Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 19 of 40
Itamadai sopy tunda suka tafi taiyi shiru dan tana k'aunar Aysha, yarinyar tanada shiga rai ga wayo da son aiki, zuwan su aunty NAFISA ne yasaka tad'an ware, suka shiga aikin gyaran gida, da kaiwa mak'ota kwanikansu da sauran abinda aka aro domin yin amfani, dayake duk danginsu anan cikin kano suke, sai yazama babu kowa a gidan sai isu isu, inna dakanta ta shirya karin kumallo sopy taje takaiwa su uncle kabeer.....................âœðŸ»
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 29~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸2⃣9⃣🔸🔶
........Gwaggo ta tari autarta da murna, dan kwana biyunnan tayi kewarta, Aysha ta ce,"gwaggo wlhy nayi kewarki kwana biyu, sai dai naji dad'in zuwa kano.
Gwaggo ta ce, "kai auta fad'i gaskiya dai, kinga yanda kikai haske da k'iba a kwana biyunnan kuwa, mikike cine haka? .
Aysha tayi dariya, aii wlhy gwaggo bazasu lissafuba, kai matar da yaya zai aura tanada kirki gwaggo gata mai k'yau.......tayi shiru domin shigowar uncle G!.
Ya ce, "to uwar surutu ince har kin fara zubama gwaggo shi.
Gwaggo ta ce, "to badoleba tayi kewanane aii.
Uncle G! Yazauna a kan tabarmar dake shimfid'e ad'akin yashiga mik'a gaisuwa ga gwaggo.
Gwaggo ta amsa cikin fara'a, ta ce, "ya aikin? Da abokan zama?.
Wlhy lfy law gwaggo sunata gaisheku, da kuma godiya.
Kai haba saikace wani abu, mu abinda kabiru yay mana aii bazamu iya biyansaba.
Uncle G! Yay murmushi, ya ce, "gwaggo ina baba yake?.
Baban ku yana wajen zana idar malam haruna mai gari.
ALLAH sarki, gwaggo malam haruna yarasu?.
Wlhy kuwa d'annan yanzu badad'ewa aka fad'i mutuwarsa, inagama ba'a binnesaba.
To ALLAH yagafarta masa da dukkan musulmai baki d'aya, amma mutuminnan yasha wahalar jinya, ALLAH dai yasa kaffarane.
To amin gwaggo tafad'a tana mik'ewa, bari nakawo muku ruwa, munata surutu ko ruwa ba'a bakuba.
Uncle G! Ya ce, "bakomai gwaggo da kin barima Aysha saita d'ebo aii, gwaggo ta ce, bari nad'ebo tunda natashi, saima ahad'o da abinci, saidai kuma ban bayar ansiyo maka awarar taka ta famaba, wannan tararrabin rasuwar ya mantar dani,, Aysha taso ki siyo masa, ALLAH yasama bata k'areba kinsan Awarar uwaliya kamar nama take agarinnan.
Aysha ta ce, "to gwaggo kawo kud'in??, ki d'akko a k'ark'ashin filo, akwai d'ari biyu.
Uncle G! Ya ce, "karb'i barmata kud'inta, ya mik'a mata dubu d'aya, ta ce, "yaya daka bari na d'auki d'ari biyun dan wlhy sai kaga anata neman canji ak'isamu.
Ya ce, "to, kuma kiyi sauri, dan karki zauna neman zance.
Aysha tafita tana turo baki.
Gwaggo tashigo da ruwa a kofin silba, ta koma ta d'akko samira ta ajiye gaban uncle G!, ya ce, "yawwa gwggonmu sannunki da aiki.
Ta zauna tana fad'in aii kune da sannu, kuda kuka sha hanya, ya d'auki ruwan yasha, yana murmushi, suka cigaba da hira kafin Aysha tadawo.
Badad'ewa Aysha tadawo, sukaci suka k'oshi yafita danyin sallah da ta'aziyyar rasuwar da'akayi.
Baba yashigo, Aysha taje ta taroshi cikin farin ciki, A'a Ayshatu! saukar yaushe??, aysha tayi dariya baba tun d'azu mukazo harda yayama.
Ya ce, "madallah ina yusufan yake?, baba yanzu yafita sallah baku had'uba?, A'a bamu had'uba, k'ila masallaci juma'a yaje sallar dan sune naji sun tada sallah yanzu.
Saida yay gasuwar yadawo, ya tsugunna ya gaida baba, baba ya amsa cikin fara'a, yusufa! ya jama'ar birni?, dasu kabiru ango??.
Wlhy lfy law baba, yanata godiyar d'awainiya.
