Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 33 of 40
Zan iya cemuku dai ayanzu fareeda tad'an fara shiga hankalinta, dan tad'an rage aikata wasu abubuwan saidaifa har yanzu tanan akan bakanta nason mallakar uncle G! amatsayin miji, to itamadai safiyya tanan tana tanadar manya2 makaman yak'ar fareeda, dankuwa kulum tana tashi da shirin kota kwana.
Yaukam sai k'arfe biyu sopy tashiga makaranta, dan batada lecture d'in safe, sai sauri take dan tasan uncle G! yau zaimusu lecture karfe biyu da kwata, cikin sassarfa ta isa class, amma saidai ta makaro, domin kuwa har uncle G! ya shiga.
Taja birki ak'ofar class d'in kamar yanda makararu suke tsaye, tofa saimuce kallon ya koma sama, sai hankalin 'yan class d'in da makararru suka dawo kanta, kowa yana so yaga ikon ALLAH, jiyayi k'amshin turarenta ya yawauta agurin dan haka yad'an juyo ya kalli inda yake zaton take, sukaima juna kallon ido cikin ido, amma sai uncle G! ya basar yacigaba da lecture d'insa.
Wani k'ududun bak'in cikin ya tokare mak'ogwaron sopy, gashi gabad'aya hankalin d'aliban yana kanta.
Uncle G! ya juyo ya kalleta yana wani d'an murmushin mugunta, dukada fuskarta tana yane da nikaf wannan bai hanata murgud'a masa bakiba, ya maida kallonsa ga d'alibai fuskarsa d'auke da murmushi.
Bayan ya kammala lecture d'in ya fito, hannun sopy yakama batareda yayi mata maganaba, sopy tayi k'ok'arin kwace hannunta, amma saita kasa, dan ba rik'on wasa yay mataba.
Har cikin office d'insa ya kaita, sannan yasaki hannunta yajiginna da k'ofar ya hard'e hannayensa a k'irji.
Sopy ta kauda kai gefe dan haushi, hannu yasa ya yaye mata nik'af d'in fuskarta, ta galla masa harar tana murugud'a bakiπ, yasa yatsu biyu ya kamo lab'b'anta, yad'an matsesu waje d'aya, ta rik'e hannunsa tana k'ara, dan taji zafi.
Uncle G! ya ce, "o, autar inna da zafine??, ta harareshi da idanuwanta dasukayi jaa, yasaki bakinta yana murmushi, hannu yasa ya d'ago fuskarta suna kallon juna, ya ce, "wannan shine gargad'inki, daga yau idan kika sake makara tofa hukuncin yafi haka yawa.
Ta lumshe idanunta, wasu hawaye suka zubo bisa kuma tunta, wani tsadadden murmushi yasaki tareda sumbatar bakinta, ta bud'e idanu da sauri, suka zubama juna ido, daka gansu kasan kallon k'auna sukema juna, suka lumshe idanu alokaci d'aya kum suka bud'e, uncle G! ya rungumeta tsam zuwa jikinsa.
Sopy ta ce, "a zuciyarta, uncle G! Kenan, zuma ga zak'i ga harbiππ».
Yau takasance juma'a, yaune kuma su aunty Hafsat zasuzo, gaba d'aya sopy ta rikita kanta sai aiki takeyi, domin tarbar bak'inta, ita dai fareeda sai kallon ikon ALLAH takeyi, hakama uncle G! binta kawai yake da kallon mamaki, dan ganin yanda taketa hidima kamar wasu bak'ine daban zasuzo basu libabatu ba.
Wajen k'arfe d'aya da rabi uncle G! yatafi tarosu a tasha..............βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 21~November~2016
π·πΉNI DA AMINIYATA!!!πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIMπ
πΆπΈ5β£2β£πΈπΆ
............Babu dad'ewa uncle G! yadawo d'aukeda su aunty hafsat, cikin matuk'ar fainciki sopy ta taresu, suma dai sunyi farin cikin ganinta, musamman ma Aysha.
Sopy tacika musu gaba da kayan abinci, aunty hafsat ta ce, "o ni, k'anwata yaya zamuyi da wannan abinci haka, saikace masu cikin zani.
Sopy tayi dariya tana fad'in duk nakune aunty, aii d'anyar fata bata fashewa.
Sukayi dariya suna fad'in lallaikam, yau zamuci har mu kasa tashi, fareeda ta fito tana musu sannu da zuwa, suka amsa suna binta da kallo, dan basu santaba, ta zauna tana wasada Sayeed d'an gidan Libabatu.
Uncle G! yafito, jikinsa sanye da farar shadda tas d'inkin nasa dai bodane kamar kullum, tayi masa matuk'ar k'yau,sai tashin k'amshi yakeyi, ya d'ora hula da farin gilas siriri.
Aysha ta ce, "yaya ina zakaje, yad'an kalli bak'in agogon dake d'aure a tsin tsiyar hannunsa, ya ce, "Aysha xanje masallacine ko.
Ta ce, "dan ALLAH zanje.
