Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 23 of 42

(Ba anan gizon yake saƙaba,nan hasken dana samu a rayuwata kenan kafin duhu ya lullubeni wanda bai yaye ba daga duniya ya har yau)

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...21...

Kinsan mai na tarar bayan naje ƙasar england,Muhammad yanada mata,juliat amma ta musulunta ta koma Amina,saboda soyayyarsa yasa ta zama ɗaya daga cikinmu,shikuma ya aureta ne yasaka ta a ƙarƙashinsa gudun kada ta sake komawa gidan jiya..
Baƙar fatace ƴar garin benue,karatu ya kaita can ta haɗu da Muhammad,anan ta ƙwadaitu da musulunci amma saidai in zai aureta yazama tana ƙarƙashin ikonsa,saboda iyayenta bazasu karbeta ba.
Daya zo wa abbanmu da zancen bai ja ba ya amince masa,ganin niyyarsa na inganta rayuwarta.
Lokacin danaje naga part biyu a gidan tana É—aya naji tsoron zama da itah,kuma nayi mamakin yanada aure ba'a sani ba,ashe mu yaran gidanne kawai bamu sani ba.
Bayan sati É—aya na zuwannawa na saki raina ,ganin tanada mutunci sosai,sabon addinin nata kawai tasaka a gaba sai kuma karatunta na medicine da takeyi.
Nima a makarantar da take na samu gurbin yin masters wato oxfort.
Muhammad ne yake ajiyemu a makarantar kana ya wuce wajen aiki.
Zamane mukeyinsa na mutunta juna,kowa yana harkar gabansa,a bangaren mijinmu kuma muna samun soyayyar sa fiyeda tunanin mai tunani,domin shiɗin mutum ne da sai an bincika kafin a samu tamkarsa wajen bawa mutum haƙƙinsa.
Kwanci tashi har munyi shekara guda da aure,ita kuma amina tayi shekara biyu.
A lokacinne kuma aka zo auren zainab,murna ta komawa ciki tayi,saboda a lokacin ba dama naje ina project na gamawa ta.
Sai Muhammad ya tafi shida Amina,dama tunda tayi aure bataje ba.
Satinsu ɗaya suka dawo,zainab har kuka tayimin akan banje ba,amma sai haƙuri na bata.
Tare suka dawo da hajiya Mammah akan zatazo taga É—akinmu. Itakam daman hajiya Fatima bazata zo ba tana kunyar dan fari irinna fulani.
A ranar da suka dawo na tashi da zazzabi, dan ma Muhammad na É—akina,domin nasha wahala sosai da daddare,amai ga zafin jiki.
Washagari da safe ya kaini asibiti,Amina Da hajiya Mammah basu sani ba suna sashen Aminan.
Gwajin farko aka cemin inada ciki na wata uku,nayi murna sosai musamman dana shafe shekara guda daman babu komai..
Shima Muhammad yayi farinciki fiyeda ni,ganin bayan shekara biyu da aure zai samu É—a ko Æ´a.
Da safen Muhammad ya tashi su hajiyah Mammah ya faɗamusu,itakam Amina ana faɗamata a take ta rungumeni tana lelleƙani,har ta bani tausayi,saboda ni kaina shaidace akan son yaranta,don abinda take karanta ma kenan a bangaren karatunta.
Itama hajiyah Mammah kabbara tayi tareda É—aga hannu sama.
Waya Muhammad ya ciro akan zai ƙira gida,amma hajiyah Mammah ta hanashi,a cewarta ya barta takai wanann albishir ɗin gida.
Da farincikinsa ya amince da maganar ta.
Tun daga wannan lokacin nafara ganin gata a wajen Muhammad,Amina kuwa ko ban nuna alamar komai ba saita gwadani. Satin hajiyah Mammah daya ta tafi gida.
A haka nikuma na cigaba da rainon a cikina,akan cewar idan cikina yazo haihuwa zan koma gida na haihu. Naji daÉ—in hakan sosai lokacin danaji Muhammad ya faÉ—a.
A ranar dana shiga wata na tara muka kamo hanyar dawowa gida,murna a wajena bazata boyu ba.
