Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 26 of 42
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...24...
Hankalinta kwance ta haɗa komai a hankali,don tasan tunda yace bada wuri ba,wataƙila ma sai wajen magriba su ganshi.
Bayan ta gama komai jawowa sashen tayi amma bata kulle ba,tunda tasan babu mai shiga idan ba itaba kokuma wani inya gayyaceshi.
Tafiya take tana ƴar waƙa,tamkar babu abinda ya dameta,tana shiga sashensu banɗaki ta faɗa domin ta ɗauraye jikinta,don tun ranar farkon da Ahmad ya kamata tayi wanka a banɗakinsa bata sakeyi ba,tanaso ya yarda da itah,idan zatayi nasara to sai ta haɗa da kiyaye irin waɗannan abubuwan.
∆∆∆∆
A bangaren Mulaifah kuwa tun safe aka kawomata maganin da zatayi aikin dashi,(sildenafil viagra).
Tana tsugunne a garden taga shigewar Sumaimah ta dawo daga sashennasa,
Hakanne yabata damar itama shigewa sashen.
Bayan ta shiga kunkumi takama tareda yamutsa fuska jin yanda ƙamshin turare yakama falon sosai.
Takawa tayi zuwa kan dining inda Sumaimah ta jera kayan abinci,saida ta buɗe tagani kafin ta fito da maganin. Gorar ruwa ta buɗe ta zuba overdose,yanda zayyi aiki yanda yakamata,kuma ta sanshi sarai idan bai gusar masa da hankali ba to zai iya riƙe kansa..
Murmushin mugunta tayi tareda rufe komai kaman bata tababa ta juya ta tafi.
Tana fitowa daga falon ta ƙira padush tareda labarta mata.
Lokacin har an fito daga sallahr magriba.
∆∆∆
Bayan Sumaimah tayi sallahr magriba bata tashiba saita fara karatun ƙur'ani har akayi sallahr isha ta tashi tayi,tana nan zaune akan daddumar taji wayarta tayi ƙara,sunan Ahmad tagani,ya dawo kenan ta faɗa a ranta.
ÆŠagawa tayi tareda yin sallama.
"Ka dawone ya hanya?"
"Lafiya ƙalau,shin kin rufe min drawer ne?"
"Ehh na rufe"
"Ina kika saka key É—in,zan É—auki wani document ne akwai abinda zan duba da darennan a ciki"
"Waii ai na taho da key É—in a jikin wanda ka vani na sashenka,amma ina wanda yake wajenka"
"To na wajennawa ne yafaÉ—i ai banganshi ba,kuma ma yanzu zaki bani ki tafi,nasan daren yayi ai"
Daga haka ya kashe wayar tasa,kallo Sumaimah tabi da wayar tareda tashi daga kan sallayar,wato ya É—ebo gajiyarsa yanason hucewa akan ta.
Da hijabinta na sallah a jikinta ta É—auki key É—in ta nufi sashennasa.
Ta baya tabi bata shiga ta cikin gidanba,duk da ba komai zatayi ba amma kada su zargi wani abun.
Ƙwanƙwasa ƙofar tayi shuru,har tagaji ta buɗe ta shiga,a wajen dining ta ganshi,a gorar ruwa a hannunsa,a ƙasa kuma ya zubarda juice ɗin da ya haɗa.
Juyar da ido tayi tareda miƙa masa key ɗin,wani lokacin mamaki yake bata idan yana abu kamar yaro.
Ɗauke jug ɗin tayi a ƙasan ta rufeshi,hanyar kitchen ta nufah zata ɗauko mopa,maganar sa ce ta tsayar da itah.
"Mai zakiyi a kitchen yanxu?"
"Wannan wajen zan gyara mana kafin gobe ya bushe,kuma da alama sai iya shiga ƙasan kujera"
"Amma dare yayi ki gyara nan wajen kuma......"
"Karka damu yanzu zan gama na tafi"
ÆŠaga mata kai yayi tareda shigewa É—akinsa.
Bayan ta É—auko mopar hijabinta ta cire ta ajiye akan kujera.
Tazo matsar da gorar ruwan dayasha sai taga abu ya taru a ƙasan robar,abinne ya bata Mamaki,mai ya kawo wani abu cikin gorar ruwa kuma.
