Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 27 of 40

๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 7~November~2016

๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท

NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž

๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ4โƒฃ4โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

............fareeda dake lab'e tana kallonsu sopy takoma da sauri tazauna danganin sopy tanufo palon tana dariya.
Sopy tashigo da sallama, fareeda taisaurin kauda komai azuciyarta ta amsa cikin fara'a, sopy ta ce, "tashi muyi break ko 'yar uwa, fareeda ta ce, "to, suna break suna hira sama2, dan yanzu babu wani sabo tsakaninsu, kunsan idan karabu dazama da mutum hakan yana faruwa, bare idan sab'ani yashiga tsakaninku.
Bayan sun gama break sopy tanufi d'akin uncle G! domin gyarawa, fareeda! ta k'urama hoton uncle G! dake palon idanu, wani kuma shida Sopy! suna murmushi, a zuciyarta ta ce, "sopy kedai kullum mai sa'a ce, inama ace............. ..., ๐Ÿ˜ณnad'an zaro ido ina fad'in fareeda!! inama ace mi?????????????????.๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

Amakaranta kuwa tunda uncle G! yay fakin d'alibai sukayo caa akansa, ya fito daga motar fuskarsa cike da fara'a, sukansu d'aliban fara'ar tasa tabasu mamaki, nan dai suka shiga gaisheshi da k'ara tayasa murnar aurensa.
Shima gidiya yayita musu da halartar d'aurin aurensa dasukayi, dakuma tanbayarsu karatunsu.
Sukace komai nomal amma sunyi missing nasa sosai, shima ya ce, "yayi missing nasu.
Wata ta ce, "uncle G! ina amarya safiyya!!?, saida yad'an murmusa sannan ya ce, "tana gida nabarota, wata ta ce, "bazata dawo school baneba??, ya ce, "zata dawo amma saita k'ara hutawa, gaba d'aya gurin suka sa dariya, shima yayi gaba yana dariyar.
A office ma bata sake zaniba, dan d'alibaine sukaita yimasa cincirindon taya murna harda malamai 'yan uwansa, wasuma gulma takawosu acikin d'aliban.
Dak'yar ya samu kansa zuwa sha biyu yashiga lecture, saidai gaba d'aya kewar sopy saita isheshi, ya kalli gurin zamanta yaga kamar zaiganta yanzu, sukansu wasu d'aliban sun harbo jirginsa, dan duk sanda ya kalli gurin daya fara ganinta saiya yi murmushi, dahaka dai yagama musu lecture d'in yafito, suka shiga gulmarsa akan kallon gurin zaman sopy dayayi tayi.
Daga nan wani ajin yaje yagabatar da lecture, sai karfe biyar na yamma yanufo gida, cikin zumud'in son ganin sopy.

