Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 20 of 42
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow teamðŸ˜karkubari abaku lbrðŸ‘
*BOOK 2*
...18...
Saida nayi wanda ya isheni kafin na tashi daga wajen na nufi bakin famfo,fuskata na wanke wacce tayi ja ta kumbura.
Kai tsaye part É—inmu na nufa domin na kwanta,abubuwan sunyi mini yawa.
Da Sameer naci karo wanda ya fito daga mota zai shiga cikin gidan dana fito É—in.
Karo muka kusan yi,hakanne yasa na dan ja da baya ina kallonsa,shima kallon mamakin yake bina dashi. Bamu taba haÉ—uwa dashi ba a gidan,kasancewar lokacin dana zo an turashi wani aiki,idan ya dawo kuma baya daÉ—ewa yake tafiyah.
Ni na ganeshi saboda kamarsu É—aya da saleem,kalar jikinne kawai da É—aure fuskar ba iri É—aya ba.
Ganin kallon dayakemin ya wuce na misali yasa na raba zan wuce,jinayi yayi min magana wanda banyi zato ba sam.
"Wacce ke,amma dai ke sabuwa ce a gidannan koh?"
"Uhm"
Shine kaÉ—ai amsata,ohh wata tambayar na kuma jin ya sake jefa min.
"Miye Sunanki"
"Sumaimah"
Daga hakan nayi wufff na bar wajen gudun wata tambayar,nasan zayyi mamakin hakan,in halinsu É—aya ma da Mulaifah har yace na rainashi. Amma abinda bana É—auka shine Æ´ar aiki ba baiwa bace,tanada Æ´an cinta da kuma ganin dama akan rayuwarta.
Bayan la'asar shine fitowata daga sashenmu,tun ɗazu nake gardama da zuciyata kan bazan yiwa Ahmad girki ba,amma kuma wani bangaren na zuciyata ya hanani amincewa da ƙin yin. Koba komai nina ce naji nagani zanyi,sannan kuma bai kamata daga yin ɗaya na bariba. Koda yake nasan idan yayi aure ma bazan sake ganinsa sosai ba.
Kitchen É—in na shiga na fara haÉ—a kayan abincin dazanyi amfani dasu.
Jallop É—in shinkafah zanyi masa da wake,mai kifi da manja. Ba abincin Æ´an gayu bane amma na marmarine,bansan ko zai ci ba.
Bayan na gama juice kawai na É—auko masa a fridge na É—ora akan tiren.
Kaina a ƙasa yake nake tafiya wajen dinning ɗin,hankalina kuma baya jiki na sosai,ya tafi duniyar tunani.
"Mai kike gani haka kina shirin buguwa da table?"
A lokaci guda na dawo hayyacina,na kalli mai maganar kana kuma na sake juyawa na kalli table É—in.
"Ohh kayi haƙuri"
"Banine wanda zaki bawa haƙuri ba ƙafarki ce inaga,karki ajiye kawomin nan"
Saida yayi magana nakula ashe ba kayan aikine a jikinsa ba,har yayi wanka ma da alama,tunda ga nan damshin ruwa a jikinsa.
Kawowa abincin nayi na ajiye a gabansa,daidai lokacin da yake sanja tashar tv.
"Yau ka dawo da wuri"
A hankali nayi maganar,banyi zaton ma zaiji ba.
"Uhm"
Naji yabani amsa.
Daga nan shuru ne ya gibta harna gama zuba masa abincin na miƙamasa.
Karba yayi kafin na ajiye yasaka a gabansa. Yanda ba bata lokaci yafara saka abincin a bakinsa har saida yabani dariya,amma a yanzu banida wannan mood É—in.
"Me yake damunki?"
"Ehh!!"
Bansan lokacin dana bashi wannan amsar ba,tambayar tasa ta razanani,ni yake tambaya wai me yasameni?
"Ehh haka nace mai ya sameki,yau naga yanayinki ya sauya ba kaman kullum ba,bakida lafiya ne?"
"Ahah babu komai,zan iya tafiya idan baka buƙatar komai?"
Jin shuru baiyi magana ba yasa na É—aga kai na kalleshi,ashe kallona yake tsawon lokacin. Kuma kallone mai É—auke da alamar kulawa,ban taba ganin ya bini da irin wannan kallon ba sai yau.
Garamm mukaji shigowa cikin falon kaman an jefo bauna.
Ɗaga ido nayi na kalleta cikeda takaici, gabaɗaya wannan kuwa tasan mai ake ƙira da hankali. Barima na tashi na tafi,domin bazan juri wani tension ɗin ba.
"Ka gama da abincinne?"
Na tambayeshi har Sannan fuskata É—auke da damuwa.
ÆŠaga min kai kawai yayi,har sannan bai daina bina da kallon tambaya ba.