Kai haba in banda abin kabiru miye na godiya, abun nawa yake, tunda ALLAH bai nufa zamu d'aurin aurenba.
Aii bakomai baba hakanma angode ALLAH yasaka da alkairi, Aysha aii ta wakilceku.
Sun dad'e suna hira, anan nema uncle G! Yasanar da baba maganar tura manya gidansu safiyya, ckin jin kunya yake maganar.
Baba yayi dariya aii ko yusufa nayi farinciki da wannan magana, wlhy dama zamannan naka ya isheni haka, mutane sai surutu sukeyi wai dan kayi boko kak'i yin aure, sun manta aure lokacine.
Uncle G! Yay k'asa da kai yana fad'in gsky ne baba, amma kuyi hak'uri.
A'a aii bakomai yusufa tunda gashi lokaci yazo, aii mu sadai muce ALLAH ya kaimu lokaci, yasa kuma ayi da ranmu.
Akan leb'ensa ya ce, "amin.
Bayan sun gama tattaunawa yafita domin ganawa da matasan k'ungiyarsa kamar yanda yasaba, domin suma tuni sun hallara gurin dasuke had'uwa tunda sunsan da zuwansa.
Da dadadare aunty hafsat suka zo itada libabatu dan tuni Aysha taje gidajensu takai musu labarin matar da yaya zai aura, harda tsarabarsu, sannan ma shi bai dawoba yana waje.
Basu dad'e da zuwaba ya shigo shima, ya ce, "A'a 'yan uwa kune da daddarennan??
"Sukace mune!!.
Yaja kujera 'yar tsugunno yazauna, suka gaisa, sukai masa godiyar tsaraba, ya ce, "wace tsaraba kuma aii ni! banyima kowa tsaraba ba.
Aunty hafsat ta ce, "e, auta tace k'anwar muce tabamu ALLAH dai yasaka da alkairi yakuma kawo mana ita lfy.
Uncke G! Ya ce, "to amin, yakuke da yaranku da mazajen!! ku?
Suka ce, "duk muna nan lfy.
Ya ce, "aii haka akeso.
Baba yashigo yana fad'in tofa yau gidan biki akene?
Sukayi dariya, kowa ta gaidashi, sannan sukace munzo sannu da zuwane.
Baba yazauna yana fad'in ince ko har Aysha taje muku?.
Sukace aii baba tun d'azu ma kuwa.
Ya ce, "auta kenan sarkin hidima, nan dai sukayita hira, harma baba yay musu bayanin maganar auren yayansu.
Sunyi murna kwarai da gsk.
Washe gari uncle G! Yataho damasu kawo kud'in aure, anyi musu tarba ta mutunci, daganan komai ya gudana, atake kuma baba ya saka ranar aure nanda wata hud'u, iyayen uncle G! Sunji dad'i domin kuwa babu wani jan rai, bayan sun kammala uncle G! Yakaisu tasha suka hau mota domin komawa gida.
Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, sopy tana karatu, kuma sukan yi hira jefi jefi da uncle G!, Dan bai cika takurata ba, saboda Baya son tasamu matsla a karatunta, yakan taimaka mata akan abinda yashige mata duhu, dukda har yanzu tananan cikin jin kunyarsa bata cika sakin jikintaba idan yana guru, zuwa wannan lokacin kuma labari yabaza makaranta cewa uncle G! Zai auri safiyya.
Wasu har zuwa suke takanas domin ganin mai sa'ar data samu zuciyar tsadajjen namiji mai aji da ilimi irin uncle G!, dayawa sukanyi mamakin ganinta, dan azatonsu farace k'al kuma mai shegen k'yau👩ðŸ», wasu sukance dama masu k'yau basu cika zab'ar mace mai k'yauba, wasukuma sukanga safiyyan tadace da uncle G! D'in, domin itama tanada k'yau, sai dai k'yawunta mai b'oyuwane, irin wanda saika cika kallonta ko kana tareda ita kullum kake gani, to koma dai miye 'yammata saiku saurara domin kuwa safiyya itace tauraruwar uncle G!, dan shiyyasan sirrikan daya gano agareta.
Magulmata dai anata aikin gulma, yayinda wasu 'yammatan suke jin haushinta dan sunnunama uncle G! D'in so amma yay burus dasu, itakam ko kallo basu ishetaba dan bata shiga sabgar kowa, garama Nadiya sukan d'anyi hira amma itama bakomai tasani dangane da sopy ba.
Dan sopy ta daina k'awa bare AMINIYA, anriga anmata tabo azuciya akan AMINTAKA............âœðŸ»
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YO[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 29~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣0⃣🔸🔶
........Akwana atashi babu wuya gurun "UBANGIJI", biki dai ya kankama, dukkan gidajen biyu sunata shiri, hakama uncle G! Yayi wuyar gani, ita kanta sopy baganinsa takeyiba, sai idan yaje musu lecture, ko kuma idan ya kirata a waya su gaisa.