Lokacin daya iso sopy tagama gyara gidan, tayi wanka tad'au kwalliya ta d'aukar hankali, ita kanta fareeda tana mamakin yanda sopy ta ke kwalliya yanzu, suna falo suna hira taji hon d'in motarsa, da sauri tatashi taje tabud'e masa get.
Tun yana mota yake sakar mata murmushi itama tana maida masa murtani, yay fakin takaraso bayan ta rufe get d'in, dakanta ta bud'e masa mota, maimakon yafito saiya jawota cikin motar ta zauna kan cinyarsa.
Ya kura mata manyan idanunsa masu haske yana wani murmushi mai k'ayatarwa, ta hure masa idanu tana murmushin itama, suka tuntsure da dariya, ta ce, my uncle kadawo lfy, saida ya sumbaci kuma tunta sannan ya ce, "lfy lau nadawo, saidai zuciyata tana nan gangar jikinace a makaranta.
Sopy tay wani far da idan ta ce, "da gsk uncle d'ina. Ya lumshe idanu cikin wani yanayi, domin farin nata yatafi da imaninsa, ya bud"e ahankali yana kallonta, sai dai yanzu idonsa yayi d'anja ya ce, "my sopy ina k'yaunarki dayawa, nakan rasa inda zansa sonki, ashe dama haka ma'abota soyayya sukeji??.
Sopy ta shafa k'irjinsa tana fad'in nima ina sonka my uncle d'ina har nakan rasa yanda zan musalta son naka.
Ya rungumeta tsam ajikinsa yana wani fidda numfashi dak'yar, sunkai tsawon minti biyar ahaka, sopy ta daure ta ce, "uncle mushiga ciki ko?.
Ya d'agota yana murmushi, ahankali yace kinsan ALLAH nama manta a inda muke, sopy ta tashi daga jikinsa tana 'yar dariya, ta zagayo tad'ayan gefen ta d'auki jakarsa ta aiki, shikuma ya bud'e baya ya d'auki wata leda suka jera zuwa cikin gida.
Fareeda tana zaune suka shigo, tai masa sannu dazuwa sannan ta gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, ya kalli sopy yana murmushi ya ce, "ashe ma mara lafiyamu ta warke?, sopy tayi murmushi batareda tace komaiba.
Taja hannunsa tana fad'in sir muje kayi wanka kazo kaci abinci.
Uncle G! ya harareta ya ce, "waye sir d'in?, sopy tayi 'yar tafiya zuwa k'ofarsa sanna ta juyo ta ce, uncle G!! mana.
Da sauri yanufota, itakuma tashige cikin d'aki tana dariya.
Fareeda tabisu da kallo tana ayyana abubuwa dayawa azuciyarsa, ahan kali ta ce, "dama ace................saikuma tayi shiru, ๐Ÿ˜ณnakuma zaro ido waje, wai ita wannan mitakeson fad'ane?????.๐Ÿ˜๐Ÿ˜
Ad'aki kuwa uncle G sunata zagaya d'aki da sopy yana son kamota, amma tak'i yarda, can yasa k'afa ya tad'ota suka fad'a kan gado suna dariya, yaymata rumfa da faffad'an k'irjinsa ya ce, "waye sir d'in??.
cikin dariya ta ce, "sorry bafa dakai nakeyiba.
ya ce, "dawa kikeyi?, ta ce, "to d'agani zan fad'a.
ya ce, fad'i ahaka mana.
Ta ce, "wlhy kacika nauyi zaka fasa min ciki.
Aiko yau sai dai cikin naki ya fashe dan bazan d'agakiba saikin fad'a.
Sopy ta ce, "wayyo ALLAH na inna kizo ki taimakeni, uncle G! Ya tuntsure da dariya, aii yau saidai ki kira duk wanda zakai kira amma babu alfarma.
Ta ce, "ALLAH kanada nauyi fa, ya ce, "kedai kika sani, batai auneba taji yana shafata, zaitai magana ya had'e bakinsa da nata, saida ya cakud'ata yanda yakeso sannan yabarta.
Ta mik'e tana kallon kayanta dasuka cuccurkud'e, ta shagwab'e fuska tana f'ad'in duk kayimin wani iri da kaya, d'aukarta yayi cak yay bayi da ita, tanata watsal2 da bashi hak'uri, amma bai sauraretaba, yadireta a bayin yarufe.
Ganitai ya hau cire kaya, tasa hannu ta rufe idonta, yay dariya yana fad'in k'yadai jidashi, amma yau dole kimin wanka shine hukuncinki.
Sopy ta durkushe kasa ido arufe dan ganin ya cire kaya gaba d'aya, ruwa ya d'iba yazuba mata ajiki, ta bud'e ido da sauri tana kallonsa, yay mata gwalo๐Ÿ˜œ, doledai tayi masa wanka, itama yay mata suka fito๐Ÿ™ˆ............................โœ๐Ÿป

๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 17~November~2016

๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท

NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž

๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ4โƒฃ5โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.........Rayuwa mai dad'i akeyi agidan uncle G, yana nuna mata soyayya irin wadda kowace mace take buk'ata a rayuwar aurenta,.
"dan gsky mazan mu na hausawa basu cika nunawa matansu soyayya ba, sukan fifita neman kud'i akan matansu, wani idan ba yazo biyan buk'atarsa ba, matarsa bazata tab'a rab'ar jikinsa taji dad'iba, inko tad'an rab'u jikinsa saiyace bata da kunya, gsky hakan ba dai dai bane, mu mata 'yan son soyayyane da tattali, muna son anuna kulawa akan mu, yakamata mazan mu su gyara, ba ayita nuna miki soyayya awajeba saikinzo cikin gida kiga sab'anin haka, wannan yanasa mata hange hange, ALLAH yasa mugane amin".

