Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 20 of 40

To yaudai lefe ya iso na sopy, mota guda muta nen GURUM sukayo domin kawo lefen Safiyya.
Akwati uku da karami na sama, babu laifi uncle G! yataka rawar gani, dan lefennan saidai mak'iyi amma yayi atalauce ba a sarauceba, anyi musu tarba ta mutunci, irin wadda suka tabbatar da sunzo gidan karamci, sun kuma tabbatar d'ansu yasamu d'iyar gidan tarbiyya,agidansu fareeda aka amshi lefen dan babanta ne zai d'aurama Sopy aure, aka had'a musu shatara ta arzik'i sukatafi, suna yabon wad'annan muta nen kirki.

Sopy tagama shirinta tsaf, tafito tana fad'in inna nashirya bari natafi kafin su cinyeni da masifarsu, bakamar aunty Nafisa sai bala'i takemin ina b'ata musu lokaci.
Inna ta ce, "to adawo lfy, kuma aii sunfiki gsky tun yaushe suke jiranki amma kina d'aki kina lank'andi, aii mijinki yaga takansa, mutum yay ta abu kamar kwai yafashe masa aciki.
To yi hak'uri inna bari natafi ina k'ara b'ata lokaci.
To ki gaishesu, kicema yayar taku gobenfa sutaho da wuri dan ayi aikin cin-cin d'innan agama da wuri.
To inna zan fad'a mata, tatafi tana dariyar inna, tunda bikinnan yamatso kullum tana kan aikin abubuwa bata ko hutawa .

πŸ”ΆπŸ”Έ3⃣1βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά

..............Da sallamarta tashiga gidan, suduka suka hauta da jaraba, aunty hauwa'u ta ce, " 'yarrainin wayo, kin zauna kinata yan kwana mu, saikace mu zai amfana, gwarama ki nutsu dan wannan mijin naki d'an kwalisa gara kije masa zam zam d'inki, ki rik'e abinki tunkafin wata takwace miki, irin wad'anna rubibinsu akeyi.
Sopy ta tab'e baki, nidai baruwana, dan tun wurima idan wannan zancen zakumin na koma, aunty asiya matar uncle kabeer ta tuntsure da dariya, barsu d'iyata wad'annan yayun banzane zoki zauna, aunty nafisa ta ce, "karma tazauna aii ita zai amfana bamuba, hakadai sukaita tsokanar sopy tana musu shagwab'a.
Gyarata suke kamar babu gobe, tundaga jikinta harzuwa inda ba'a fad'aπŸ™ˆ sunsha gyara, zata zauna agidan auty Nafisa dan suci gaba da gyarata, tunda bawasu k'awaye garetaba wad'anda zasu takura mata.
Bata zuwa ko'ina daga d'aki sai tsakar gida, kunji 'yar gatan auntys d'inta, wayartama ankarb'a ankashe, hankalin uncle G! Duk yatashi yanaso yaganta kodan su tattauna amma hakan tak'i samuwa.
Ya kira uncle kabeer ya tambaya?.
Uncle kabeer ya ce, "lafiyarta k'alau wlhy, nima haka nemanta nake amma tak'i yarda naganta, way tana wani gida b'oyo.
Tofa, uncle G! Yafad'a, to watake b'oyemawa??.
Uncle kabeer ya ce, "agonta mana.
Uncle G! Yay dariya to shikenan tunda dai lfy ai da sauk'i, amma yakamata kazo gobe mu had'ufa.
Okey to badamuwa, zuwa k'arfe hud'u zan shigo insha ALLAH.
TO ALLAH YAKAIMU.

yau k'unshi amma babu amarya, inna sai fad'a takeyi akan b'oye Sopy amma sunk'i fito da'ita saidai subata hak'uri, can gidan aka kai mai k'unshi tamata ta'iya sosai wlhy karkuga yanda Sopy tayi k'yau kamar ba'itaba, jikinnan yasha gyara, Nadiya kad'ai tasan inda take, dan ita take kula da abinda yashafi k'awayensu na makaranta da wanda sukayi secondary tare.
Sai a daren d'aurin aure aka dawo da sopy gidansu, inna ta rud'e daganin k'yawun da sopy tayi, sai latsa jikinta take tana fad'in kaga yara da dabara mikukaima auta na ne tayi haka?.
Su aunty asiya sai dariya suke ma inna.
Inna ta ce, "A lallai dole nabaku tukuyci dan gyaran dakukaima autata yayi.

