Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 35 of 40

Turkashi musu karatu, komai zai faru a wannan gida yau, lallai kila yau sai an kwatanta yak'in duniya nafarko awannan gida. Nima kaina a tsorace nake bare fareeda da uncle G!!!!!!!!!.

Kuyi hak'uri darashin type na kwana biyu.

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 24~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸5⃣4⃣🔸🔶

...........Sopy tayi wani wawan tsale ta cakumi wuyan fareeda, wata muguwar shak'a tayi mata irinta mutuwa, idanun fareeda suka fiffito, tafara kakarin fitar rai, dan numfashinta sai safa da marwa yakeyi, uncle G! sai k'ok'arin b'an b'areta yakeyi amma yakasa, yarasa wane irin k'arfine da sopy.
Ganin idan yay sakaci zata iya halaka yarin yar mutane, saiya saka k'arfi ya finciketa daga kan fareeda.
Fareeda tafara murza wuya dan taji shak'a, sopy tak'ara kukan kura saman fareeda, kokawa ta kaure tsaka ninsu, dukda sopyce take jibgar fareeda wannan bai hana fareeda kare kantaba, uncle G! kuwa wajen k'ok'arin rabasu aka bashi naushi a baki, dole yay baya hannunsa rik'e da baki.
Su sopy kuwa tuni sunkai falo, duk abinda kowa yasamu makawa d'an uwansa yakeyi, dan danan suka hargitse falon, babu abinda kakeji sai ihu da ashariyar da fareeda take kutun tumawa.
Tabas fareeda tana shan duka, dan tun tana iya karewa harta fara gazawa, uncle G! ya d'auki waya yakira uncle kabeer, ya ce, "kabeer kataimakeni wlhy za'ayi kisa agidana, ka gaggauta zuwa, nakasa tab'uka komai saboda tashin hankali.
Cikin rud'u uncle kabeer ya ce, "lfy? ??, kai dai kazo uncle G! yafad'a tareda kashe wayar yanufo falo.
Fareeda ta rarumi wuk'a wai zata kashe sopy, uncle G! duk yarikice sai hak'uri yake bama fareeda.
Amma sopy ko'a jikinta dan fuskarta bata nuna alamar tsoroba, sopy tad'auki filawa ta jefama fareeda jikake dauuuuuu agoshi, dan danan goshin fareeda ya fashe jini yafara ambaliya a fuskarta, dama duk anjimata ciwo a hannuwa da jiki.
Fareeda tayi wata k'ara mai razanar wa, amma ko ajikin sopy, taje ta tad'e fareeda ta fad'i akan tayils takara fasa kai, da alama kafarta ta karye kokuma targad'e, hakan bai ishi sopy ba, ta hau kan ruwan cikin fareeda tacigaba da ribd'a, gaba d'aya hankalin uncle G! yatashi, gashi yakasa d'aga sopy daga saman fareeda, ga fareeda tanata kakarin mutuwa, da gudu uncle kabeer yak'aso, dak'yar suka iya d'aga sopy daga saman cikin fareeda.
Sopy saijan ajiyar zuciya take kamar zata mutu, uncle kabeer yasan sopy idan tayi zuciya zata iya aikata komai, kuma tana samun k'arfi na musamman awannan lokacin, dan haka bai zargi uncle G! da sakakin hana sopy dukan fareeda ba.
Ta kuma yun kurowa zata damki fareeda, unlce kabeer ya ce, "youseef kariketa, dan yanzu sopy bata cikin han kalinta.
Ruk'o sosai uncle G! yayma sopy, amma sai fige2 takeyi tana fad'in ya saketa ta kashe fareeda kowama yahuta.
Data kasa kufcewa saita fashe da kuka mai ban tasayi, acan kuma uncle kabeer yana k'ok'arin far fad'o da fareeda dan ta suma, tad'an dad'e kafin ta kawo numfashi, dak'ar uncle kabeer ya d'agata ya d'ora saman kujera.
Kamar daga sama sukaji ana buga k"ofa, uncle kabeer yaje ya bud'e dan yasan ko su waye.

