Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 26 of 40
♡~♡~♡~♡~♡~♡~♡~♡
Saida suka kwanta ta ce, "uncle!!.
Ya ce, "Na'am,
Wai dan ALLAH a ina ka ga fareeda ne?.
Saida ya rungumeta ajikinsa sannan ya ce, "kin daina fushin da nine?, ta ce, "nidama ba fushi nakeyi da kaiba aii, kawai dai rainane ya b'aci, amma kayi hak'uri bazan sakeba.
Yay mirmushi tareda sake rungumeta sosai yana shafa bayanta, ya ce, "na hakuta sopyna, amma kinsan ban tab'a ganin fareeda ba, nadai santa a labarine kawai.
Ta ce, "hakane".
ya gyara kwanciyarsa zuwa rigingine, ya ce, "bayan fita ta daga gida, asibiti na nufa, dan dubo yayan faruk da baida lafiya, nafito kenan tsautsayi yasa na bige fareeda da mota akan titi, wannan yasa na d'auketa muka koma cikin asibiti, aka karb'eta da gaggawa dan a sume take, amma ""ALLAH gafurun rahimun"" sai ta farfad'o da wuri, kuma babu inda taji wani mummunan ciyo saidai d'an guggurjewa, dan haka aka sallamemu, to sainace tafad'amin gidansu na kaita, saita shiga kuka ta ce, "batada gurin zuwa, to nikuma saita bani tausayi shine nace tabani labarinta, amma saita kasa tanata kuka, nikuma ganin haka yasa nataho da'ita gida dan ta huta, sannan idan inada halin taimaka mata saina taimaka mata, kinji yanda akai muka had'u.
Sopy taja ajiyar zuciya ta ce, "tomiyasa baka d'aga wayataba?.
Saida ya kalleta sannan ya ce, "na barta a motane, shiyyasa banga kirankiba.
Ta ce, "to, yanzu yakake gani zamuyi da fareeda?, dan gsky bazan iya zama da itaba.
Ya d'an murmusa tareda jawota jikinsa ya ce, "haba sopyna nasanki mai tausayice, kiyi hak'uri mu zauna tare harta warke, sannan saimu san abinyi, ko muje mubama baba hak'uri amaida ita gidan mijinta, nasan har yanzu kina k'yaunar fareeda, ki yafe mata sopyna ALLAH yana tareda masu hak'uri.
Ta ce, "uncle amma kasan fareeda ta cutar dani ko?, ya ce, "nasan haka sopyna amma ki daure ki yafe mata, aii wani hanin ga ALLAH baiwane.
Ta rungumeshi itama tana 'yar dariya ta ce, "gashima ALLAH yay min canji da samun gwarzon namiji mai ilimi da k'yau, ga nasaba.
Uncle G yad'ago fuskarta yana murmushi, ya ce, "sopyna nagode, amma taya nazama gwarzo? Tunda ban tab'a yin wani abu dazai nuna ni gwarzo bane.
Tayi murmushi tareda b'oye fuskarta a k'irjinsa ta ce, "kaima kasan kai gwarzone.
Cikin kunnenta ya ce, a wajen....... ya'arasa a hankali batareda najiba, ta kuma cusa kanta a kirjinsa tana fad'in nidai babu ruwana ga bily nan tana kallonmu.
Ya ce, "aii yanzu zan koreta, dan sa idonta yayi yawa.
🚶🏼nima sainayo waje tun kafin a koroni, nad'an lek'a fareeda naga har sannan barci takeyi, dan haka nima nataho wajen my sweet d'ina😜😜😎...............✍🏻
Kuyi hakuri jiya ba'ayi type ba.
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 7~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸4⃣3⃣🔸🔶
............Washe gari dak'yar sopy ta iya b'an b'are jikinta daga na uncle G!, dan tunda sukayi sallahr asuba suka koma suka kwanta, takula zaifara wani takale2, gashi yau zai koma aiki, tasamu dai dak'yar yabarta tashiga kichin ta had'a musu break, tana cikin gyaran falo fareeda ta fito, Sopy tayi burus da ita taci gaba da aikinta.
Fareeda ta daure ta ce, "mizan tayaki dashi sopy?.
Batareda ta kalletaba ta ce, "kibarshi kawai nama kusa gamawa.
Fareeda ta dage saita taya sopy aiki, Sopy ta ce, "kije ki kwanta kinsanfa bakida lafiya, fareeda tad'anyi murmushi mai ciwo ta ce, "Sopy kenan!!; karki damu da lafiyata dan nikaina batada amfani agareni, dan haka ki kawo natayaki kedai.
Sai asannan sopy ta kalli fareeda dake hawaye, saikuma jikin sopy yay sanyi, ta tabbata har yanzu tana k'yaunar fareeda, kawai b'acin raine yahana son tasiri dakuma danneshi datakeyi.
