya isheta, dan taso ace uncle G! ya hau kan sopy da masifa, taja kwafa tana fad'in aii idan kunsan wata bakusan wataba, ta mik'e tanufi d'aki.

Sai dare uncle G! yadawo, sopy taje ta taroshi kamar yanda tasaba, suka shigo falon suna dariya, fareeda dake zaune a falon tana kallo tad'anja k'aramin tsaki, amma basujiba, tayima uncle G! sannu da zuwa, ya amsa tareda tambayarta ya gida, ta ce, "lfy lao.
Sopy taja hannunsa suka nufi d'akinsa, tadawo ta d'aukar masa ruwa mai sanyi takai masa, ya karb'a yasha yana fad'in sannu 'yar albarka.
Ta karb'i kofin ta ajiye tana murmushi, ta ce, "sai wanka ko?, ya ce, "e, amma fara bani ledar can dana zo da'ita.
Ta d'akko masa, ya ce, "bud'e ki gani mana.
Ta bud'e tana dubawa, manyan hijjabai ne guda goma, sai nik'af guda uku, ta kalleshi tana fad'in uncle wannan fa??.
Ya ce, "nakine, dan gobe zaki koma makaranta, kuma bana buk'ata kowane wawa ya kalle mini matata, dan tawace ni kad'ai.
Sopy tayi dariya, hubbina kishinka yayi yawa wlhy.
Yay murmushi, oho, kodai mizakice kice, nidai bana son arink'a kallon min matata.
Ta ce, "to ngd sosai mijina, abin k'aunata.
Yay dariya to saka nagani!!.
Ta saka, har k'asa yakai mata, dan wasuma suna d'an jan k'asa, tasaka nik'af d'in shima, ya kalleta ya tuntsure da dariya, wai kamar ojuju.πŸ‘½
Itama dariyar tayi ta ce, "aii kaine dai ka maidani inma ojujunne.
Ya shige bayi yana fad'in gara dai haka aii.
Saida yay wanka ya shirya sannan sukaje falo, sukaci abinci, yau basuyi wata hira mai tsawoba suka tashi, dan sopy tana d'okin komawa makaranta gobe.
Koda sukaje d'akinma ba barcin sukayiba, saida suka kashe juna da soyayya mai tarin ladaπŸ™ˆπŸ‘πŸ».
Fareeda kam ana gado anata juye juye dan babu mahad'i😜😜.................✍🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.