Kwanukan na É—ebe na nufi kitchen,ta gefensa na wuce tana tsaye ta naÉ—e hannaye,batamin magana ba bayan hararar dayayimin,nima kuma dama hakan nake so ai.
Juye sauran abincin nayi na wanke kwanukan,tun daga kitchen ina jiyo maganar Mulaifah,amma dai banajin abinda take cewa sosai.
"Haba D mai yasa kakemin hakane, karka manta fah har an kusa aurenmu wancan abin ya faru,kasan kuwa irin halinda na shiga. Dana jure sai gashi komai ya wuce.
"Wai nikam banaji ance kinyi aure ba,maiyasa kika kashe shi?"
"Saboda bazan iya zama da wani ba idan bakai bane"
"Shine kawai hujjarki"
Ba kunya ta É—aga masa kai kuwa.
"Hmmm ki tashi ki barmin sashe,karki ga don na amince da aurenki kiyi tunanin cewar domin ke na amince,hakan bazai sauya komai ba daga kallon danake miki"
"Karka ce haka D nasan zaka soni idan muka fara zama tare ina ƙarƙashin ikonka."
Daga haka ta tashi tabar falon,duk da maganganun daya faÉ—amata amma ko kaÉ—an basu wani dameta ba,tunda burinta na zama matarsa zai cika.
Da daren ma yau bamu huta ba,ummi sai mita takeyi,gwara suma sunsan ana hakan a gidan,nida bansani ba fah.
Idan akwai abinda za'a tattauna daman ana ƙiran family meeting irin haka. To ranar dukka masu aiki zasu haɗu suyi aikin,ayi dinner tare a babban falo kowa ya tafi bayan an tattauna.
"Mtsww ko akan me za'ayi wannan meeting É—in kuma oho"
Ummi ta faÉ—a wacce take zaune a kan kujerar kitchen É—in..
Kallo É—aya nayi mata na É—auke kaina tareda cigaba da zuba fried rice a cikin warmer.
Muryar inna ladiyo mukajiyo tana shigowa.
"Kun shirya komai da komai kuwa,kowa fah ya hallara yakamata akai abinci zuwa yanzu"
Cikin sauri na ƙarisa zuba abincin na ɗauka na fita.
Kaina a ƙasa na ajiye abincin a tsakiyar table ɗin.
Suna zaune a can tsakiyar falon,ban da hayaniya babu abinda sukeyi.
Dama haka sukeda ɗan yawa. Amma duk yawanci ƴan uwan hajiyah Mammah ne,sai ƙanwar babansu wacce take aure a maiduguri da ƴaƴan ta manya haka,Hajiya Aina'u sunata hira itada Maimuna.
Sai Fatee kuma da suke kallon abu a waya itada wacce naji Æ´ar hajiyah Aina'u ce Muneerah.
Bayan mun gama jejjera komai da É—aÉ—É—ai da É—aÉ—É—ai suka fara zama a dinning É—in.Wajen ya cika har Alhj Aliyu ma yazo da hajiyah Mammah.
Kowa sai gaisheta yake ana mata ya jiki,saboda ƙafarta tana ciwo abinka da jiki ya sha miya.
"Ahh how sweet,ba'a tabayin family meeting da zayyi min daÉ—i ba sai wannan"
Mulaifah ce ta faÉ—a wacce take zama a kujerar da babu kowa akai.
Blue material ne a jikinta yanata sheki,kaman wanda aka cemata yaune bikin.
Bayan an zazzauna iya manya masu wayo ne kawai a wajen,ƙananan yara kuma inna ladiyo da mai aikin hajiyah Mammah inna kareema sun tafi dasu.
Shuru wajen yayi naga kowa ya juya yana kallon ƙofah,nima waiwayawa nayi ina zubawa hajiyah Maryam abinci.
Caraf idona ya sauƙa a cikin nasa,don tunda ya shigo wajen idonsa akaina yake.
Inda nake ya nufo kai tsaye,mai kuma zayyimin ya taho wajena.
Kujerar danake gabanta naga yana shirin ja,hakan yasa na jamasa ya zauna kana na matsa. Fuskar mutanen wajen na kalla,dukkansu kowa yayi mamakin zuwan Ahmad wajen da alama,banda Alhaji Aliyu dakuma Mulaifah wacce take ta washe baki kamar gonar auduga.
Plate É—in gabansa na É—aga zan saka abinci,wani kallo yayimin nasan na gargaÉ—i ne,amma sai nayi kamar ban ganshi ba.
Zuba masa nayi na tura gabansa,haÉ—a ido mukayi amma bansan ya akayi ba na samu kaina nuna masa babu komai da idona.
Sauƙar da kai yayi tareda jan abinci gabansa kamar wanda akayiwa yaro dole.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.