Complete Hausa Novels

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 38 of 40

🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹
Yau dawuri uncle G! yafita dan zaiyi lectures d'in safe.
Sopy ta tashi tad'an gyara gidan iya inda zata iya, dan yau bata jin dad'in jikinta kwata2, tana dai daurewane dan bataso tahana uncle G! fita aiki, tad'an cije leb'e ta rik'e bayanta da hannu d'aya, tadafe kujera da d'ayan.
Tad'an dad'e tsaye tana shan azabar ciyo, daga bisani yalafa, ta rarrafa dak'yar takoma bedroom.
Tana zuwa tazube agado, tanata murkususu, saidaga baya wani bacci mai dad'i ya saceta.
Agigice ta farka domin jin wani azababben ciyo, mai kamada na fitar rai, ai bata san sanda ta silmiyo daga gadoba, babu abinda takeyi sai salati da kiran sunan ALLAH, dak'yar ta iya d'aukar wayarta, batare da tasan nomber ko wayeba takira kawai, ALLAH yasota aunty Asiya takira, dak'yar ta ce, "plz kowaye yazo ya taimakeni zan mutu.
Aunty asiya bata jira ta karasa ba, ta fito da sauri daga gida, gidansu ummy ta mik'a khalil, agurguje tazo gidan, sanda ta iso sopy harta fita hayyacinta, dan kuwa haihuwa ce gadan2.
Aunty asiya ta rik'eta tana mata sannu.
Ita dai sopy babu abinda takeyi sai ambatar sunan ALLAH, da duk addu'ar datazo bakinta, zuwa can tasaki wani uban nishi, jikake wani kacam, d'a yafad'o, yana tsanyara ihu.
Aunty Asiya ta ce, "masha ALLAH, sopy sannu da aiki.
Aunty asiya takira ummy ta ce, "ta turo mata mamarsu.
Babu dad'ewa mamarsu ummy tazo, aka yanke cibiya, tareda d'auke sargad'ed'iyar yarinya maikama da babanta, maman ummy ta ce, "masha ALLAHU, da zuwan wannan k'yak'yk'awar yarinya duniya gidan gwa gwarmaya.................✍🏻

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞

27~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸5⃣8⃣🔸🔶

...........tsaf suka gyara jaririya da sopy, Aunty Asiya takira uncle kabeer ta sanar masa, shikuma yasanar da uncle G!, dan danan labari ya karad'e dangi, har muta nen Gurum labari yakai musu, acanma murna ce ta kaure, da addu'oin fatan alkairi ga jaririya, bak'uwar duniya.
Uncle G! ya iso cikin murnarsa, bai damu da makwaftan dasuke zaune afaloba, suka gaidashi tareda yimasa barka.
D'akin sopy ya isa cikin matuk'ar zumud'in son ganin jaririyarsa, yana shiga ya rungume sopy dake bakin gado tana shafa mai, dan batajin ciwon komai, saidai aunty asiya ta ce, "ta shirya suje asibiti aduba lafiyarta itada baby.
Sopy tad'ago tana kallonsa, suka sakarwa juna murmushi, ya ce, "sannu sopyna, ya jikinki??, sopy ta ce, "komai nomal hubbina.
Ya ce, "masha ALLAH, aunty asiya tashigo da sallama, suka amsa, ta mik'a masa jaririyar da'aka shirya cikin fararen kayan sanyi masu laushi.
Yasa hannu biyu yakarb'a, ya tsura ma jaririyar ido kamar zai cinyeta, yad'an mannata da jikinsa tareda lumshe idanu yana zubar da hawayen farinciki.
Sopy tasaka hannu tana share masa, yad'an dad'e ahaka sannan ya bud'e idanu, ya sauke akan jaririyarsa, mai tsananin kama dashi, tanata barcin ta.
Tad'an motsa kad'an, yay saurin fad'in sorry my dear, yad'an jijjigata kad'an, takoma barcinta.
Sopy ta ce, "hubbina santin baby ya hanaka magana ko??, yad'ago yana murmushi, ya ce, "sopyna k'yautar d'a!! dabance, bazan iya misalta miki irin farincikin danake cikiba yau wlhy.
Sopy ta ce, "aii naga alama, dadyn baby!!.
Uncle G! ya ce, "haka zancen yake, amma zonabaki sunan babyna, sopy ta mik'ama uncle G! kunnenta, ya gwargwad'a mata, tayi wani murmushi tana fad'in inko haka ta kasance to kayi halacci hubbina!.
Ya ce, "ko? Sopyna!.
Ta ce, "ALLAH kuwa.
Ya ce, "anyi an gama, barima kiga nayi maya hud'uba.
Uncle G! yay mata hud'uba sannan suka tafi asibiti dan aduba lafiyarsu.
Haka akayita hidima, koda yaushe gida cike da 'yan barka, su aunty Nafisa kuwa kullum sai sunzo, fareedama tazo saidai sopy bata sakar mata fuskaba sosai, itako fareeda bata damuba tanata rungume jaririya danji take wata irin k'aunar yarinyar tana shigarta.

