Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 12 of 42

.......

Neelah ce ta kalli hajiyah Maryam wacce suke zaune a cikin mota suna kallon videon Sumaimah tana bincike É—akin hajiya maryam.
Tun daga shigowarta É—akin har zuwa fitarta duk suna kallonta, a cikin videon da camera take É—auka.
Sai bayan sun gama kafin Neelah ta kashe tana kallon hajiyah maryam.
"Kingani koh? dama saida na faÉ—amiki jiya ta ganmu kika ce bata ganmu,kina kallonta kaman batasan mai take ba,amma itama ta wuce yanda kike zaton,wannan takardun na jiya take nema"
Hajiya Maryam ce tayi maganar cikin wani murmushi na gefen baki.
Cikeda mamaki Neelah tasake kallonta a videon kafin tace.
"To ita kuma mai nata nayin wannan binciken,batasan ma takardun menene ba,idan ma tasani mai zatayi dasu,tana bayan Ahmad ne?"
"Ohh tambaya ma kike bayan kinsan komai,uhhhh hakan da tayi kuma yasa ta burgeni,batada tsoro da duhun kai,tasan mai takeyi sannan na kula bakaman sauran Æ´an aikin ba tasan mai takeyi,ta wuce yanda nayi zatonta ma"
"Hajiyah shikenan haka zamu barta bazamu tsayar da itah ba"
Jijjiga kai tayi tareda yin dariya.
"Batta tayi bincikenta,tana da damar yin hakan,karki hanata saima ki bata satar amsar hanya,duk abinda ta gano zanga shin zata iya ɗauka kokuma zata kasa,duk hakan yana cikin gwajinta kafin takai irin macen da nake so. Ko ajiyeni a wajen aiki ki wuce,kwanannan banason yaran sojojincan sun faye caja kai.....Daga can kije ki faɗamasa abinda na gaya miki na binciken dayace kuyi masa,karki yarda ki bari ku ƙara daga haka"
"An gama hajiyah zamuyi yadda kika ce"
Jan motar tayi zuwa inda hajiya Maryam take aiki,wani babban wajene ya haÉ—a komai da komai na taimakon talakawa da marayu,kama daga sana'a harma da koyarwa.
"Ki bari basai kin rakani ba san tafi,ki cewa samuel yazo da motata ya É—aukeni in anjima"
"To"
Fita tayi daga cikin motar tashiga wajen,cikin tafiyar isa da aji take tafiyah har ta bace,a yanayin shekarunta ba mai cewa zata iya tafiya da irin wannan takalmin idan ba gani yayi ba.
Ƙirane ya shigo wayar Neelah wacce take ƙoƙarin tada mota,dakatawa tayi tareda dagawa.
"Ehh eemran kana inane,yanzunnan zan tafi headquater,kaima kayi sauri saimu haÉ—u a can"
Taka motar tayi da gudu domin isa inda zataje akan lokaci.