Ɗagawa tayi tana jujjuyawa,kaman an ce takai idonta ƙasa saita hango ƙwayar magani a ƙasan table ɗin,tsugunnawa tayi da sauri ta ɗauka tana jujjuyata,tabbas ɗazu ta gyara wajennan bataga komai ba.
To kennan waye yashigo ya ajiyeta a wajen,da alama kuma irinta aka saka a cikin gorar ruwan,wani abin tashin hankalin wanda aka hara da koma mai nene yariga da yasha.
Hannayenta ne suka fara rawa kana da dukka ilahirin jikinta.
Saurin tashi tayi kaman an tsikareta tayi É—akin Ahmad É—in da gudu.
A bakin gado ta ganshi ya kifah kai,hannunsa kuma yana kan cikinsa ta ƙasa,babu riga a jikinsa daga shi sai gajeren wando.
Ga drawer ya buÉ—eta ga kuma kayansa a gefe..
Da gudu ta nufeshi tareda zama a gefensa.
"Wayyo dan Allah kada ka mutu ka tashi muje asibiti,wayyo Allah mai kayi musu zasu kasheka"
Riƙo hannunta yayi gam,hakan yasakata tsayawa da yin kukan ta kalleshi.
Shima itan yake kallo,idanunsa sunyi jawur tamkar garwashin wuta. Magana yakeson yi,amma fatar bakinsa rawa takeyi,kana gani kasan yaƙi yakeyi da wani abu dayake son tasowa a cikin jikinsa.
"Ki......kitafi.....ki rufe ƙofar kada ki kuskura ki dawo..."
"Meyasa mai kake nufi,wanine yasaka maka abu a cikin ruwa Kasha,kuma da alama mai illah ne,inaga ma guba ce tunda tasaka maka ciwon ciki,dan Allah ka tashi muje asibiti"
"Nace. ....kkkkitafii Sumaimah,meyasa bakyajin magana,Ko so kike na rasa tunanina na aikata miki abinda dukkanmu zamuyi danasani....."
Shuru tatsaya tana kallonsa,dan har yanzu bata gano mai yake faruwa ba,saida ya daka mata tsawa kafin ta tashi ta fita tana share hawaye.
Harta fita daga sashennasa sai kuma tagano alamar motsin mutum yana tahowa zuwa inda take.
Gabanta ne yafara bugawa,don a zatonta ko hajiyah Mammah ce zatayi siddabarunta.
Komawa tayi a hankali zuwa falon ta rufo ƙofah tana leƙowa ta glass ɗin ƙofar.
Saida ta matso kusa kafin taga Mulaifah ce,tana tafiya tana waiwayawa tamkar munafuka.
'To ita kuma mai haÉ—inta danan wajen zatazo goman dare.'
Shine tunanin da Sumaimah tayi wacce take kallonta ta glass ɗin ƙofah.
Ganin sashen Ahmad ta nufo zata shiga,hakan yasa Sumaimah tayi saurin saka key wanda yake hannunta,saboda kada ta shigo ta ganta a ciki itama da daddaren,amma kuma Ahmad yana buƙatar taimako. Kai amma ba a wajen wannan ba.
Murɗa ƙofar tayi ta jijjiga amma shuru,kaman zatayi kuka tayi,duk Sumaimah tana kallonta.
Wayarta ta ɗauko ta danna ƙira,can bayan an ɗauka tace.
"Padush ya rufe ƙofar bayan ma,tayi ta bugawa har mai gadi na yaci yaji,amma shi bai buɗe ba,kumafah bai daɗe da shiga ba,baici maganin ya fitar masa da hankalin sa ba zuwa yanzu,kuma hakanne ma zaisa ya buɗe da wuri ai.........ohh padush yazanyi ne,idan bai buɗe ba asirina zai tonu in aka gane inada ciki a gidannan..........najira menene,ni haƙurina ya ƙare,idan bai buɗe ba yakwana bayyi releasing ba maganinnnan zayyi masa illah,karnaje nayi silar hakan,kinsan ina sonsa..........wayyo nashiga uku,yanzu duk plan ɗin dana wuni ina haɗawa ya vaci,shiya sani yasan yadda zayyi,in wani abuma ya sameshi babu wanda zaisan nice"
Bayan ta kashe wayar juyawa tayi kaman zatayi kuka,duk abinda take kuma take cewa Sumaimah tana kallonta. Wani ƙululun baƙin cikine da kuma na tashin hankali suka haɗu mata a cikin ƙirjinta.