MASU IYA MAGANA SUKANCE RANA BATA K'ARYA SADAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA, to haka kuwa wannan ranar take ga uncle G! da Sopy.
Ayau dai and'ara auren Youseef Hussein Ahmad da Safiyya Ibrahim kabeer, karkuso kuga wankan shaddar da ango yayi, yayi kyau matuk'a, da yawan d'alibansa da malamai 'yan uwansa sun halarci d'aurin auren, mutanen GURUM kuwa aii ba'a magana, matasan garinsu d'ai d'aine basu zoba, sai washe baki yake dan farin ciki wasuma bai sansuba, lallai naga taron gagarimin d'aurin aure, abin sai wanda yagani.
Dak'yar na iya nemo muku amarya sopy, itamadai taci gayu cikin wata atamfa mai k'yau, idan natsaya bayyana muku kwalliyarta sai nacika littafin, amma dai tabbas ta had'u tamkar zata gasar sarauniyar k'yau, tana zaune itada k'awaenta agidan su fareeda, dukkanin 'yan professional writer da Zumunta sunje, sunkumayi rawar gani wajen mik'awa Sopy gudummawa, canna hango Hauwa lele😘 kusada amarya, to sopy saimuce ALLAH yasanya alkairi.
Wajen k'arfe hud'u aka shirya amarya domin kaita garinsu uncle G!, dan sai ankaita can sun gama bikinsu, daga baya sai angonta yadawo da ita gidansu dake nan kano.
Sopy sai kuka take, dan iyayene suka zagayeta ana mata fad'a da nasiha, irin wadda akema amare, "sai dai wasu amaren basa d'aukar irin wannan fad'an saboda kunnen k'ashinsu", to ita dai sopy da alama komai yana zama a kwakwalwarta.
Da haka dai aka d'ungunma da amarya zuwa GURUM dake acikin k'aramar hukumar Tsanyawa, tareda gayyar 'yan uwa da abokan arzik'i, a k'awayenta Nadiya ce kawai taje, muma dai munbi ayari nida gayyar 'yan group d'ina dan kar abamu labari...................✍🏻

πŸ’žBilyπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žMrs Abdus'salamπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žI LOVE YOU MY FAN'sπŸ’žπŸ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 30~October~2016