A tsaye yake a gaban mutumin wanda kamanninsa suka sauya baka gane komai a fuskarsa saboda wahala da kuma dukan dayasha.
Ɗayane daga cikin ƴan kungiyar BC wanda aka kama shekara biyu baya,duk yadda za'ayi dashi yayi magana amma yaƙi,da haushi ya ishi masu tambayar sukayi masa lahani sosai.
Yanzu ma cewa yace a kawo masa shi ko zai iya gane wani abun,duk sun tabbatar masa da yazama mahaukaci ai da daÉ—ewa,shikaÉ—ai sai yayi ta dariyah yana cizon baki.
Anyi kimanin awa guda kenan Gen Ahmad yana gabansa,amma yaƙi cewa komai.
"Kai É—ago ka kalleni shin ka sanni?"
Amma shuru kaman yana magana da kungi,wani yashigo wajen tareda sara masa,kana yafara da cewa.
"Gen Neelah da Eemran suna neman izinin shigowa,tun É—azu suke waje"
"Kace musu su shigo"
Neelah ce tafara shigowa kana Eemran,gaisheshi sukayi kafin Neelah ta miƙa masa wani file..
"Yallabai ga bayanan da muka samu a asibitin,bayan tsawon bincike bamu samu komai ba,saida muka duba files na hotunan marasa lafiya har na shekara biyun kafin muka gano naka."
Tun kafin ta gama bayanin ya buÉ—e file É—in yana kallo.
Hotone kawai a jiki sai suna ta sign.
"Gojee???"
Shine abinda Ahmad Ya faÉ—a cikeda mamaki..
"Miye kuma goje,narasa sunan da zanyi amfani dashi sai goje?"
"Eh goje ƙwarai kuwa goje,shine shugaba ai na yanzu goje baaa"
Mutumin dayake gabansu ne yafara faÉ—a yana wasa da babyn robar da take hannunsa.
Da sauri Ahmad ya tsugunna a gabansa tareda cewa.
"Eh shi kasanshi?"
"Hhhhhhhh goje bindigar roba ba"
Tsuka yayi ya tashi tareda sake kallon su Neelah.
"Shikenan iya abinda kuka samo,waye to ya kaini asibitin,ƙungiyar BC ce?"
Jijjiga kai Neelah tayi kafin tace.
"A yanda suka faɗa mana kuma kaga wannan saka hannun,sunce matarka ce ta kawoka asibitin,itace ma take zaune a wajenka har ranar daka tafi. Sannan bayan ka tafi tasuma suka karbeta a asibitin,har sukayi mata test na juna biyu....bayan sun sallameta kuma basusan ta da kuma daga inda take,amma sunce jininta ya hau sosai ga yaron ciki,da ƙyar idan batayi barin sa ba"
Zaro ido Ahmad yayi yana kallon Neelah kamar ya samu madubi,mata da kuma ciki nasa wai? Abin takaicin kuma bai tuna komai ba? Tabbas daya tashi kam yaga wata mace a gefen gadonsa a kwance,kaico da bai tasheta ba,yasan da duk baisha wannan wahalar ba.
"Taya zakuce to babu sunanta da kuma garin da take,wannna ba abune da hankali zai ɗauka,kuxo muje asibitin ina buƙatar duk wani bayani daya shafeta"
"Am sorry sir,amma mun iya ƙoƙarinmu amma bamu samu komai ba,ƙarshe ma sai suka ce wai anyi musu kutse waccar shekarar,to a lokacin sun rasa data da yawa na bayanai"
Wani gumi ne ya yanko masa,bai san lokacin daya samu waje ya zauna ba yana dafe kai,wannan wane irin abune ne haka.
Tashi yayi zai fita,har yaje bakin ƙofa mai kulada wajen yayi masa magana.
"Sir ya zamuyi da wannan mutumin?"
"Zai warkene?"
"Ahah ƙwaƙwalwarsa ta lalace ba lallai va"
"To kuyi duk yanda zakuyi dashi,kai Eemran ran ka rufemin office É—ina bazan koma ba,gida zan tafi"
A hanyar zuwa motarsa yaji wayarsa tayi ƙara,shareta yayi harta katse,saida aka sake ƙira kafin ya fito da itah ya duba.
Hajiyah maryam ce take ƙiransa,har bazai ɗaga ba saikuma ya danna ɗauka.
"Har haka na zama a wajenka saikaga dama ka ɗau ƙirana?"
"Shin me kike buƙata?"
"So nake kazo inda nake akwai maganar dazamuyi?"
"Inada........"
"In kanaso kaji sunan matarka da kuma a wanne gari take to kazo inda nake,sannan kayi abinda nace"
Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar,sauƙe wayar yayi a kunnensa tareda runtse ido,abin bai wani bashi mamaki,domin hakan ba shine farau ba. Yarigada yasan bashida wani mutum ɗaya daya yarda dashi wanda ba nata bane.

Ƙofar motar ya buga tareda jingina kansa a jiki.
Yakai aƙallah minti biyu a haka kafin ya buɗe motar ya shiga.
Kai tsaye ma'aikatar data buÉ—e ya nufah,ransa badan yaso ba saidan bashida zabi.
Get É—in aka buÉ—e masa ya shiga,mutane sai zirga zirgarsu sukeyi,a ransa yace hankalin su kwance kaman basu san da wacce suke zaune ba.
Bayan yayi parking kai tsaye makeken office É—inta ya nufah,babu sallama kawai ya saka kai.
A zaune take a kan kujerar da take gaban makeken wani tebur,magana sukeyi da wata. Ta gefen ido ta kalleshi kafin ta cigaba da maganar ta.
Shikuwa ganin haka yasa yakama wata kujera a gefe ya hakimce akanta. Fuskarsa babu yabo ba fallasa,duk tururin dayake cikin zuciyarsa amma haka ya shanye shi ya bayyana tamkar a nutse yake a zahiri.
Bayan matar ta fita zuyawa hajiyah maryam tayi akan kujerarta tareda ƙare masa kallo daga inda take zaune.
"A tunanina ba ƙirana kikayi domin ki ƙaremin kallo ba,dan haka ki tafi kanki tsaye maganarki,mai kike buƙata?"
"Nima a nawa tunanin ko baka É—aukeni uwaba,naci darajar na haifi yakai,kokuma na amsa sunan matar ubaka koh.....dan haka ba gaisuwa ne malam Ahmad?".
ÆŠauke da murmushi akan fuskarta tayi maganar,inba wanda yasan abinda take aikata masa ba ko shi kansa,mutum zai É—auka a yanzun ba kallon tsana take aika masa ba sai na ta raina wayonsa,ta guma dariyar yanda ya tsime fuska shi a dole kada ta rainashi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.