Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 37 of 42
Sun barin wajen driver ya kawo hajiyah Mammah itada Kultum,lokacin tara na dare yayi.
Ta É—au wani glass tasaka,tana tattakawa a hankali.
Hannun A.M Aliyu yakama suka shiga inda take. Tana ganin halinda hajiyah Maryam take ta fashe da kuka tana gogewa da gefen zaninta.
"Allah sarki baiwar Allah,wannan wacce irin wahala ce haka kika gamu da itah Æ´ar nan?"
"Wlh nima Mammah bansani ba sai yanzu,a she ciwon yaci ya yacinyeta. Naso ma fita da itah,amma su yaran sun ce yakamata ayi na islamic ma,saboda abin yana kama da kamun aljanu"
"Eh to hakane kam kace wani abun,amma kasan fah akwai wani lokacin da ciwukan zamani sai kaga kaman na aljanu,sai anke asibiti kaga ashe zallan kamen ciwone"
"Wasu kam suna zuwa da haka,abinda yasa na yarda da maganar su likitocin munyi magana dasu,sunce wai basuga komai ba a jikinta,ko É—agawar da kirjinta yake sunce basuga komai ba."
"Hasbunallah,shikenan sai a yi na musuluncin,akwai wani malami zanyi masa magana akan matsalar"
"Hakan ma yayi,Allah ya bata lafiyan ya tashi kafaÉ—unta"
A.M Aliyu ya faÉ—a cikin damuwa.
Kallonsa hajiyah Mammah tayi tareda cewa ameen cikin ƙasan maƙoshinta.
∆∆∆
A bakin get Ahmad ya sauƙe Sumaimah,bayan yabata nata abincin,yaso rakata har sashensa,dan shi a son ransa yafison ta kwana a can, amma taƙi yarda,haka yayi mata sallama ya juyah.
Sashensu ta nufah,ummi da inna ladiyo sunata hira sun kunna fitila kasancewar sannan aka É—auke wutah,ba a kunna generator ba.
Sallama tayi tashiga É—akin,shuru sukayi suna kallonta,ganin yadda take tafiyah kaman an yi mata mutuwa.
"Ke kuma daga ina haka tun rana,kikaje kika É—ebo damuwa?"
Zama tayi tareda É—ora kanta a kan cinyar inna ladiyo.
"Inna ciwon hajiyah Maryam ya tashi,wannan karon har yafi nada,inna bakiga ba kaman bazata waye safiyar gobe ba,duk da rai da mutuwa na hannun Allah"
Hannunta ta É—ora akan Sumaimah tareda jan numfashi.
"Tana ganin jarabawa kam a gun matar can,amma in Allah yasa da sauran kwananta sai kiga komai yazo da sauƙi. Ki kwantar da hankalin ki,Inshaallah zata samu sauƙi"
Da haka inna ladiyo ta lallami Sumaimah taci abincin ta tazo dashi,hankalin ta kuma ya É—an kwanta ba kaman nada ba..
Dare ya fara kowa ya kwanta,amma Sumaimah gabaÉ—aya ta kasa bacci,sai juye juye take,tunowa da wani abu tayi. Zumbur ta tashi Zaune tareda saka mayafinta.
Lallabawa tayi a hankali ta bude É—akinnasu saboda karsu ummi su jita.
Ko tsoro bataji ba haka ta nufi sashen hajiyah Mammah ga duhu.
Tafiyah take kaman wata mai shiga É—akin fatalwa jikinta yana rawa,amma taurin kai ya hanata juyawa da baya.
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...35...
Motsi kaÉ—an taji saita haska,kuma dayake tasaka hakan a ranta har muryoyi takeji suna amsa mata kuwwa.
Key É—in falon ta É—akko,dan dama tana dashi saboda tana yi mata aiki.
Abinda zai bata cikas shiga É—akin hajiya Mammah ne,wanda batasan yana buÉ—e ba kokuma a rufe.
Murɗa ƙofar tayi,amma wannan kam babu zancen zai buɗe a lokacin.
Hankalin ta ya tafi wajen buɗe ƙofar,bata tsammata ba sai muryar Mulaifah taji a bayanta.
"Ke kuma mai kike anan wajen da wannan daren"
Cikin alamar maye take maganar tana tangaÉ—i,kana ganinta kasan ta hau air.
Ganin hakanne yasa Sumaimah wata dabarar ta faÉ—o mata.
Gyara fuskarta tayi alamar damuwa kafin tace.