Yauma takama weekend dan haka uncle G! yana gida, su duka suna zaune afalo har fareeda, sopy na zaune saman doguwar kujera, uncle G! yana kwance ya d'ora kansa bisa cinyarta suna kallon wani hausa film, fareeda ma na zaune a kujera mai zaman mutum d'aya, itakam ba kallon ne agabantaba, dan taraba hankalinta gida biyu, rabi a kallon tv, rabi a kallon su sopy.
Uncle G yad'ago idanu yana kallon sopy dake shafa kansa ahankali tana kallo, yay d'an murmushi tareda saka tafin hannu ya kare idanunta daga kallon tv.
Cikin shagwab'a ta ce, "kai uncle neman magana ko?, ta cire hannunsa ta rik'e, yay dariya tareda fad'in to aii kece naga gaba d'aya kinbama tv amanar idanuwanki, ni koma kallona ba'ayi.
Sopy ta tuntsure da dariya ta ce, "o, kishi kake da tvn??
Ya d'anja hancinta yana fad'in indai akan Sopyna ne tofa komaima zan iya kishi dashi.
Sopy ta shafa sajen sa daya kwanta luf luf akan kumatunsa, suka zurama juna idanu tamkar zasu cinye kansu.
Sopy tafara janye nata tana d'an murmushi cikin yanayin kasala, shima saiya lumshe nasa idanun yana murmushi.
Fareeda dake kallonsu ta runtse idanu hawaye suka zubo, tai saurin sharewa da d'an kwalin kanta, tana mamakin yanda kullum Safiyya take kasan cewa asamanta, tunda take bata tab'a wuce safiyyaba, gashidai tafi sopy k'yau nesa ba kusaba, gata fara dirarriya, amma tun suna yara, sai sopy ta samu abu kafin ita tasamu, kuma kota samu saitaga na sopy yafi nata, da tana ganin idan ta samu Abdul kamar tawuce da sanin sopyn ne, amma sai sopy tazo ta auri wanda yafi Abdul komai na rayuwa, k'yawu, ilimi, kwarjini, aji, iya soyayya, da tarin abubuwa masu yawan gskg, itakam saitaga kamar batada sa'a a rayuwarta, "muguwar zuciyarta mai sakata a hanya mara b'illewa ta ce, "mata karkice haka, yakamata ki gwada sa'arki akan uncle G,๐Ÿ˜ณnace, "itakuwa wannan tana cikin hankalinta๐Ÿ˜Ž?????.
Ta kai kallonta garesu, ta kula sunma manta tana cikin falon, dan babu abinda sukeyi sai shan sharafin soyayyar su, uncle G ya matso da bakinsa kusada na sopy, yana nufin suyi kiss, da idanu ta nuna masa fareeda, ya dafe goshi yana fad'in kes.
Sopy tayi murnushi, cikin tsokana ta ce, "irinku d'aya aii.
Yay saurin kallonta, ya ce, "dawa??.
Tayi dariya mai k'ayatarwa ta ce, "da...........sallamar dasukajine yahanata k'arasawa, suduka suka maido kallonsu ga k'ofar.
Su Nadiya suka shigo da sallama, su biyarne, uncle G! yatashi zaune yana fad'in lallai yau munada manyan bak'i, sannunku da zuwa.
Sopy taje ta rungume Nadiya, da sauran yammatan, harda zaliha, suka k'araso cikin falon.
Kowacce ta rusuna ta gaida uncke G!, ya amsa cikin fara'a, ya ce, "zuwa babu sanarwa?
Sukayi dariya tareda fad'in aii muna son bama sopy mamakine.
Ya mik'e yana fad'in ayko kun bata, sannunku da zuwa.
Sopy ta dire tire agabansu, cike da kayan motsa baki, nan suka zauna anata shan hira, da labarin makaranta, fareeda dai babu abin fad'a sai binsu take da idanu.