Ya girgiza kai yana fad'in A'a bazanje dakeba, masallacin nan bakamar na gida bane.
Sopy tafito daga kichin hannunta d'auke da tire, ganin uncle G! ya d'au kwalliya saita tsaya tana kallonsa.
Ya kanne mata ido d'aya, tad'anyi murmushi tana nuna masa su aunty hafsat da idanu.
Shima murmushi yayi tareda d'aga kafad'a alamu, so what, sopy ta ce, "uncle sai ina?, ya ce, "lallai kin manta yau juma'a?, ta ce, "o, masallaci fa ko??, ya jin jina mata kai yana lumshe idanu, ta ce, "to ALLAH ya tsare.
Yad'an yima sayeed wasa yana fad'in amin sopyna, sayeed yashiga wangale baki yana mik'a masa hannu.
Uncle G! ya d'aukeshi yana fad'in yaro masallaci zanje, yad'an yimasa wasa sannan yamaidashi wajen fareeda ya fice yana fad'in saina dawo.
Sukace to adawo lafiya.
Yau kam sunasha hira abinsu, sopy tasha firar gurum, sun kawo masu tsaraba irinta k'yauye, tasu data gwaggo, babama ba'a barsa abayaba.
Sai k'arfe hud'u uncle G! yadawo, sopy ta taroshi amma bakamar yanda ta sababa, saboda yau tana jin kunyar bak'i, ya zauna yana fad'in wash ALLAH!!; na.
Su duka suka dawo da kallonsu gareshi, Libabatu ta ce, "yaya ka gajine.
Ya kwantar da kansa jikin kujera yana fad'in wlhy kuwa sosaima kuwa, sopy ta kawo masa ruwa, ya tashi yakarb'a yasha yana mata murmushi.
Yagama sha ya mik'o mata kofin, ta karb'a tana fad'in abincifa uncle?, ya ce, "zanci dan wlhy ina jin yunwa.
Sopy ta nufi kichin tana masa dariya, ta ce, "a ajiye a dinining ko akawo nan, ya mik'e yana fad'in kawo nan, sai naci muna hira, amma bari nafara watsa ruwa tukuna.
Ta ce, to.
Sunan zaune suna hira yafito sanye cikin k'ananun kaya, sopy takawo masa abinci, yanaci suna hira.
Da magriba yatafi sallah, sukuma sukayi a gida.
Saida akayi isha'i yadawo, yadawo musu da gasashshen tsire mai dad'i, sukaci suna farin ciki.
Uncle G! ya ce, "oh, Safiyya namanta, albishirinki?, da sauri ta ce, "goro fari tas uncle.
Ya ce, "to saiki kawomin goron sannan, sopy ta ce, "to mikake so?, yay shiru alamar tunani, can yad'ago yana mata wani irin kallo, wanda har yabata kunya, ta duk"ar da kai k'asa.
Uncle G! ya ce, "alawar madara nakeso, ta yi d'an murmushi, dan ta fahimci inda yadosa, ta ce, "to kad'auka ka samu.
Babu wanda ya fahimci inda zancensu yadosa, sai fareeda Dan haka ta had'e rai, tana jin haushi, azuciyarta ta ce, "jara babbu kawai,π
Ya murmusa, ya ce, "to, Asiya ta haihu d'azu, tasamu d'a namiji.
Sopy ta k'an k'ame Aysha tana murna, ta ce, "uncle yaushe zamu?, ya ce, "to sarkin zumud'i aii k'ya bari sai gobe ko.
Ta ce, "ALLAH yakaimu.
Su aunty hafsat sukace amin.
Saida sukaga kowa ya kwanta sannan suka tafi d'akinsu suma, a d'aki uncle G! ya rungume sopy yana fad'in, yaufa ranar tadaban ce, ta d'ago tana kallonsa, ta ce, "miyasa yau tazama tadaban?.
Ya murmusa, ya ce, "kedai zoki bani alawar madara, sopy ta rufe fuska tana fad'in kai uncle ALLAH karage abinda kakeyi, agaban su aunty kake fad'ar wata alawar madara.
Ya ce, to aii basu ganeba ko?, ta ce, "aiiko sun gane, sundai yi shirune kawai.
Ya jawota saman k'irjinsa yana fad'in, bawani ganewa dasukayi, saidai idan fareeda dan naga tanata b'ata rai.
Sopy ta sumbaci k'irjinsa ta ce, "banida matsala da wannan.
Uncle G! yayi dariya, ALLAH sopy ke muguwace, nakula kwanannan kin sako fareeda a gaba fa.
Sopy ta ce, "niban sakata gababa, nagadai kawai rainin hankalinta yafara yawane.
Nafito ina fad'in bari nad'an lek'o su fareeda suma, d'akin na tura ahankali nashiga, suduka sunyi barci, babu wani mai kwakwkwaran motsi, da sauri nafito, nadawo d'akinsu uncle G!, amma saidai kash harsun rufe d'aki, nadawo baya da haushi, dan naso naga miye alwar madarar da sopy zata bawa uncle G!, dan nima naje nabawa nawa mijinππ................βπ»
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.