Suduka suka shigo, uncle G! yana binsu da kallo, akwai baban farida da mamarta sai k'anin babanta sai yayyaenta maza biyu, sai zainab, sai baban sopy da inna saikuma aunty Nafisa da aunty hauwa'u da aunty asiya matar uncle kabeer, suduka kallon falon suke, dan kuwa ya hargitsu, lallai sun tabbata ansha gumurzu agidan.
Suka kai dubansu akan fareeda dake kwance jina jina, sai kuma sopy da uncle G! yasaketa ganin iyayenta, yazata tahak'ura tunda taga iyayensu, amma ina baisan zuciyar sopy idan tab'aci akwai matsalaba.
Yana sakinta kan fareeda tayi, tacigaba da jibga, baban tane ya wanka mata mari, wanda yasa tashiga hankalinta, ta zube a k'asa tana gunjin kuka, dan an hanata koyama fareeda darasi, mamar fareeda tazo ta rungume sopy tana lallashi, saida kowa ya natsa, aka zazzauna falon yayi ahiru, babu abinda kakeji sai shashshekar kukan sopy, wanan kuma sunsan bazata dainaba har sai ta huce, ko kuma an tofa addu'a acikin ruwa an bata tasha sannan.
Wani mai kyamis dake bayansu uncle kabeer yakira, yazo yay musu diresin d'in wajajen dasukaji ciwo, na sopy kad'an ne, amma fareeda abin sai wanda yagani, ma gunguna yabasu sannan ya gice.
Palon yay tsit kamar ruwa ya cinyesu, har tsawon minti goma babu wanda ya ce, "uffan.
Sai can k'anin baban fareeda yay gyaran murya, tareda sallama suka amsa, ya ce, "yusufa miya kawo wannan d'anyen aikin a gidanka, kuma a ina kuka samo fareedatu???.
Uncle G! ya sassauta murya cikin ladabi, yashiga basu labari tundaga zuwan fareeda gidan har zuwa abinda ya faru yau, baba yadawo kan fareeda ya ce, "fareeda haka akayi, ta ce, "tunda taji uncle G! bai fad'i tsiyatakun datayiba, yadawo kan sopy wadda har yanzu tana ajiyar zuciya ya ce, "ke kuma mikika sani gameda hakan safiyya??.
Sopy saitayi shiru, kowa yasan idan tayi zuciya batason magana, dan haka uncle G! yay saurin ce wa, "a k'yaleta kawai wanda suka fad'a shida fareeda ya isa, Dan baya so sopy tab'aro komai.
Baban fareeda ya ce, "dolene itama tayi magana dan kar a tauyeta, uncle kabeer ya mika mata kofin ruwan addu'a takarb'a tasha, bayan "yan muntuna tadawo hayyacinta.
Ta zauna ta zayyano duk abinda ya ke fatuwa tsaka ninta da fareeda, har abinda yasa Abdul ya koma kan fareeda, dan fareedar tafad'ama sopy komai da bakinta, tafad'i zuba mata gishiri da yaji da suga cikin abinci da fareeda tayi, har saka kayan barci tazo falo ta zauna saida sopy tafad'i, tafad'i gargadin data yima fareedar dan takiyayeta, dakuma abinda yafaru a yau.
Sopy bata rage komaiba.
Maman fareeda ta dakawa fareeda tsawa ta ce, "koki warware tuggun dakika kulla yau kokuma na tsine miki, nakuma kasheki da hannuna, yayanta ya zazzare mata idanu ya ce, "bazaki fad'aba muna fuka annamimiya.
Fareeda dataga babu sarki sai ALLAH saita fad'i gskyr abinda yafaru yau, takuma wanke uncle G! daga zargi, danshi yak'i fad'ar komai.
Uncle G! yaja ajiyar zuciya danjin ALLAH mai komai mai kowa ya kub'utsr dashi.
Maman fareeda ta fashe da kuka danjin abinda d'iyar tata ta aikata, abin kunya da kazanta.
Dak'ar aka lallasheta, ta ce, "kuma bazasu sake zama da fareedaba, saidai tanemi wasu iyayen badai suba.
Nakula yau fareeda tayi nadama ta gsky, dan kallo d'aya zakai mata ka sheda hakan, kuka tashiga rerawa tana basu hakuri, da fadin tayi nadama walhy tayi nadamar aikata duk abinda yafaru abaya da yanzu, takumayi alkawarin canja halayenta.
Baban ya daka mata tsawa ya ce, "makaryaciyar banza da wofi, ba haka kika cema su yufan ba yayinda ya tsuntoki, kekam inaga wutar ALLAH ce kawai zata sakaki nadama.
Da sauri baban sopy ya karb'e da fad'in A'a bama fata, kuma ni na yarda da tubanta, dan haka zata koma gidana da zama, kafin ALLAH yabata miji tayi aure, sai dai ina nemar mata gafara daga gareku,, kuyi hakuri ku yafe mata, bakinku kawai zai iya hana dawwamar tubanta, zai kara jefata wajen aikata wani kuskuren, ku yafe mata dan ALLAH.
da k'yar uncle G! da uncle kabeer da inna suka saka baki, iyayen fareeda suka yafe mata, aka dawo kan 'yan uwa suma ansha fama kafin su yafe, sopy kuwa duk'ar dakai tayi dan baxata iya yafe waba, sunsan halinta sarai yanzu tana kan dokin zuciya, dan haka uncle kabeer ya ce, "su barta sai nan gaba, idan ta huce, dan ba'a tursasa mutum ya yafe zalincin da'akai masa.
Haka aka hak'ura aka bar sopy, suka tusa k'eyar fareeda suka tafi, akabarsu aunty zainab suna gyara gidan sopy, dan yayi kaca2 kamar filin sukuwa.
Gyara sosai sukai mata aka maida komai mazauninsa, wadanda suka fashe aka zubar, sai bayan isha'i suka tafi, bayan sun yimusu girki sunsaka sopy ta gasa jikinta da ruwa mai zafi, saboda tsamin jiki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.