Yau da yamma Sopy tashigo anguwarsu, tana shigowa layinsu tayi kicib'is da Abdul, suduka gabansu ya fad'i, yabita da kallon k'urullah, itako ta tamke fuska kamar bata tab'a dariyaba, ta ratseshi zata wuce, da sauri yasha gabanta, takauce zuwa gefensa nanma ya tareta.
Ta ce, "malam bani hanya nawuce.
Ya ce, "haba gimbiyata ninefa Abdul d'inki mai sonki da k'aunarki, wlhy ina kewar rashin ganinki, dan ALLAH ki tsaya muyi magana.
Ta balla masa harara tareda jan wani mugun tsaki ta ce, "kaga malam tunkafin na shuka maka rashin mutunci kabani hanya na wuce, wlhy Abdul natsaneka.
Ya rinyse ido ya bud'e dan tabbas kalmar tata ta daki zuciyarsa, ya marairaice murya yana fad'in, Sopy nasan baki tsaneniba haryanzu kina sona, kina cikin b'acin ran abinda yafaru abayane, dan ALLAH kibani dama namiki bayani yanda zaki fahimceni, kece kad'ai nakeso kuma ashirye nake dana aureki ahalin yanzu.
Sopy ta tuntsure da dariya, sannan ta tamke fuska tamkar ba ita tayi dariyarba, ta nunashi da d'anyatsa 👉ðŸ»â˜¹Abdul wai kaine! kake tunanin zama mijina!, tad'an murmusa, Abdul har abada bazan zama shashashar macen dazanyi miji irinkaba, ka d'auka SAFIYYA IBRAHIM KABEER ta sub'uce maka har gaba da abada, ta ciro kati daga jakarta ka karanta wannan shi kad'aima ya isa yabaka amsa, inama gayyatarka, dan nasamu miji mai tarin ilimi k'yau, aji mutunci, kai idan ina lissafa maka abinda ya dangan ceshi tofa sai mu kwana anan,kuma katashimin ahanya kafin natara maka mutane wlhy.
Jiki asanyaye yamatsa mata ta wuce, tunda yafara karanta katin yake fitar da numfashi mai kama da nishi, yajingina da bango gudun karya fad'i, cikin murya kamar mai kuka ya ce, "fareeda kin cuceni ALLAH ya isa tsakanina dake, kuma wlhy yau saikin gayawa aya zak'inta, yanufi gida kamar mayun wacin zaki.
Da sauri muka bishi dan muganewa idanmu abinda zai faru.
To bari mugani fareeda kota zubur da cikin??.
Tunda nagabato b'angarenta nakejin ihun kukanta, wanda inada tabbacin suma mutanen dake gidan sunajinta, amma babu wanda yay yink'urin zuwa yaga abinda yafaru.
Nak'arasa d'akin da sauri nida madina, Abdul ne ke lakad'awa fareeda dukan 'yan danbe, duk yaji mata ciwo, amma wannan baisa ya daina d'irkartaba, dak'yar muka iya kwatarta, ya bimu da kallo yana huci kukuma daga ina??.
Madina ta ce, "tofa, Abdul maida wuk'ar mu bak'in fareeda ne, yaja tsaki tozaku iya tafiya aii ko.
Na ce, "kayi hak'uri Abdul kabari mu taimakawa fareeda kaga duk ciwone a jikinta, wata uwar harara yasakarmin, to aii ko uwar tace tazo gidannan saita fita, tunda sunce sun sallama mini ita, bareku gayyar sod'i, wlhy tun kafin nabud'e idanuna kubar gidannan idan kuwa bahakaba tokuwa jikinku zai fad'a muku.
Aii kafin yagama rufe baki madina uwar 'yan tsoro taja hannuna munyi waje, ta ce, "humm aunty bily naga mutuminnan yafara haukacewa wlhy zai iya dukanmu, kekam gaki lutiya idan yasamu wannan tsokar aii kinga takanki.
Na balla mata harara ina fad'in ALLAH madi kin rainani, ni son k'ibar nan tawa nakeyi idan baki saniba.
Amma gsky Abdul bashida mutunci irin wannan duka dayake mata kamar wata karuwarsa, kuma muta nen gidan sunaji amma sunk'i cetonta.
Madina tayi dariya aii ni dad'i nakeji wlhy ALLAH yasa yay mata abinda yafi hakama, aii maganin maci amana kenan, kad'amma tagani.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.