Bayan mun sauƙa mun kai kaman minti biyar ba motar datazo daukarmu,nikamma harna gaji,saida suka samamin kujera na zauna,Amina sai sannu takeyimin.
Munan nan zaune wata mota ta zo baƙa,wani mutum haka gajere ya fito daga motar, wannan kuma wanene,bansanshi a gidan ba ko sabon driver ne.
Nidai tun kafin su É—akko kayanmu na ja jiki zuwa cikin motar,dama na gaji.
Tafiya muke amma maimakon hanyar gida sai naga suna wani waje daban,Muhammad ne ya fara ƙoƙarin yiwa drivern magana,amma sai ya shaqa masa abu a hanci.
Ganin haka yasa muka saka ihu nida Amina,domin abin ba ƙaramin razana mu yayi ba.
Duhune ya fara lullube ganinmu,yayinda hankalin mu yake neman hanyar fita daga cikin kanmu.
Kafin idona ya ƙarisa rufewa naga drivern ya saka facemask,yana kuma magana da wani ko wata a waya.
Ruwa aka watsamana,shine sanadiyyar buÉ—e idanummu muka ganmu a cikin wani cell.
Wajen kaman kango yake,amma a rufe kirif domin badan hasken da aka kunna na za'a samu duhu a wajen..
Jijjiga ƙarfen bakin ƙofar nake ina kuka tareda ƙiran Muhammad da zainab,a zatona basa wajen,sai can bayan wani ɗan lokaci tukunna naji tarin Amina,ƙiran sunanta nafarayi sai can ta amsamin a galabaice,mai suka mata? Ina Muhammad yake shi.
Kafin na samu mai bani amsa naji takun sawun mace yana tahowa.
Wata mata ce ta rufe kanta da baƙin ƙyalle,bana gane wanne irin kallo takemin saboda bana ganin fuskarta sosai..
Batayi min magana ba,sai bada umarni da tayi da yatsun hannunta.
Kaman abin tsafi haka naji ihun muryar Amina da kuma Muhammad..
Zare ido nayi tareda fara jijjiga ƙarfen wajen,wayyo wacece ita mai takeyi musu da hannunta?.
Maganar data gefenta tayi yafi komai É—agamin hankali.
"Ranki ya daɗe sun ƙarisa mutuwa a yanzu"
"Ku sakata a wajen ajiyar gawa,shikuma ku kaishi bakin hanya daidai inda za'a ganshi"
Mutuwa mai take nufi,kashesu tayi kenan meyasa??
Ƙara na sake mai cikeda firgici,wanda sanadiyyar hakan ya haifar min da yankowar ruwa ta ƙasa na,nishi na fara cikin kukan,wanda bazan iya tsaidashi ba..
Jin kalar nishin danake fitarwa ne yasakata itada matar juyo da hankalin su gareni.
Nan ma kaman abin tsafi ƙofar cell ɗin danake ciki ta buɗe,jan hannuna mataimakiyar tata tayi zuwa wani ɗakin daban,duk da halin danake ciki amma sai duka nake kaimata zan ƙwace,shikenan sun kashemin mutane biyu kenan danake rayuwa dasu,shikenan bazan sake ganinsu ba. Wayyo mijina,zan haihu batareda yana wajen ba,dukkuwa tsananin muradinsa na son ganin gudan jininsa.
Saboda tashin hankalin danake ciki hankalinnawa ya gushe lokacin da jaririn ya faÉ—o daga jikina.
Ihun sane ya dawo dani cikin hayyacina..
Duk halin da nake ciki hannuna na rawa na miƙa hannun zan dauke,amma haka naga wani hannun dayafi nawa hanzari ya ɗauke.
Binta nayi da ido ganin yanda ta riƙe a jaririn a hannunta tana jijjiga shi da jininsa da komai.
Hanyar fita daga ɗakin naga ta nufah,da gudu na bita a baya har ina faɗuwa saboda rashin ƙarfin jiki,domin a zatona kasheshi zatayi kaman yanda ta kashemin mijina.