"Am dama hajiyah Mammah ce tace na gyara mata É—aki,to kuma na manta ne sai yanzu nazo,gashi bata nan banaso tazo taga ban gyaraba"
"To kuma gyaranne zakiyi shi yanzu,ina Mamman taje ta?"
"Dare bayyi bafah sosai bakya ganine,ita kuma taje asibitine hajiyah Maryam batada lafiyah. Dan Allah kozaki buÉ—emin na gyara mata,yanzunnan zan gama"
Shuru tayi kaman mai tafiyah tunani kafin ta gyara tsayuwarta.
"Uhm banida key É—inta,amma nasan tana ajiyewa a Drawer tv stand dinta,amma fah ba ruwana in kika É—auka,don ta hana"
TafaÉ—a tana saka hannun ta a baki,kana ganinta kaga marar hankali.
Murmushi Sumaimah tayi jin barin zancen da Mulaifah take,kai dole ace giya haramunce,Sannan tana saka mutum yin komai da aka hana.
Bayan ta shige É—akinta wajen data kwantanta mata ta nufah. Cikin sa'a kuwa saiga key É—in,guda uku ne saida ta gwada dukkansu kafin ta samu wanda ya shiga.
Ɗakin duhune ƙirin,baka ganin komai,ga batada wayah bare ta haska.
"Kince zaki gyara É—aki amma bakida haske a hannunki,ga fitila ki gyara mata kizo ki fitah,dan bawani sonki nake ba kinsani. Ohhh"
Tana cikin maganar tasaki amai a É—akin.
Matsawa gefe Sumaimah tayi tana kallonta,itah harta manta tana gidan ma,rabonta data shigo gidan ta kusa wata uku,yau mai ya dawo da itah oho. Ga nan cikin jikinta ya fito sosai.
Miƙowa Sumaimah fitilar tayi tareda yin Murmushin masu shaye shaye.
"Ahhh abinka da mai ciki tana shaye shaye,so nake ba ya mutu kar yazo da rai,banason haifarsa ko kaÉ—an"
Taƙarisa maganar tana jijjiga hannunta alamar ahah.
Karbar fitilar Sumaimah tayi ta koma gefe tana kallonta,duk rayuwar data tsinci kanta taji tausayin kanta,amma wannan ta damata ta cinye akan wacce za'a tausayawa.
Bayan ta gama magangunun ta fita jan ajiyar zuciya Sumaimah tayi tareda rufe ƙofar.
Dube dube takeyi ko zata samu wani abu daya sabawa hankalin ta a É—akin,amma bata gani ba har ta shafe wasu mintuna.
"Wayyo Allah nah shin ina take ajiye abubuwan ta ne? Ohh ƙarƙashin gado,anan naga wannan fatalwar ta fito"
Tsugunnawa tayi ta leƙa ƙarshin gadon,har nishi take saboda girman da cikinta ya fara.
Ido biyu tayi da akwatin,batayi wani tunanin ba ta jawoshi waje.
A buÉ—e yake sai wasu kwalabe guda biyu a ciki. ÆŠayar a bude take ba komai a ciki,sai kuma É—ayar da wani jan abu a ciki.
ÆŠaga su tayi a hannunta tana kallo.
"Wannan kuma mai nene,ya nagansu a buÉ—e,ina abin cikin?"
Motsin mutum taji,ga fitilar da Mulaifah ta bata tana ta rawa,itama kuma jikinta yana rawa.
Dan muryar kaltum babu makawa taji,mai ya dawo da itah yanzu.
Bakin ƙofar tazo a garin tafiyah tayi tuntube kwalbar hannunta guda ɗaya ta faɗi,taji fashewarta kuma a lokaci guda ta taka bata saniba.
Zafine ya ziyarci ƙafartata har cikin kanta,bata tsaya duba ciwon ba ta fito daga ɗakin,daidai lokacin da kaltum tashige ɗakinta,hakanne yabawa Sumaimah damar ficewa daga sashen.
Muryar Kultum taji tana fadin.
"Waye anan,Mulaifah kece?"
Gudu Sumaimah ta fara jin Kultum ta biyo bayanta,wani lungu ta shiga da wasu fulawowi a wajen. Ban nishi babu abinda takeyi,tana cikin wannan halin aka kawo wuta wajen ya É—au haske,Allah ya taimaketa Kultum É—in ta wuce.
Kwalbar da take hannunta da kallah,sai yanzu ta gane ainihin kalarta,baƙace samanta a tsuke. Wani baƙin zarene a cikinta an cika shi tamm.
Zarewa takeyi tana zubarwa har saida ta cireshi tass tukunna ta mayar kwalbar ta rufe ta nufi sashensu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.