Zaliha! ta ce, "kai Safiyya kinyi k'yau wlhy, kodai mun samu ne??.
Sopy! tad'an harareta cikin wasa ta ce, "kun samu me???.
Suka tun tsure da dariya, ayeesh! ta ce, komun samu baby mana, ikilee! tai saurin cewa kema daga gani kinsan mun samu aii.
Sopy ta ce, "kudai wlhy 'yan iskane, nidai babu ruwana.
Ridallah! ta dafa kafad'ar sopy tana fad'in, barsu sopy!, suma nanda wani lokaci zaizo kansu aii, indai cikine, Nadiya! ta ce, bar 'yan iska, ALLAH yasa uncle G! yajisu.
Sopy ta ce, "aii nasanma yana jinsu Nadiya.
Gaba d'aya suka zaro idanu suna fad'in da gske yana jinmu???.
Sopy ta tuntsure da dariya tana fad'in matsorata, nandai sukaita hirarsu da dariya, wadda fareeda tazama 'yar kallo, dan duk sun wuce da ajinta.
Uncle G! yafito cikin k'ananun kaya yanata zabga k'amshi, sopy ta bishi da kallon tuhuma, shima ya fahimci mitake nufi, dan haka ya d'an murmusa, sannan yabi su ayeesh da kallo ya ce, "kuna nan ko har yamma??.
Suka ce, "da anyi la'asar zamu tafi, ya ce, "okey babu damuwa harna dawo.
Ya maida kallonsa ga sopy data had'e rai kamar zatayi kuka, ya ce, " 'yammata ya dai??, sopy ta turo baki gaba ta ce, "wai ina zaka???, yay murmushi, wajen budurwata zani hira.
Da sauri ta kalleshi, idanunta suka ciko da kwalla ta ce, "wlhy to ban yardaba, aii kai kace yau babu inda zaka, tazo ta kwace key d'in motar, takoma saman kujera ta zauna, suko su ikilee sai kunshe dariya sukeyi.
Ahan kali yatako yazauna kusada ita, ya sak'alo hannunsa ta bayanta ya tallafota zuwa jikinsa, ya ce, "sorry my sopy, wasa nake miki, ALLAH wajen kabeer zanje.
Ta kalleshi tana hawaye, to kabari anjima saikaje, yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce, "A'a kiyi hak'uri naje yanzu, tunda kunada abokan hira, nima sainaje muyi hira da uncle kabeer, aii bazan dad'eba.
Ta kuma turo baki, amma aii cakayi sai la'asar zaka dawo, yad'n had'eta da jikinsa yana murmushi, A'a, yanzu nafasa anjima kad'an zan dawo, ta ce, "da anyi azahar, ya ce, "nayarda, ya kama hannunta yana fad'in tashi ki rakani.
Suna fita ya rungumeta tsam ajikinsa, cikin kunnenta ya ce, "sarkin shagwab'a, kinata zuba shagwab'a agaban su Riddallah ko???.
Ta b'oye fuskarta a k'irjinsa tana fad'in aikaine kasa nayi, ya sumbaci goshinta toshikenan saina dawo, dan idan nabiye miki bazan fitaba, yashiga mota suna dariya.
Bayan tafiyarsa ta dawo falon, su zaliha suka shiga tsokanarta, way irin wannan shagwab'a haka, sopy ta ce, " 'yan sa ido, kwa gaji kubarmu, gaba d'aya suka shek'e da dariaya, banda fareeda data maida kanta kan tv.
Anan suka wuni, sunsha hira sosai, dazasu tafi sopy tabasu kayan kwalliya acikin kayan lefenta, suka tafi suna godiya, da ajandar zata shigo makaranta ranar litinin....................โœ๐Ÿป

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.