Fareeda ta surkushe agaban sopy tana zubar da hawaye, ta ce, "dan ALLAH Sopy ki yafe min, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, rud'in shaid'anne kawai ya kaini ga aikata kuskure mafi girma ga Aminiyata 'yar uwata, dakuma iyayena, kuyimin kowanne irin hukunci, indai zaku huce, ki daina fushi dani plz, ta rushe da kuka mai ban tausayi.
Sopy ta kauda kai itama tana hawaye, sunkai tsawon minti uku kowa yana kuka, sannan sopy ta d'ago fareeda ta rungumeta suka cigaba da kuka ahaka, uncle G yana tsaye yana kallonsu cikin tausayi, lallai yasan gurinnan ana k'aunar juna, shaid'anne kawai yashiga tsakanin aminan juna, har yay tasirin b'ata tsakaninsu, ganin kukan nasu bamai k'arewa bane yasa shi yin tafi, da sauri suka juyo suna kallonsa, yay murmushi mai k'ayatarwa, tareda fad'in lallai yau ranace mai tarin farinciki da tarihi, na godema ALLAH dayasa muku hak'iri azukatanku.
Su duka murmushi suke, farida tai surin dafe kujera danjin jiri yana d'ibarta, da sauri sopy ta ruk'ota tana tambayar lfy??.
Fareeda ta ce, "kainane, uncle G ! Ya ce, "ki kaita d'aki ta kwanta, to sopy tafad'a tana rik'eda fareeda, uncle G! yabisu da kallo yana murmushi.
D'aki yakoma ya kwanta dan dasauran safiya, sopy kuma taci gaba da aikinta, bayan tagama tanufi d'aki danyin wanka, amma saita tarar fareeda ta gyara d'akin tsaf, sopy ta ce, "kai fareeda keda nace kizo ki kwanta ashe kina nan kina aiki.
Fareeda tad'anyi murmushi kawai, wanka sopy tashiga ta tsantsara kwalliya cikin siket da riga na material tayi k'yau sosai, ta ce, "fareeda kema yakamata kiyi wankan dan kiji k'arfin jikinki, saiki fito muyi break, fareeda ta ce, "to.
D'akin uncle G! tanufa, yana kwance d'ai d'ai yana barcinsa, sopy ta kalleshi tana murmushi, lallaima mutuminnan kamanta yau zakaje aiki ko?, saman gadon ta hau, tad'an jamasa hanci, ya d'an motsa, tashiga shafa kumatunsa da saje yakwanta luf luf na bak'in gashi, ahankali ya bud'e idanunsa, ta nuna masa agogonsa data d'aukko a durowar gefen gado, ya ware ido sosai dan ganin lokaci, ya mik'e yana fad'in sopyna nakusa makara fa.
Sopy tayi dariya tana fad'in ato hutun nan yasa kafara mantawa da makaranta, ya juyo yana kallonta, ya matso daf da ita murya kasa2 ya ce, "ba hutune yasani mantawa da makatantaba aii.
Sopy ta lumshe ido ta bud'e ta ce, "to, miye?, yad'an rungumota gefen jikinsa ya ce, "sopyna ce ta shayar dani zuma mai d'an d'ano, harna manta da kowa da komai.
Safiyya ta kwace jikinta tana dariya, ta ce, "uncle nidai babu ruwana ga ruwan wankanka can a bayi, bayi yanufa yana murmushi, saida yaje bakin k'ofar yajuyo yana kallonta.
Ta ce, "miya faru kuma??, ya d'an marairaice fuska ya ce, "baza'a taimaka amin wankanba.
Sopy ta zaro ido waje tana fad'in rufani kasayani, yanufota yana fad'in to bari na rufaki na sayaki, da gudu tafita tana dariya, shima bayin yashiga yana dariya.
A gurguje yayi break dan yakusa makara, har wajen mota sopy ta rakoshi, ya kalli motar da mamaki dan ganin an gogeta tsaf, ya ce, "Sopyna sannu da k'ok'ari, amma yaushe kikayi aikin nan??.
Tayi murmushi ta ce, "da safen nan uncle, ya jawota jikinsa ya rungume tsam tareda sumbatar kumatunta, ya ce, "lallai nayi dace da samun mace tagari k'yak'yk'yawa mai hankali, ALLAH yay miki albarka sopyna, yabamu 'ya'ya nagari masu irin halayen nan naki.
Tayi murmushi tareda fad'in aikafini halaye masu k'yau, nafison 'ya'yanmu subiyoka tafad'a tana rufe fuska dan kunya🙈.
Uncle G! Yay murmushi ya ce, "sarkin kunya, ni bari nawuce dan karna makara dayawa.
Ta ce, "to ALLAH ya tsare ya kiyayeminkai!!, ka gaida min da mutane.
Ya ce, "amin, tareda mata hararar wasa ya ce, "ninema d'an aikenki??.
Ta ce, "A'a nina isa na aiki my sir d'ina, kuma sarkina.
Yay dariya, idan nadawo zaki gayamin waye sir d'in aii.
Sopy tashige gida tana dariya, shima yaja motar yatafi yana dariya, da k'ara jin yarinyar a zuciyarsa..................✍🏻
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.