Yau muta nen gurum sukazo mota guda, aka had'a musu cima masu dad'i, sukaci sunata santi, sai yamma suka tafi akabar su aunty hafsat da libabatu da aysha anan, komai yana tafiya yanda akeson gwaggo ta had'o ma sopy kayan barka sosai, mutane sunata santi kayan, dan gwaggo ta taka rawar gani.
Yau kuma aka kawo naman k'auri daga gidansu sopy, suma sunyi k'ok'ari, dan d'an akuya guda uncle kabeer ya siyo aka gyara, suma sunyi rawar gani wajen had'o kayan barka, ayau kuma shima uncle G! ya kawo nasa kayan barkar, abindai sai wanda yagani, komai dai2 saidai mak'yi zai kushe.

RANAR SUNA.
yaune akasha sunan baby wadda taci sunan BILKISU MAI GADON ZINARI", lallai uncle G! yay mini halacci kuma nagode.
Bayyana muku yanda taron suna yakasance b'ata lokacine saidai fa, ansha shagali na ban mamaki, groups dayawa sun halacci taron sunan baby Bilkisu!, irinsu.👇🏻
💞PROFESSIONAL WRITER
💞ZUMUNTA GROUP
💞HAUSA NOVELS
💞 MANSHAT NOVELS
💞PRECIOUS WRITER' FORUM
💞IKKIAM'S NOVELS
💞HAUSE OF NOVELS
💞SO DA K'AUNA GROUP
💞FASHION & NOVELS
💞BEST FRIEND'S
💞LABARUN LITTATAFAI
💞HAUSA NOVEL BOOKS
💞 MACE MUTUM GROUP, ma sun halacci wannan taron suna, harma da groups d'in daban fad'aba, suyi hak'uri amma suma duk mun gansu.
Dahaka taron suna yatashi lafiya, akabar mai jego da jaririya Bilkisa, tareda dadynta uncle G!!!.
An kawo musu tsohuwar dazata kula dasu, har suyi arba'in, AYSHA ma ta nan anbarta, saboda wasu ayyukan.

Bayan arba'in, baby Bilkisu tayi b'ul2 da'ita gwanin sha'awa, tana shan tarairayar iyayenta, dan uncle G! yana dawowa aiki zai d"auketa sallah ce kawai takesawa ya ajiyeta, ranar weekend kuwa ai ahannunsa take wuni, yayta mata wasa tana b'angale baki, sunje Gurum yawon arba'in, an kaiwa gwaggo da baba sunga jikarsu, takosha addu'oi, awajen kakanninta.
Ananma kano sun zagaya gidajen 'yan uwa da abokan arzik'i, daga baya sopy ta tattara takoma makaranta itama..................✍🏻

WASA KWAKWALWA.
wannan sak'one daga gareni, inaso ku fad'i abinda yake ranku game da wannan littafi mai suna NI DA AMINIYATA!!!.
SHIN WA👇🏻
☆WAKUKAFI TAUSAYI??.
☆WAKUKAFI JIN HAUSHI??.
☆WAKUKAFI SO???.
☆ WAYAFI BIRGEKU??.
Karki bari ayi babu ke, fad'i ra'ayinki, ko gyara gareni agun danayi kuskure.
Idan kuntashi, kusaka sunanku, da gruop d'in dakuke, dakuma ra'ayinku.
Inanan ina jiran sak'wanninku, ta hanyar gruop gruop d'inku, dan saikun rubuta ra'ayoyinku kafin mu kalmashe bakin wannan labari, daga nan zuwa ranar litinin.
Plz karkuyi sanya, nagode sosai da k'yaunarku gareni.
SAINA JIKU📢📢📢📢!!!!!!!!!!!!!.

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞

[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 28~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸5⃣9⃣&6⃣0⃣🔸🔶

.............haka rayuwa tacigaba da tafiya, su sopy suna rainon baby bilkisu, yanzu haka tafara zama, uncle yadawo da Aysha wajensa, an nema mata makaranta tana yi anan, haka sopy tana zuwa makaranta kuma tana fahimta, abunda bata ganeba uncle G! yana nuna mata.
Adai2 wannan lokacinne kuma aka sha bikin fareeda da wani d'an anguwarsu salmanu, yanada mata d'aya da yara uku, fareeda ta aureshine kawai amma badan yayi mataba, dole ta aureshi dan zaman gidan ya isheta, gasu baba sun dameta akan tafito da miji, to hakadai aka rurrumata aka kaita, indama ALLAH yasota ba gidansu d'aya da kishiyarta ba, gidan hayane d'aki d'aya ya kama mata, suna had'akar bayi da kichin da sauran 'yan hayar gidan, bawata cimar arzik'i, shinkaface fara da mai da rana da safe kuwa koko da k'osai shima idan kin samu, da daddare tuwo, dan haka fareeda duk tafita hayya cinta ga wani uban bak'i datayi kamar ba itaba, shiyyasa kullum cikin kuka take da nadamar abinda ta aikata abaya, ALLAH yasotama sopy tayafe mata harda uncle G!.
Agidan sopy kuwa abun su d'anas komai yana tafiya yanda suke so, ga mijinta yana nuna mata soyayya mai tsafta, koda yaushe k'ara tattalinta yake, itama k'ara sonshi take kullum, ga 'yar d'iyarsu abin sha'awa da burgewa.
Aunty asiyama ta sake haihuwar mace, itama suna cin soyayyarsu da uncle kabeer, komai yana tafiya musu dai2.
Haka yayun sopy sumadai Alhmdllh, komai dai2.
Mutan gurum ma a b'angarensu komai nomal masha ALLAH.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.