"Oh dama kece,kuma abinda kika saka masa kenan a cikin ruwansa,sai yanzu na kamo bakin zaren,wato so kike ya kwanta dake ba'a cikin hankalin sa ba,saboda ki laƙaba masa cikin da kika iyooo"
Hannu Sumaimah tasaka a ha'barta tana jinjina lamarin..
Ta É—an daÉ—e a wajen,saida ta tabbatar Mulaifah ta tafi tukunna kafin itama ta murÉ—a zata fita.
Har ta saka ƙafarta a waje saikuma maganar Mulaifah ta dawo cikin kunnenta.
Cewar in ya kwana batareda mace ba ya samu matsala shiya sani.
Maida ƙofar tayi ta rufe bayan ta dawo cikin falon.
Safah da marwa tafara tana tunanin abinyi,itadai in tace zata samo makarin maganin dayasha a daren to tayi ƙarya,sannan shin wa zata nema yabata shawara akan ya zatayi.
Wayarta ta ɗata ta danna ƙorna Neelah.
Can kaman ringing biyu ta É—aga,muryar tarau take da alama batayi bacci ba.
"Hello anty Neelah kina jina?"
"Ehh ina jinki,yadai jikin mommy ne ya tashi?"
"Ahah daman............"
Kaff ta zayyane mata abinda yake faruwa,ajiyar zuciya tasake bayan ta gama jin abinda yake faruwa.
"Kai amma wannan yarinya akwai shegiya,wai su bazasu barshi ya huta bane? Kinsan miye,yanda ta faɗa gaskiya ne zai iya yimasa illah,tunda tace overdose tabashi,sannan ni bana nan ina kaduna bare na samo masa maganin dazai karya wanda ya sha. Abinda za'ayi tunda ke matarsa ce dole kene zakiyi masa magani,kuma dama hakan haƙƙinki ne......saidai kiyi haƙuri zakiji jiki sosai tunda baya hayyacinsa....."
"Bakomai dama nayi tunanin hakan,na tambayi shawararki ne kar hakan yazama kuskure,musamman da rayuwarsa ke cikin hatsari"
"Shikenan kiyi haƙuri kikuma jure,komai zaizo da sauƙi Inshaallah"
Kashe wayar Sumaimah tayi tareda kasheta,hanyar É—akinnasa ta nufah cikin sanyin jiki.
A hankali ta murɗa ƙofar ɗakin,yana nan a inda ta barshi,saidai yanzu daga inda take tana hango yanda jikinsa yake rawa.
Ƙarar maida ƙofar da tayine yasakashi ɗagowa ya kalleta,zuwa yanxu kam ya sanja kamanni.
Takawa take a hankali tana nufar inda yake,yayinda shikuma yake binta da wani mayen kallo mai cikeda fassara,gabanta dukan tara tara yake har ta zauna a bakin gadon.
Hannunta ta É—aga zuwa kannasa hannun,wanda jijiyarsa suka fito raÉ—a raÉ—a,tausayinsa ne ya tsirga mata har cikin ranta,wanda hakan yasakata fashewa da kuka.
"Kayi haƙuri ka yafemin,nasan hukuncina bazayyi maka daɗi a gobe ba,amma kayi haƙuri dan Allah"
Tana gama faɗin hakan takai bakinta saitin nasa,kaman dama riƙewa yake,amma yanzun ƙarfinsa ya gaza control ɗin ƙishirwar da take cikin ransa,hakan yasaka mai makon yaji haƙurin da take bashi,saima sumbatarta daya farayi a zafafe.
Kuka take tana cize baki jin yanda yake yamutsata,tun tana jin da ɗan ƙarfi a cikin jikinta harta daina ji.
Ta daÉ—e tana É—anÉ—anar azabar,har saida maganin yasakeshi jikinsa ya sake laraff baccci ya É—aukeshi,kafin itama tasamu damar runtsawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.