πŸ”·πŸ”ΉNI DA AMINIYATA!!!πŸ”ΉπŸ”·

NA BILKISA IBRAHIM πŸ’ž

πŸ”ΆπŸ”Έ3⃣2βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά

.........A garin GURUM su Sopy sun sami tarba mai k'yau, daga dangin uncle G!, Suma sunada kirki, ananma biki aka d'ora, da daddare matasa suka warware kid'in daya bama dangin sopy sha'awa, atak'aice an dai sha shagali.
Washe gari bayan sallar azuhur dangin sopy sukayi haramar komawa kano, bayan an k'ara yima amarya nasiha da jan kunne akan sirikanta da dangin mijinta, suka tattaro suka taho, aka baro amarya tana kwasar kuka.
Da k'yar gwaggo ta lallasheta dan ad'akinta suka barota, daga k'arshe gwaggo ta lallab'ata tayi barici, kunga sirikan kwarai masu tattalin matan 'ya'yansu.
Libabatu ta gyara b'angaren da su sopy zasu zauna kafin sutafi, wato b'angaren uncle G! Kenan, acan gefe yake akatange babu ruwanta da sirikanta saidai idan sun shiga, gyara sosai tayi ma b'angaren, ta amshi turaren wuta wajen gwaggo taje takunna, tak'ara da da wasu turarurrukan data gani ad'akin, azuciyarta ta ce, "oh ni liba, kaga d'akin yaya kamar na mace, nan dai tagama tafito.
Uncle G! Kuwa bayan yagama hidimar sallamar bak'i masu tfy, saikuma yashiga sabgogin sallamar 'yan uwa da abokan arzik'i dake nan, dakuma mammaida kayayyakin da'aka aro na mutane.
Sai gab da magriba aka maida Sopy b'angarenta, aunty hafsa da kanta ta had'a mata ruwan wanka, Sopy ta ce, "nagode aunty!, aunty hafsat tayi murmushi bakomai k'anwata jekiyi wankan, dan muma tafiya zamuyi, lubabatu nacan tana jirana, sai da safe.
" Sopy ta ce, "to ALLAH yakaimu.
Bayan fitar aunty hafsa Sopy tashiga wanka zuciyarta cike da tunani iri-iri, tagama wanka tafito sukayi kicib'is da lubabatu, lubabatu ta ce, "to amarya muzamu gudu gida, sai gobe nazo cin kazar amarci, kifa ragemin.
Sopy tayi d'an murmushi ta ce, "to.
Libabatu tana tafiya sopy tashiga d'akin, tabi d'akin da kallo babu wani tarkace, katifa ce k'atuwa an lailayeta da zanin gado, sai wardrobe ta zuba kaya itama k'arama, sai kujera doguwa a gefenta akwai firij, saikuma wani tebir da kujera agefensa cike yake da littatafai, da alama library d'in uncle G! Ne, ba laifi d'akin yayi k'yau a talauce ba a sarauceba.
Ta zauna tashafa mai tayi kwalliya mai d'an sauk'i, wata atamfa tasaka siket da riga, sun kama jikinta sosai, ta ja k'aramin tsaki nikam bana son kaya su matseni, amma na lura duk haka aunty hauwa'u ta d'inka min kayana.
Haka ta zauna tana gyaran kai tana mitar d'inkunan, nace ashe Sopy tanada gashi ba laifi, dan dai tana b'oyeshine, tagama ta gyara gurin, sannan tahau sallah, bayan ta idar ta zauna agurin har aka kira sallar isha'i, ta tashi tayi.
Ta cire hijjabin kenan tanufi waje akwatin ta dan d'aukar k'aramin hijjabi wanda baikai girman wanda tayi sallarba.
Uncle G! Ya shigo d'akin da sallamarsa, Sopy tarikice tarasa inda zata dosa, wajen akwatin ko kuwa wajen hijjabin data gama sallah yanzu?.
Shima uncle G! Tsaye yake kam cikin farar shadda k'al yaukam harda hula, sai bulbula k'amshi yakeyi, fuskar nan tasa fayau da annurin angwanci, ya kasa koda motsi dan d'imautuwa da surar Sopy, ya tambayi kansa? wai dama haka sopy take da diri da cikakkiyar sura ta d'aukar han kali, lallai dolene ya godema ALLAHn daya halicci wannan k'ak'yk'yawar sura.
Ahankali ya k'arasa gareta, tasaka hanu tana kare k'irjintaπŸ™…, ta rintse idanu danjin uncle G ya mannata da jikinsa, cak ya d'auketa ya dire saman kujera, shima ya zauna, kallonta yakeyi sama da k'asa kamar yau yafara ganinta.
Itako kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta, ta daure ta ce, "ina yini?, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda kama hannunta ya r'intse anasa.
Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrrrrrr, yaune rana ta farko da namiji ya tab'a kama hannunta, ta runtse manyan idanunta.
Uncle G! Yay murmushi, cikin muryarsa mai dad'i da amo ya ce, "kin wuni lafiya ??.
Cikin jin kunya ta ce, "lfy law.
Ya ce, "ya gajiyar biki??.
"Nanma saida tayi k'asa da kai sannan ta amsa.
Ya ce, "my Sopy aii kuma kunya ta k'are yau, domin kin zama tawa nazama naki har abada.
Ita dai tayi masa shiru, idonta arufe saboda tsananin kunyarsa datake ji, gashi kuma yak'i sakar mata hannu, ya matso da fuskarsa kusada tata, harsuna jin fitar numfashin juna, batayi aune ba taji ya manna mata wata k'yak'yk'awar sumba😘a kumatu. (Kiss)
Tayi wata 'yar girgiza dan sumbar ta shigeta har cikin kwakwalwa......................✍🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.