Inda ta kawoni nagani,babban falone amma ba komai ne a cikinsa ba banda wata kujera,wazan gani a kai matar nan ce mai hula wacce ta kashemin miji.
Baƙin ciki naji da fargaba lokacin danaga matar tasaka mata yarona akan hannunta,bai kamata zuwansa duniya kenan ya hau kan hannun waɗannan azzalumanba.
"Maryam"
Naji ta ƙira sunana,muryar tayimin kaman nasan wacece,amma kuma mai zai kawota nan wajen,mata kamilah mai ɗumbin ilimi.
"Nasan kin gane muryarta,kina shakkane kawai da tunanin nice kokuma ba nice bace,to niɗin ce dai wacce ƙwaƙwalwarki ta baki"
Saka hannun tayi ta zare hular kanta,"hajiyah Mammah" shine abinda na faɗa cikin mamaki da ƙarfi.
Dariya ta sheƙe dashi tareda cewa.
"Karkiyi mamakin hakan,komai ya faru ke kika jawo ba kowa ba,san kanki ne dana mahaifinki ya jawo komai.
Ɗana ya nuna miki so,nima na nuna miki so amma haka kika tsallake kika tafi taki rayuwar,shi kika barshi a cikin duhu. Duk wanda zan nuna wa kulawa da so ƙarshe wajen fatima yake komawa,ni a barni dagani sai ƴaƴana,shikansa Hamma ko ƙafarsa zan tsugunna na lasa haka zai take harshena ya tafi wajenta. Dan haka wannan ya ƙare, duk sainaga bayan kowa amma bandake ke kaɗai.
Kinsan meyasa? Saboda kece soyayyar Aliyu ta farko,amma akan idonsa yarasata aka bawa Muhammad saboda son kai,kukayi ta murnar biki da shagali,nikuwa babu wanda ya kulada ni da Æ´aÆ´ana,ina ji ina gani yabar gida amma babu wanda ya tsaida shi bare yayi masa abinda yake so.
Har lokacin da kikayi aure inada yaƙinin kashe aurenku,ba yanda banyi ba abu yaƙi yiyuwa,ƙarshe ma wai harda ciki gareki. Hakanne yasa nayi muku gabaɗaya,yanzu dolene ki auri Aliyu tunda Muhammad ya mutu"
"Bazan aure shi É—in ba,badai kisane aikinki ba to ki kasheni nima amma bazan aure shin ba"
Dariya tasake tuntsirewa da itah.
"Mai kike nufi,dama nasan ai zaki ce haka,zan baki zabi guda biyu.
Ko kiƙi amincewa na kasheki,na kuma kashe wanann yaron.
Ko kuma ki amince da ƙudurina,nikuma zan bar ɗanki da rai,amma da sharaɗi duniya bazata shaidashi a matsayin ɗanki ba,saboda bazai yiwu ki auri ɗana zaki haifamin jikoki yazamana kuma wanann yana ranki ba.
Dan haka zai shiga alhalin Hamma ne a matsayin amina,dama already na faÉ—a musu cewar itace da ciki bake ba"
"Kutt mai kika ce, itace da ciki bani ba?"
"Da mai kike nufi,har abada bazan bada wannan lbarin ba,ke din dan Aliyu aka halittoki ba Muhammad ba,dan haka bazan taba bada albishir na kinada cikinsa ba sam.
Yanzu zabi ya rage ga naki. Zan baki wata biyu ki zauna anan ki gama bawa ɗanki soyayya,daga nan kuma dole tsana zaki dunga nuna masa,ke zaki raineshi amma raino na azaba,duk ranar da soyayyar sa ta ɗarsu a ranki to sunansa matacce,saiki zaba ko ceton jinin Muhammad na ƙarshe dayake muradin gani,kokuma mutuwarsa da taki da kuma ta dukka ƴan uwanki da ubanki?
Wanann shine hukuncinki da butulcin da kikayiwa soyayyar ɗana,kuma haka zaki girbeta har ƙarshen rayuwarki. Sannan kada ki manta,dukkan ahalin gidan suna ƙarƙashin ikona ne,kuskure kaɗan zai kaiki ga yin dana sani marar misali"......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.